Jami’an Tsaro Sun Ceto Mutane 84, Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 3 A Katsina
Published: 20th, March 2025 GMT
A cewar Kwamishinan, sojojin sun yi artabu da ‘yan ta’adda a kauyukan Malori da Matalawa, inda suka kara tura su cikin tsaunukan.
Mua’zu ya ci gaba da bayanin cewa, yayin da jami’an tsaron suka isa sansanin Sanusi Dutsin-Ma, sun yi nasarar tarwatsa jama’arsa tare da kashe ‘yan ta’adda uku, yayin da wasu da dama suka gudu da raunuka.
Bayan haka, sojojin sun ceto mutane 84 da aka yi garkuwa da su da suka hada da maza bakwai, mata 23, da kananan yara 54 da aka tsare a sansanonin ‘yan ta’addan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Majalisar Dattawa ta amince Tinubu ya tura sojojin Najeriya zuwa Jamhuriyar Benin
Majalisar Dattawa a ranar Talata ta amince da bukatar Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta tura sojojin Najeriya zuwa Jamhuriyar Benin domin tabbatar da dimokuradiyya a kasar.
Majalisar ta kuma ce tana goyon bayan matakin da shugaban ya ɗauka kwanaki kafin haka domin hana yunƙurin kifar da tsarin dimokuraɗiyya a makwabciyar kasar.
Gwamnan Jihar Ribas ya sauya sheka zuwa APC Juyin Mulki: ECOWAS ta ayyana dokar ta-baci a kasashentaBukatar dai na kunshe ne a cikin wata wasiƙa da Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio, ya karanta a zauren majalisa yayin zamanta.
Tinubu ya umarci tura sojojin makon da ya gabata domin dakile yunƙurin karɓar mulki ba bisa ka’ida ba a Jamhuriyar Benin da kuma kaucewa rikicewar tsaro a yankin yammacin Afirka.
Sai dai Tinubu bai nemi amincewar majalisa ba kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.
Bayan karanta wasiƙar, majalisar ta koma zaman kwamiti domin tantance bukatar. A yayin zaman, ’yan majalisa sun tattauna kan tasirin tsaro, jin‑ƙai da diflomasiyya da ke tattare da wannan mataki.
Babbar damuwar a cewarsu ta haɗa da yiwuwar kwararar ’yan gudun hijira zuwa Najeriya, tsaron iyaka da kuma tasirin matakin ga zaman lafiya da tsaro a yankin.
Bayan doguwar muhawara, majalisar ta koma zama a zaurenta, inda ta kada kuri’ar amincewa da matakin shugaban ƙasa cikin rinjaye.
Shugaban Majalisar, Akpabio, ya gabatar da rahoton kwamitin domin tabbatarwa, inda ’yan majalisa suka amince ba tare da wata adawa ba kafin su amince da tura sojojin ta hanyar kada kuri’ar murya karo na biyu.
A jawabin sa, Akpabio ya yabawa Shugaba Tinubu bisa ɗaukar matakan da suka tabbatar da zaman lafiya a yankin da kuma bin ka’idojin kundin tsarin mulki ta hanyar neman amincewar majalisa, ko da bayan tura sojojin cikin gaggawa.
“Wannan mataki ne da ya zama dole. Shugaban Ƙasa ya yi aiki ne domin kare tsaron ƙasa da kuma kare dimokuraɗiyya a yammacin Afirka. Barazana ga kasa ɗaya barazana ce ga kowa,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa za a isar da kudurin majalisar ga Shugaban Ƙasa nan take.