Sin: Shingayen Kasuwanci Suna Illata Wadatar Tattalin Arzikin Duniya
Published: 20th, March 2025 GMT
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Mao Ning ta bayyana cewa, kakaba haraji da sauran shingayen kasuwanci ba za su amfani kowa ba, kuma suna matukar haifar da illa ga samar da wadatar tattalin arzikin duniya, da tafiyar da shi cikin kwanciyar hankali.
Jami’ar wacce ta bayyana haka a yau Alhamis yayin wani taron manema labarai, ta ce kasar Sin za ta ci gaba da kara bude kofa ga kasashen waje, da nuna goyon baya ga ka’idojin ciniki cikin ‘yanci, da tsarin kasuwanci a tsakanin bangarori daban-daban, da karfafa samun moriyar kasa da kasa ta fuskar tattalin arzikin da ya hade kowa da kowa, da neman bunkasa ta bai-daya, tare da samar da moriyar juna da dukkan kasashen duniya.
Mao ta bayyana hakan ne a matsayin martani ga sabon rahoton hasashen tattalin arziki na wucin gadi na kungiyar bunkasa hadin gwiwar tattalin arziki da ci gaban kasashe ta OECD, wanda ya rage hasashen matakin ci gaban da za a samu a duniya. Rahoton ya yi nuni da cewa, shingayen kasuwanci na baya-bayan nan da wasu kasashe suka kafa na iya kawo cikas ga ci gaban tattalin arzikin duniya, da kuma haifar da hauhawar farashin kayayyaki.
Bugu da kari, a cewar rahotannin kafofin yada labarai, wani dan siyasa a majalisar dokokin Amurka ya aike da wasiku zuwa jami’o’in Amurka shida, inda ya bukaci a bayar da bayanai kan dalibansu Sinawa saboda abin da ya shafi batun “tsaron kasa”. Sai dai, Mao ta bukaci Amurka da ta guji daukar matakan nuna wariya da takura wa daliban kasar Sin. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Babban Taron Kawancen Sin Da Afirka Ya Nuna Hadin Gwiwa Kan Gudanar Da Tsarin Shugabancin Duniya Na Bai-Daya
Babban taron dandalin kafafen yada labarai na kasashe masu tasowa da kwararru na kawancen Sin da Afirka da aka bude a jiya Alhamis a birnin Johannesburg da ke kasar Afirka ta Kudu, zai lalubo hanyoyin karfafa hadin gwiwa, da fadada yin magana da murya daya a tsakanin kasashe masu tasowa da kuma habaka gudanar da tsarin shugabancin duniya na bai-daya.
Wanda kamfanin dillancin labarai na Xinhua, da Tarayyar Afirka (AU) da kamfanin Independent Media na kasar Afirka ta Kudu da sauran abokan hulda suka shirya, taron na kwanaki biyu ya samu halartar wakilai sama da 200 daga kafofin watsa labarai fiye da 160, da kungiyoyin kwararru, da hukumomin gwamnati da sauran cibiyoyi daga kasar Sin da kasashen Afirka 41, da kuma kungiyar AU.
A karkashin taken “garambawul ga tsarin shugabancin duniya: sabbin rawar da za a taka da kudurori na hangen nesa ga hadin gwiwar Sin da Afirka,” taron ya mayar da hankali ne kan yadda hadin gwiwa tsakanin kafofin watsa labarai da kungiyoyin kwararru zai iya ba da gudummawa wajen tsara shugabanci na duniya mafi adalci da ya hade kowa da kowa.
ADVERTISEMENTTaron ya kuma kunshi fitar da wani rahoto na kwararru mai taken “gina sabon tsarin shugabancin duniya–yin aiki tare don neman samar da tsarin shugabancin duniya mai adalci da ma’ana,” da kuma kaddamar da turbar sadarwa ta hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa mai lakabin “hadin kai a cikin zukata, hanya da kuma aiki–shirin aiki kan karfafa hadin gwiwar Sin da Afirka na shekarar 2026.” (Abdulrazaq Yahuza Jere)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA