Leadership News Hausa:
2025-12-13@14:17:39 GMT

‘Yansanda Sun Gano Haramtaccen Wurin Hada Makamai A Kano

Published: 14th, April 2025 GMT

‘Yansanda Sun Gano Haramtaccen Wurin Hada Makamai A Kano

Rundunar ‘yansandan Nijeriya ta gano wani haramtaccen wurin hada makamai a jihar Kano, lamarin da ya kai ga kama wasu mutane uku tare da kwato bindigogi kirar gida guda 15 tare da harsashi 102. Wadanda ake zargin sun hada da Abdul Sadiq mai shekaru 43; Ahmad Muazu, 22; da Aliyu Sharif, mai shekaru 40, an kama su ne a ranar 10 ga watan Afrilu a unguwar Dorayi Babba da ke jihar, sakamakon wani hadin gwiwa da jami’an rundunar ‘yansandan jihar Kano suka jagoranta.

Tinubu Ya Kaddamar Da Ci Gaba Da Aikin Titin Abuja Zuwa Kaduna  Salah Ya Kafa Tarihi Yayin Da Liverpool Ke Dab Da Lashe Gasar Firimiya Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan, ACP Olumuyiwa Adejobi ya tabbatar da kamen a wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce an gudanar da aikin ne bisa wani sahihan bayanai da suka kai ga gano tarin haramtattun makaman. Sufeto-Janar na ‘yansanda, IGP Kayode Egbetokun, ya yaba da matakin gaggawar da jami’an suka dauka tare da jaddada aniyar rundunar na dakile yaduwar makamai marasa lasisi a fadin kasar nan.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Sojoji sun kashe ’yan bindiga 3 a Binuwai

Dakarun Sojin Operation Whirl Stroke (OPWS), sun kashe wasu mutum uku da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, yayin wani samame da suka kai a Ƙaramar Hukumar Ukum, a Jihar Binuwai.

Mai magana da yawun OPWS, Laftanar Ahmad Zubairu, ya ce sojojin sun samu bayanan sirri kuma suka yi aiki tare da ’yan sandan Zaki-Biam.

Kotun Koli ta soke afuwar da Tinubu ya yi wa Maryam Sanda Dan sanda ya yi batan dabo a bakin aikinsa a Katsina

Maharan sun kafa shinge a kan hanyar Aturuku–Wembe–Ayati, inda suke tare matafiya suna ƙwace musu kayayyaki.

Da sojoji suka isa wajen, maharan sai suka fara harbe-harbe, wanda hakan ya sa sojojin suka buɗe musu wuta.

Hakan ya yi sanadin mutuwar uku daga cikinsu, sauran kuma suka tsere cikin daji.

Dakarun sun ƙwato babura guda biyu, yayin da suka ci gaba da farautar waɗanda suka tsere.

Bincike ya nuna cewa mutanen da suka mutu suna cikin wata ƙungiya da ta daɗe tana yi wa al’umma barazana ta hanyar garkuwa da mutane da kai hare-hare, musamman kusa da kasuwar doyar Zaki-Biam.

Mutanen gari sun tabbatar da sunan waɗanda dakarun suka kashe.

Kwamandan OPWS, Manjo-Janar Moses Gara, ya yaba wa sojojin bisa ƙwazo da jarumtarsu, tare da alƙawarin ci gaba da kare al’umma da tabbatar da zaman lafiya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ’Yan sanda sun ba da tabbacin isasshen tsaro a zaɓen ƙananan hukumomin Borno
  • Gwamnatin Kano ta haramta kafa hukumar Hisbah mai zaman kanta
  • Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 2, sun ƙwato makamai a Borno
  • Sojoji sun kashe ’yan bindiga 3 a Binuwai
  • Kotu Ta Umarci EFCC Ta Biya Wani Ƴan Kasuwar Kano Miliyan 5, Ta Nemi Afuwar Su
  • Annabi SAW Ya Zarce Duk Sauran Annabawa Yawan Mu’uzijoji
  • Kotu Ta Yanke Wa Wani Mutum Hukuncin Kisa Bisa Garkuwa Da Kashe Mai Gidansa A Kano
  • Mahajjata 2,235 Ne Suka Yi Rijistar Aikin Hajjin 2026 A Sokoto
  • Ɗaliban Jami’ar Unijos 8 sun mutu a hatsarin mota
  • Gwamnan Kano ya naɗa mace ta farko a matsayin shugabar Jami’ar Northwest