Aminiya:
2025-03-19@16:47:39 GMT

Dan ta’adda zai biya tarar miliyoyi bayan shan dukan kawo wuka a Katsina

Published: 12th, March 2025 GMT

Wani dan bindiga da ya karya yarjejeniyar sulhu a Karamar Hukumar Jibiya ta Jihar Katsina mai suna Bala Wuta na Garin Mazanya, na can kwance rai-kwakwai-mutu-kwakwai bayan ya sha dukan kawo wuka.

Tubabbun ’yan bindiga sun yi wa Bala wuta takakkiya ne har gida inda suka yi masa bugun dawa, bayan da ya yi garkuwa da wasu matafiya jim kadan bayan sulhun da aka yi, inda bayan sun lugwiwita shi, suka wajabta masa biyan tarar Naira miliyan uku.

HOTUNA: Fashewar tankar gas ta kashe gomman mutane a Legas HOTUNA: An hana Gwamna Fubara shiga Majalisar Dokokin Ribas

Ana iya tuna cewa, a ranar 28 ga watan Fabrairu, 2025 ne aka yi sulhun, wanda ya samu wakilcin sojoji da ’yan sanda da sauran jami’an tsaro da masu ruwa karkashin jagorancin shugaban karamar hukumar ta Jibiya Alhaji Maitan, kamar yadda su ’yan bindigar suka nema.

’Yan bindigar da suka halarci zaman a karkashin jagoransu Audu Lankai, sun hada da Kantoma da Ori da Tukur Dan Najeriya da Bammi da sauransu da suka fito daga yankin Zamfara.

Yarjejeniyar da aka kulla

Jama’ar yankin sun shimfida wa ’yan bindiga sharadin barin kai hare-hare a fadin karamar hukumar da hanyar Katsina zuwa Jibiya da hanyar Jibiya zuwa Gurbi da kuma wadda ke zuwa Batsari.

Za kuma su da daina kai hari ko barna a gonaki ko cikin daji ko guje-guje a kan babura a cikin garin ko nuna rashin da’a ko tarbiyya ga al’umma.

Kazalika, yarjejeniyar ta bukaci za su kiyaye duk dokokin gwamnati su kuma daina yawo da makamai a bainar jama’a.

A nasu bangaren, tubabbun ’yan bindigar dajin sun shardanta a daina kashe su ko kama dabbobinsu babu dalili da kuma tabbatar da adalci a tsakaninsu da sauran al’umma a matsayinsu na ’yan kasa.

Sa’annan sun bukaci a daina daukar doka da hannu a rika barin hukuma ta yi hukunci ga mai laifi.

Bayan nan ne suka sako mutane 10 na garin Daddara da ke hannunsu tare da mika bindiga kirar AK-49 guda biyu.

Bala Wuta ya ji a jikinsa

Sai dai duk da wannan yarjejeniyar sulhu da aka kulla, sai ga shi a ranar Alhamis da ta gabata, wani wanda bai shiga sulhun ba mai suna Bala Wuta na Garin Mazanya da ya addabi hanyar zuwa Jibiya, ya kayar da wata mota ya yi awon gaba da matafiya a Mallamawar Batsari — garin su Lankai.

A dalilin haka shi Audu Lankai jagoran sasanci ya taras da shi har gida ya yi mishi dukan kawo wuka sannan ya sanya masa tarar kudi har naira milyan uku.

Har zuwa yanzu, wakilinmu ya ruwaito cewa, Bala Wuta yana can kwance yana jin jiki a garin na Mazanya.

Labarin da muka samu daga garin na Jibiya an ce, a ranar Lahadi an ga Fulanin da ke cikin dajin sun shigo kasuwa mazansu da matansu cikin murna saboda samun wannan ’yanci.

Majiyarmu ta shaida mana cewa, Fulanin sun rika sayen lemon kwalba mai sunyi da ake sayarwa Naira 250, wanda suke cewa a can daji naira dubu ake sayar musu.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Jibiya yan bindiga

এছাড়াও পড়ুন:

‘Yansanda Sun Kama Wata Mata Da Ake Zargi Da Safarar Makamai A Katsina

Haka kuma, a ranar 3 ga Fabrairu, jami’an ‘yansanda sun kama wasu mutum uku da bindigogi 10 ƙirar AK-47, inda suka amsa cewa suna sayar da su ga masu aikata laifuka.

Rundunar ‘yansanda ta ce za ta ci gaba da yaƙi da fasa-ƙwauri da safarar makamai da miyagun ƙwayoyi, tare da kira ga ‘yan ƙasa da su riƙa kai rahoton duk wani abu da ba su yarda da shi ba.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ‘Yan Bindiga Sun Sace Mutum 7 A Jihar Neja
  • ’Yan Banga Sun Ceto Mutum 3 Daga Hannun ’Yan Bindiga A Taraba
  • ‘Yansanda Sun Kama Wata Mata Da Ake Zargi Da Safarar Makamai A Katsina
  • Janar Tsiga ya shafe kwanaki 40 a hannun masu garkuwa duk da biyan kuɗin fansa
  • Trump Zai Tattauna Da Putin Kan Kawo Ƙarshen Yaƙin Ukraine
  • Iran An Dauke Wa Mahdi Karubi Daurin Talalar Da Aka Yi Masa A Gida
  • Tsofaffin furodusoshin Kannywood da aka daina jin ɗuriyarsu
  • Gwamnatin Kano Ta Umarci Ma’aikatanta Da Su Tantance Allbashin Watan Maris Kafin A Biya Su
  • Ba Don Tarbiyantar Da Mutane Nake Yin Fim Ba -Amina Shehu Lulu
  • Sojoji sun kashe ’yan bindiga 31, sun lalata sansaninsu a Katsina