Hamas : matakin Isra’ila na hana shigar da kayan agaji zuwa Gaza ”laifi na yaki”ne
Published: 12th, March 2025 GMT
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta ce matakin da Isra’ila ta dauka na hana shigar da kayayyakin jin kai da bukatun yau da kullum a zirin Gaza da aka yi wa kawanya ya zama “laifi na yaki da kuma hukuncin gama-gari.”
A cikin wata sanarwa da ta fitar, Hamas ta ce matakin rufewar ya saba yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta watan Janairu ne.
“Irin wannan matakin keta dokokin kasa da kasa da na jin kai, da yarjejeniyar Geneva, kuma laifukan yaki ne da hukuncin gama-gari da ke barazana ga rayukan fararen hula wadanda basu ji basu gani ba.”
Hamas ta ce rufewa da kuma hana shigar da kayan agaji sama da kwana 10 a jere yana kara tsananta radadin da Falasdinawa sama da miliyan biyu ke fama da su, kuma yana nuna yiwuwar fuskantar yunwa a Gaza.
“hana shigar da abinci, magunguna, man fetur, da hanyoyin agaji na yau da kullun ya haifar da tashin gwauron zabin abinci da kuma tsananin karancin magunguna, lamarin da ya ta’azzara matsalar jin kai a Gaza.”
Hamas ta yi kira ga masu shiga tsakani da su matsa wa gwamnatin kasar lamba wajen “cika alkawurran da ta dauka” a karkashin yarjejeniyar tsagaita bude wuta.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: hana shigar da
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci Ta Iran Ya Ce: Jagora Da Kansa Ya Shiga Dakin Ba Da Umarnin Sojin Lokacin Yaki
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya bayyana cewa: Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ba da umarninsa ga sabbin kwamandojin da kansu a lokacin yakin baya-bayan nan
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran Muhammad Baqir Qalibaf, yayin da yake ishara da umarnin da Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayar a yakin kwanaki 12 da aka kakabawa Iran, ya ce Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya kasance a dakin kwamandoji sau biyu a lokacin yakin tare da bayar da umarninsa ga sabbin kwamandojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
A wata hira da aka yi da shi ta gidan telebijin, Qalibaf ya kara da cewa kwamandojin da aka nada sa’o’i bayan fara kai hare-hare kan kasar Iran, kwararru ne da suka yi kama da tsararsu kwamandojin da suka yi shahada kuma suka shiga filin nan take.
Qalibaf ya jaddada cewa: Cikin sa’o’i kadan ne Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya samu nasarar kubutar da sojojin kasar daga irin firgicin da suka shiga na fuskantar hare-haren wuce gona da iri da yahudawan sahayoniyya suka kaddamar kan Iran.