HausaTv:
2025-07-09@05:27:25 GMT

Jamus, Faransa, Birtaniya Da Italiya Sun Yi Maraba Da Shirin Larabawa Kan Gaza

Published: 9th, March 2025 GMT

Kasashen Jamus, Faransa, Birtaniya da Italiya “sun yi maraba” da shirin kasashen Larabawa na sake gina Gaza.

 A cikin wata sanarwa ta hadin guiwa da ministocin harkokin wajen kasashen suka fitar a birnin Berlin, sun ce shirin idan an aiwatar da shi zai bada damar gaggauta warware mummunan halin da Falasdinawa ke ciki a Gaza.

A yayin taron da suka gudanar ne a ranar Talata data gabata a Masar kasashen Larabawan suka gabatar da wani shiri da zai lakume dalar Amurka Biliyan 53 na sake gina Gaza cikin fiye da shekara biyar inda shirin zai mayar da hankali kan taimakon gaggawa,dawo da ababen more rayuwa da kuma ci gaban tattalin arziki mai dorewa.

Shirin na kasashen Larabawa tamakar neman maye gurbin shirin da shugaban Amurka Donald Trump, ya fitar a watan da ya gabatar na karbe iko da zirin Gaza dama tilasta musu hijira zuwa kasashen Masar da Jordan.

Matakin na Trump dai ya fuskanci martini da tofin Allah tsine daga daga Falasdinawa da kasashen Larabawa da kuma gwamnatoci da yawa a duniya, inda sukayi fatali da duk wani shiri na korar mutanen Gaza daga kasarsu ta asali.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: kasashen Larabawa

এছাড়াও পড়ুন:

‘ADC za ta mayar da APC jam’iyyar adawa a 2027’

Tsohon Ministan Sufuri, Idris Umar, ya bayyana cewa jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ce za ta ceto Najeriya daga halin da take ciki, tare da mayar da APC jam’iyyar adawa a Zaɓen 2027.

Yayin wani taron haɗin gwiwar jam’iyyu na adawa a Gombe, an amince da amfani da ADC a matsayin dandalin siyasa na bai ɗaya domin fuskantar zaɓen 2027.

Gwamnatin Tinubu na shirya mana zagon ƙasa — ADC NAJERIYA A YAU: Sarƙaƙiyar da ke gaban Haɗakar ADC: Atiku ko Peter Obi

Taron ya gudana a Shugleez Event Centre wanda ya samu halartar fitattun ‘yan adawa daga sassa daban-daban na jihar.

Idris ya ce za su yi haɗakar ce ba wai kawai don karɓar mulki ba, sai dai domin ceton ƙasa da talakawa daga matsin tattalin arziƙi da rashin shugabanci nagari.

Shugaban ADC na jihar, Auwal Abba Barde, ya ce jam’iyyar na samun karɓuwa daga sabbin mambobi tare da tabbatar musu da wakilci

Aminiya ta ruwaito cewa an kafa kwamitin rajistar sabbin mambobi ƙarƙashin tsohon Mataimakin Gwamnan Gombe, John Lazarus Yoriyo, da AVM Adamu Fura a matsayin mataimaki.

Tsohon shugaban matasan APC, Sunusi Abdullahi Ataka, ya ce haɗakar za ta yi tasiri wajen karɓar mulki a Gombe da Najeriya gaba ɗaya.

Wasu daga cikin mahalarta sun haɗa da wakilin Farfesa Isa Ali Pantami, Abubakar Abubakar BD, da sauran jiga-jigai na jam’iyyar ADC.

Bayanai sun ce a yanzu haka jam’iyyar ADC da ’yan haɗaka da wasu jagororin ’yan hamayya suka dunƙule a ƙarƙashin inuwarta ta fara karɓe tsarin jagorancin jam’iyyar PDP a jihohin Yobe da Adamawa da kuma Gombe.

Sun ce an samu ’yan PDP da dama da suka sauya sheƙa zuwa ADC, ciki har da waɗanda suka riƙe manyan muƙamai a baya.

A Jihar Adamawa wasu daga cikin ƙusoshin jam’iyyar da suka riƙe mukamai a matakai daban daban na jiha tuni suka sauya sheƙa zuwa jam’iyyar ’yan hadaka ta ADC inda kawo yanzu shugabannin jami’yyar PDP a ƙananan hukumomi goma a cikin jihar suka fice daga cikin jam’iyyar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ‘ADC za ta mayar da APC jam’iyyar adawa a 2027’
  • Shugaban Kasar Iran Ya Ce; An Rusa Hanyar Tattaunawa da Iran Kan Shirin Na Makamashin Nukiliya Na Zaman Lafiya
  • Kasar China Ta Yi Watsi da Barazanar Trump Na Kakabawa Kasashen BRICS Karin Takunkuman Tattalin Arziki
  • Sin Za Ta Gina Wuraren Cajin Ababen Hawa Masu Ingantaccen Lantarki
  • Reuters: Amurka Tana Da Shirin Korar Falasdinawa Daga Gaza
  • Bidiyon tsiraici: Babiana ta sake jawo ce-ce-ku-ce
  • ’Yan Boko Haram sun kashe mutum 9, sun Jikkata 4 a Borno
  • ’Yan Boko Haram sun kashe mutum 9, skun Jikkata 4 a Borno
  • An Kaddamar Da Shirin Samar Da Wutar Lantarki A Jami’ar Kashere Gombe.
  • Zulum ya musanta shirin ficewa daga APC