Aragchi: Hare-hare Kan Cibiyoyin Makamashin Nukliya Na Kasar Iran Ba Za Su Wargaza Shirin Ba
Published: 8th, March 2025 GMT
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa hare-hare a kan cibiyoyin makamashin Nukliyar kasar ba zasu dakatar da ayyuka a cibiyoyin ba. Sai dai yin haka zai kara yada yaki a yankin kudancin Asiya.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Aragchi yana cewa cibiyoyin nukliya na kasar Iran suna da kekyawar kariya daga makamai.
Ministan ya bayyana haka ne a taron kasashen musulmi na OIC wanda aka gudanar a birnin Jedda na kasar Saudiya a yau Asabar. Ya ce iran zata ci gaba da neman fahintar juna ta hanyar diblomasiyy, Amma idan sun dage zasu yi amfani da karfi to Iran a shirye take ta kare kanta, kuma bata da zabi sai hakan.
A wani bangare ministan ya bayyana cewa Iran ba ta cikin sauri wajen samar da hulda da sabuwar gwamnatin kasar Siriya.
A jawabinsa a taron na OIC Aragchi ya kawo baton kasar Falasdinu da kuma shirin Amurka na kwace Gaza daga hannun falasdinawa ta kore su zuwa kasashen Masar da Jordan. Ya yi allawadai da hakan ya kuma bayyana cewa ya sabawa dukkan dokokin kasa da kasa.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kasar Sin Na Adawa Da Zarge-Zargen G7 Don Gane Da Tekun Kudancin Kasar
Kasar Sin ta bayyana matukar adawa da zarge-zargen kungiyar G7 kan tekun kudancin kasar da manufofinta na tattalin arziki, kuma ta bayyana korafinta ga kasar Canada.
Ofishin jakadancin kasar Sin dake Canada ne ya bayyana haka a yau Asabar.
A cewar ofishin jakadancin, sanarwar taron ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar G7 da sanarwar ministocin game da tsaron teku, sun yi shisshigi cikin harkokin gidan Sin, kana sun bata mata suna. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp