HausaTv:
2025-09-17@23:26:29 GMT

Shari’ar ‘Yan Hamayyar Siyasa 40 A Tunisiya Ya Jefa Kasar Cikin Takaddama

Published: 6th, March 2025 GMT

Kasar Tunisiya ta shiga cikin sabuwar dambaruwar siyasa saboda yadda ake yi wa wasu fitattun ‘yan siyasa, lauyoyi da kuma ‘yan jarida 40 shari’a, bisa zargin cewa suna yi wa kasa makarkashiya.

An jibge jami’an tsaro masu yawan gaske a bakin kotun, yayin da a wajenta kuma masu fafutuka suke bayar da taken nuna kin amincewa da shari’ar, suna bayar da taken; ‘Neman ‘ ‘yanci, da kuma zargin ma’aikatar shari’a da zama ‘yar koren gwamnati.

Lauya a cikin kwamitin lauyoyi masu bayar da kariya ga wadanda ake yi wa shari’ar, Lamia Farhani ta bayyana cewa; Abin ban mamaki shi ne shugaban kasa wanda ya rantse zai kare shari’a, wanda kuma shi kwararre ne akan tsarin mulki shi ne na farkon da ya karya doka.

Wani daga cikin ‘yan kasa da su ka halarci gangamin mai suna Ahlem ya shaida wa kamfanin dillancin labaurn “Associated Press” cewa; Ya zo ne domin ya nuna goyon bayansa ga wadanda ake tsare da su, tare da tuhumar gwamnatin kasar da cewa garkuwa take yi da mutanen da take yi wa shari’a.

Sai dai kuma wasu ‘yan kasa suna da ra’ayin da yake cin karo da  wannan, suna ganin cewa wadanda ake yi wa shari’an sun cancanci a daure su tsawon rai. Har ila yau ya kuma tuhumi ‘yan siyasar da ake yi wa shari’ar da cewa, sun ruguza tattalin arzikin kasar ta yadda darajar  kudaden kasar  ta fadi kasa.

A gefe daya MDD ta yi kira ga gwamntin ta Tunisiya da ta kawo karshen duk wata shari’a  ta siyasa da ake yi wa ‘yan hamayya, sannan kuma ta bar mutanen kasar cikin ‘yancin bayayna ra’ayoyinsu.

MDD ta ce, yi wa ‘yan hamayyar shari’a zai mayar da tsarin demokradiyyar kasar baya.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: ake yi wa shari yi wa shari a da ake yi wa

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamna Namadi Ya Taya Malaman Makarantu Da Suka Yi Fice A Jihar Murna

Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya yabawa Hukumar Makarantun Kimiyya da Fasaha ta Jiha bisa ƙirƙirar Kyautar Malami Mafi Nagarta, yana mai bayyana hakan da ɗaya daga cikin manyan manufofin da za su ƙarfafa koyo da koyarwa a fadin jihar.

A cikin wata sanarwa da Babban Jami’in Yaɗa Labaran sa, Hamisu Mohammed Gumel, ya fitar, gwamnan ya bayyana cewa bikin na farko na bada lambar yabo da aka gudanar a Dutse ya dace domin girmama malamai da suka yi fice ta hanyar jajircewa da sadaukar da kai.

Ya ƙara da cewa wannan mataki zai ƙara kwarin gwiwa, ya samar da gasa mai kyau, tare da inganta darussa a makarantu.

Namadi ya jaddada cewa ingancin ilimi bai tsaya kan gina makarantu kawai ba, yana ta’allaka ne ga ingancin malamai, kayan koyarwa da kuma yanayin makarantu.

Ya bayyana cewa gwamnatinsa ta fara ɗaukar malamai tare da horas da su akai-akai domin rage cunkoson ɗalibai da malamai da kuma horar da su sabbin dabarun koyarwa.

“Wannan shiri ɗaya ne daga cikin mafi kyawu da muka gani. Idan wani ya yi kuskure, sai a hukunta shi, yayin da duk wanda ya yi fice, wajibi ne a yaba masa. Wannan shi ne yadda ake samun cigaba,” in ji gwamnan.

Ya bukaci sauran hukumomin ilimi kamar Hukumar Gudanar da Makarantun Sakandare, Hukumar Ilimin Addinin Musulunci, da Ma’aikatar Ilimin Firamare su yi koyi da wannan tsari domin ƙara ƙarfafa gwanintar malamai a dukkan matakai.

Gwamnan ya kuma sake jaddada  cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da maida hankali wajen gina makarantu, horar da malamai, da walwalar su.

Ya tabbatar da cewa za a ci gaba da baiwa bangaren ilimi goyon baya don inganta sakamakon koyo a makarantu a fadin Jihar Jigawa.

 

Usman Muhammad Zaria 

 

 

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yakin Haraji Da Cinikayya Ba Zai Gurgunta Fifikon Da Sin Ke Da Shi A Fannin Raya Masana’antun Sarrafa Hajoji Da Kasar Ta Gina A Tsawon Lokaci Ba
  • Gwamna Namadi Ya Taya Malaman Makarantu Da Suka Yi Fice A Jihar Murna
  • Ma’aikatar Shari’ar Iran Ta Sanar Da Rataye Dan Leken Asirin Hukumar Mossad Ta Isra’ila
  • Babban Jirgin Ruwan Kasar Sin Ya Nufi Yankin Tekun Kudancin Kasar Domin Gwaji Da Samar Da Horo
  • Kungiyar Human Rights Watch; Isra’ila Ta Kashe ‘Yan Jarida Fiye Da 30 A Kasar Yemen Ne Da Gangan  
  • Taron Doha: Daga matakin Allawadai zuwa matakan kalubalantar laifukan Isra’ila
  • Pezeshkian: Ya kamata kasashen musulmi su yanke alaka da gwamnatin sahyoniya tare da kiyaye hadin kai
  • Sabunta Cinikin Ba Da Hidima, Masu Zuba Jari Na Waje Suna Ganin “Damar Da Kowa Ke Bukata A Kowane Lungu Na Sin”
  • Burkina Faso: Masu Ikirarin Jihadi Sun Kashe Fararen Hula 50 A Cikin Watanni Hudu
  • Tattalin Arzikin Sin Ya Samu Ci Gaba Ba Tare Da Tangarda Ba A Watan Agusta