Jakadan JMI a hukumar makamashin Nukliya Mohsen Naziri ya bayyana cewa sabbin takurawar da kasashen yamma, musamman Amurka suke wa kasarsa ba zasu yi tasiri ba. Banda hakan zasu cutar da wadanda suka dora mana su,

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Naziri yana fadar haka a Jawabin da ya gabatar  a taron gwamnoni hukumar ta IAEA a birnin Geneva a jiya Laraba.

Ya ce kasashen yamma ne suka jagoranci karin takunkuman tattalin arziki a kan Iran, ko kuma bayyana cewa Iran bata bada hadin kai da ta dace ga hukumar makamashin Nukliya ta duniya wato IAEA. Da kuma zargin kasar Iran da cewa tana kokarin mallakan makaman Nukliya.

Naziri ya zargin kasashne yamma kan rashin cika al-kawalin da suka dauka a yarjeniyar JCPOA na shekara ta 2015, inda Amurka ta fara da janyewa daga yerjeniyar da aka dauki shekaru biyu cur ana tattaunawa a kanta.

Yace Amurka ta fice daga yaerjeniyar a shekara ta 2018 da sunan shi ne yarjeniya mafi muni wanda Amurka ta taba sanyawa hannu, kuma zata tilastwa Iran amincewa da sabuwar yarjeniya da ita, ko kuma ta sha wahala, ko gwamnatin JMI ta rushe karkashin takurawar ta.

Banda haka kasashen Turai wadanda suke goyon bayan Amurka sun ki cika nasu alkawulan a cikin yarjeniyar ta JCPOA.

Naziri Asl ya bayyana cewa martanin da Iran ta mayar shi ne, rage abinda yah au kanta a yarjeniyar, , wanda ita kanta Yarjeniyar ta bada damar yin haka a duk lokacinda dayan bangaren ya saba alkawulan da ta dauka a cikinta.

Ka’ida ta 26 da 36 na yarjeniyar ta bawa Iran wannan damar, na sabawa yarjeniyar don dawo da dayan bangaren kan abinda yakamata ya yi.

Ya kuma kara da cewa kasashen yamma basu da damar sake maida takunkuman tattalin arziki kan Iran saboda sune suka sabawa yarjeniyar.

Daga karshe ya ce Iran zata koma kan amfani da yarjeniyar ne kawai idan kasashen yamma sun dauke mata dukkan takunkuma tattalin arzikin da suka dora mata.

Sannan yace kasashen Ingila Faransa da Jamus sun sabawa kudurin kwamitin tsaro na MDD mai lamba 2231 wanda yake goyon bayan JCPOA.

Daga karshe yayi kira da gwamnonin hukumar ta IAEA da su maida hankalinsu wajen dabbaka kudurin na 2231.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: kasashen yamma a yarjeniyar

এছাড়াও পড়ুন:

Real Madrid zata nemi diyyar Dala bilyan 4 daga UEFA

Wata kotu da ke birnin Madrid ta yi watsi da ƙarar da Hukumar ƙwallon ƙafa ta Nahiyyar Turai UEFA, LaLiga da Hukumar Kwallon Kafa ta Sipaniya suka shigar kan ƙin amincewa da gasar Super League.

Wannan yana nufin yanzu Real Madrid da sauran ƙungiyyoyin za su iya neman diyyar kudi Euro Milyan 4.

Kotu ta tsige dan majalisar da ya sauya sheka zuwa APC Shugabannin Kudancin Kaduna za su karrama Janar  Christopher Musa 

Real Madrid ta ce, wannan hukuncin ya tabbatar da cewa UEFA ta karya dokokin gasa, kuma ƙungiyyoyi sun rasa maƙuden kuɗaɗe tun daga lokacin da aka dakatar da gasar.

Gasar wacce aka shirya farawa a shekarar 2021 tare da manyan ƙungiyoyin Turai, an yi hasashen zata samar da kusan Yuro miliyan 200 ga ƙungiyoyin da suka shiga.

A nata martanin hukumar UEFA ta dage cewa wannan sabon hukuncin ba ya nufin an dawo ko an amince da a buga gasar Super League ba ne.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Araqchi: Da Hadin Bakin Amurka, Gwamnatin Isra’ila ta kaddamar Da Hari Kan Kasar Iran
  • Gwamnatin Isra’ila Tana Ci Gaba Da Hana Masu Jinya Zuwa Kasashen Waje Neman Magani Daga Gaza
  • IAEA : Babu wata shaida da ke nuna cewa Iran na kera makaman nukiliya
  • Iran Ta Gargadi Isra’ila Kuma Tasha Alwashin Kare Shirinta Na Nukiliya
  • Shugaban Kasar Najeriya Ya Mayar Da Martani Ga Takwaransa Na Amurka Akan Rikicin Addini
  • Kasashen Pakistan Da Afghanistan Sun Tsawaita Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta
  • Real Madrid zata nemi diyyar Dala bilyan 4 daga UEFA
  • An raba wa iyalan jami’an ’yan sandan da suka rasu a bakin aiki a Borno N63.4m
  • NPA Da Ƙungiyar Injiniyoyi Ta Yi Haɗaka Don Bunƙasa Tashoshin Jiragen Ruwa
  • Sin Da Amurka Suna Taimaka Wa Juna Da Samun Wadata Tare