Da wahala City ta yi nasara a gidan Madrid — Guardiola
Published: 18th, February 2025 GMT
Kociyan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester City, Pep Guardiola, ya ce damarsu ta samun nasara kan Real Madrid ’yar kaɗan ce a yayin da a gobe Laraba ƙungiyoyin biyu za su yi karon-batta a Gasar Zakarun Turai.
Ana iya tuna cewa, a karawar farko da ƙungiyoyin suka yi a Talatar makon jiya, Madrid ce ta je har gida ta lallasa City da ci 3-2, minti huɗu kafin a tashi wasan.
To sai dai gabanin karawar ta biyu da za a yi a filin wasa na Bernabeu, a wasan neman gurbin tsallakawa zagayen ’yan 16, Guardiola ya ce damar da suke da ita kan Madrid kaɗan ce, amma za su yi iya ƙoƙarinsu wajen ganin sun yi amfani da ita.
City dai ta farfaɗo daga dukan da ta sha a hannun Madrid a wasan da ta yi da Newcastle a gasar Firimiyar Ingila, inda ta lallasa ta da ci 4 da nema, lamarin da ya sa a ke ganin wataƙila ta iya sauya sakamakon na Madrid, sai dai Guardiola ya ce ba ya tunanin hakan ta kasance.
A karawar ta gobe dai, ya zama wajibi ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyin biyu ta fice daga Gasar Zakarun Turai ba tare da kai wa zagayen ’yan 16 ba, wanda ke zama karo na farko a cikin shekaru.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Gasar Zakarun Turai Pep Guardiola
এছাড়াও পড়ুন:
Rasha ta ayyana tsagaita wuta ita kaɗai a yakinta da Ukraine
Fadar Kremlin ta kasar Rasha ta ayyana tsagaita wuta na kwana biyu ita kaɗai a yakinta da kasar Ukraine.
Shugaba Vladimir Putin ya sanar a ranar Litinin cewa Rasha za ta aiwatar da tsagaita wutar ne daga tsakar dare na 8 ga Mayu zuwa tsakar dare na 10 ga Mayu.
A ranakun da za a tsagaita wutar ne Rasha ke bikin karshen da yakinta da kasar Jamus a shekarun 1941 zuwa 1945, wanda aka fi sani da Yakin Duniya na Biyu a yawancin duniya.
A Rasha ana kiran yakin na Duniya na biyu da sunan Babban Yaƙin Ceton Kasa.
Shekara 10 ina sayar da sassan jikin ɗan Adam — Wanda ake zargi Dukan farar hula saboda sanya kayan sojoji laifi ne — Janar Chibuisi