An ƙaddamar wa ’yan kasuwa sabon tsarin biyan haraji a Gombe
Published: 6th, February 2025 GMT
A ƙoƙarin bunƙasa tattalin arziƙin Jihar Gombe, Hukumar Tattara Kuɗaɗen Shiga ta jihar, ƙarƙashin jagorancin Hajiya Aisha Adamu, ta ƙaddamar wa ’yan kasuwa sabon tsarin biyan haraji.
An ƙaddamar da tsarin ne a sakatariyar Ƙungiyar ’Yan Kasuwa da ke cikin babbar kasuwar Gombe.
Majalisa na son ƙirƙiro sabbin jihohi 31 a Najeriya An tsinci gawar Ɗan Majalisar da aka yi garkuwa a jajibirin KirsimetiHajiya Aisha ta jinjina wa haɗin kan ’yan kasuwa, musamman, Alhaji Sanusi Abdullahi Mai Rediyo.
Ta ce kuɗaɗen haraji suna da muhimmanci wajen aiwatar da ayyukan raya ƙasa don amfanin al’umma.
Ta yi kira ga ’yan kasuwa da su dage wajen biyan harajinsu na shekara-shekara, wanda kowane mai shago zai biya sau ɗaya kawai.
Hajiya Aisha ta kuma bayyana cewa an samar da hanyoyin biyan haraji masu sauƙi, ciki har da ofisoshin haraji, Intanet, da kuma hedikwatar Hukumar Tattara Kuɗaɗen Shiga.
Shugaban Ƙungiyar ’Yan Kasuwa, Alhaji Sanusi Mai Rediyo, ya tabbatar da cikakken goyon bayansu ga wannan tsari.
Shi ma Sakataren Tsare-tsare na ƙungiyar, Alhaji Sabo Coca Cola, ya jaddada muhimmancin haɗin kai domin cimma burin bunƙasa tattalin arziƙin jihar.
Sabon tsarin biyan harajin zai taimaka wajen ƙara kuɗaɗen shiga na cikin gida tare da inganta ayyukan ci gaba a Jihar Gombe.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: yan kasuwa gwamnati Haraji Sabon Tsari biyan haraji
এছাড়াও পড়ুন:
Babu Wata Tattaunawa Tsakanin Sin Da Amurka Game Da Batun Haraji
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya bayyana a yau Litinin cewa, babu wata tattaunawa da aka yi ta wayar tarho tsakanin shugabannin kasashen Sin da Amurka a baya-baya nan, haka kuma bangarorin biyu ba su cimma wata yarjejeniya ko su tuntubi juna game da batun haraji ba. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp