2025-11-01@17:47:27 GMT
إجمالي نتائج البحث: 8636

«Robert Lewandowski»:

    Rundunar Rapid Support Forces ta Dakarun Kai Daukin Gaggawa a Sudan ta karɓe iko da Barbi da El Fasher a daidai lokacin da ake gargaɗin jin kai Rundunar Rapid Support Forces ta Dakarun Kai Daukin Gaggawa ta sanar da gwace iko da birnin El Fasher, babban birnin jihar Darfur ta Arewa, jim kaɗan bayan sanar...
    Tsohon gwamnan, wanda ya dade yana cikin jam’iyyar PDP kuma fitaccen mai fada a ji a cikin jam’iyyar, yana neman jagorantar jam’iyyar yayin da take shirin yin babban taronta na kasa.   Ana sa ran jam’iyyar PDP, wacce ta mulki Nijeriya daga 1999 zuwa 2015, za ta zabi sabon Shugabanta na kasa da sauran shugabannin...
    Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya ce wasu daga cikin mutanen da saba yabon tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari lokacin yake kan mulki, su ne suka fara yi masa ba’a tare da suka bayan ya sauka daga mulki. Da yake jawabi a wani taron “Lakcar Raymond Dokpesi” da Ƙungiyar Masana Hulɗa da Jama’a ta Najeriya...
      Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana matukar bakin ciki game da wannan lamarin.   Gwamnan, a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ismaila Uba Misilli ya fitar, ya yi ta’aziyya ga iyalan da suka rasu da kuma dukkan al’ummar Nafada, yana addu’ar Allah ya jikan mamatan. ShareTweetSendShare MASU ALAKA ...
    Shugaban majalisar Mohammad Baqer Qalibaf ya bayyana cewa, wasika ta hadin gwiwa da Iran, Rasha da China suka aike wa Majalisar Dinkin Duniya a cikin ‘yan kwanakin nan, da ke adawa da yunkurin Turai na sake dawo da takunkumi kan Iran wannan ya nuna hadin gwiwa mai karfi a tsakanin manyan kasashen uku. Ya yi...
    Sakataren Hezbollah, Sheikh Naim Qassem, ya tabbatar da cewa Hizbullah ta shirya don fuskantar isra’ila, yana mai bayyana cewa duk da cewa ba su da niyar fara yaki, amma suna shirye su kare Lebanon idan yaki ya barke. Sheikh Qassem a zantawarsa da tashar Al-Manar TV ya jaddada cewa idan aka tilasta musu yin yaki,...
    Wani babban kusa na Hamas ya jaddada kudirin kungiyar na tabbatar da tsagaita wuta a Gaza, yana mai jaddada cewa Falasdinawa ba sa neman komai illa ‘yancinsu na samun cin gashin kai a duniya. Khalil Al-Haya, shugaban Hamas a Gaza, ya fadi a wata hira da aka watsa ranar Lahadi cewa bangaren Falasdinawa yana da...
    Dakarun sa kai na Jama’a a Arewacin Darfur  sun fitar da wata sanarwa a ranar Lahadi suna  musanta rahotannin kafofin watsa labarai game da faduwar birnin El Fasher a hannun Dakarun RSF, tare da bayyan hakan a matsayin farganda da kuma yakin kwakwalwa. Sanarwar ta ce, “A halin yanzu ana fuskantar wani kamfen na kafofin...
    Duk da saukar farashin abinci a kasuwanni a sassan Najeriya, manoma na kokawa cewa sun shiga damuwa saboda asarar da suka tafka na kuɗaɗen da suka kashe wajen noma gonakinsu, lamarin da suka ce ya rage musu ƙwarin gwiwa su ci gaba da sana’ar. Wasu daga cikin manoman da wakilinmu suka zanta da su sun...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Tun bayan sauya hafsoshin tsaro da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi ne dai mutane da dama keta tofa albarkacin bakinsu, yayin da wasu ke ganin hakan zai taimaka wajen yaki da rashin tsaro, wasu kuwa na ganin duk jama’ar ja ce.   Shin ko sauya hafsoshin...
    A ranar 25 ga watan Oktoban shekarar 1945, wato bayan da kasar Sin ta samu nasara a yakin kin harin mayakan Japan, kasar ta Sin ta karbi yankin Taiwan daga hannun Japanawa da suka yi rabin karni suna mamayar yankin, inda suke aiwatar da mulkin mallaka. Sa’an nan zuwa ranar 25 ga watan Oktoban bana,...
    Matatar Dangote ta sanar da shirin ƙara ƙarfin sarrafa man fetur daga ganga 650,000 zuwa miliyan 1.4 a kowace rana, wanda zai sanya ta zama babbar matatar mai mafi girma a duniya. Shugaban kamfanin, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana hakan a taron manema labarai a Legas, yana mai cewa faɗaɗawar na nuna ƙwarin gwuiwa ga...
    Alhaji Aliko Dangote, na shirin faɗaɗa matatar mansa domin ta riƙa tace gangar mai miliyan 1.4 a kowace rana. A halin yanzu, matatar tana tace gangar mai 650,000 a rana, amma Dangote, ya bayyana cewa suna shirin ƙara adadin cikin shekaru uku masu zuwa. Ba zan sake tsayawa takara ba, zan bai wa matasa dama...
    Shugaban ƙungiyar ta ƙasa, Frank Ogunojemite, ne ya sanya rattaba hannunsa a wasiƙar kamar yadda Jaridar PUNCH, ta samu kwafinta. Shugaba ya bayyana cewa, ya kafa hujjar buƙatar soke tsarin, kan ƙalubalen da take fuskanta, na kashe kuɗaɗe masu yawa, musamman wajen safarar mayan Kwantainonin da ake shigoa da su daga ƙasashen da ke a...
    Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazaɓar Kebbe/Tambuwal, Abdussamad Dasuki, ya ce ba zai tsaya takara a zaɓen 2027 ba. Dasuki, ya ce ya ɗauki wannan mataki ne domin bai wa matasan Najeriya damar shiga harkokin mulki. El-Clasico: Real Madrid ta doke Barcelona da ci 2 Majalisa ta amince a ƙirƙiro sabbin jihohi 6 a Najeriya...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin An Yi Taron Tattaunawa Mai Taken “Shugabancin Duniya Da Samun Wadata Tare A Yankin Asiya Da Pasifik” A Beijing October 26, 2025 Daga Birnin Sin Sin Da Amurka Sun Cimma Matsaya Dangane Da Tsare-Tsaren Warware Batutuwan Cinikayya Da Suke Mayar Da Hankali A Kai October 26, 2025...
    Ya ƙara da cewa Basira ‘Yar Guda ta bayyana cewa za ta amince da aure ne kawai idan Idris ya mallaki gidansa na kansa, ba wanda yake haya ba. Wannan ne ya sa kotu ta dakatar da yanke hukunci domin bai wa Hisbah damar tabbatar da cewa an bi tsarin aure yadda ya dace da...
    Gyaran da aka fara ya yi daidai Nambobi suna ba da labarin wani ɓangare na labarin,  amma suna bayyana lamarin ne kawai, amma suna bayyana lamarin gaba ɗaya. A shekarar 2023, FIRS ta samu Naira Tiri liyan12.36, abinya zarce kuɗaɗen da ake tsammanin shigowa daga gare ta, har ma wuce kashi 7 na kuɗaɗen shigar...
    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ta doke babbar abokiya hamayyarta, Barcelona da ci 2 da 1 a filin wasa na Bernabeau. Wasan tsakanin manyan ƙungiyoyin biyu shi ne wasa mafi girma na hamayya a duniya. Majalisa ta amince a ƙirƙiro sabbin jihohi 6 a Najeriya An kama mutum 25 kan zargin shirya auren jinsi...
    Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ya ce Tehran a shirye take ta shiga tattaunwa ta diflomasiyya da Amurka domin cimma “mafita kan batun nukiliya cikin mutunta juna. “Iran ta sha sanar da cewa ba ta taba yin watsi da diflomasiyya ba kuma,” in ji Araghchi a wata hira da akayi da shi. “Ba za...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sharhi: Wannan Manufar Sin Za Ta Sa Kaimin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya October 26, 2025 Daga Birnin Sin An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan October 25, 2025 Daga Birnin Sin Sin Da Amurka Sun Fara...
    A birnin Paris, an gudanar da wata zanga-zanga a filin jirgin saman Roissy-Charles-de-Gaulle game da shigar da makamai da kayan aikin soja na Faransa zuwa Isra’ila. An shirya zanga-zangar ne bisa kiran wasu kungiyoyi da nufin bayyana rawar da Faransa ke takawa wajen samar wa sojojin Isra’ila makamai da kayan soji, musamman ta babban filin...
    Kungiyar gwagwamaryar Falasdinawa ta Hamas ta bayyana cewa ba za ta bari Isra’ila ta samu wata hujja ta ci gaba da yaki a Gaza ba. Khalil al-Hayyah jigo a kungiyar ta Hamas, ya nuna gazawar gwamnatin Isra’ila na cimma burinta a Gaza kuma ya bayyana cewa kungiyar tana mutunta dukkan alkawuran da ta dauka a...
    Sai dai ya yabawa masu ba da agajin gaggawa, da jami’an tsaro da kuma ‘yan sa-kai da suka yi aiki tuƙuru wajen ceto waɗanda lamarin ya rutsa da su, tare da ba su agaji, yana mai cewa ɗaukin gaggawan da suka kai ya taimaka wajen rage munin ibtila’in. A yayin da take addu’ar Allah ya...
    Wata tanka ɗauke da man fetur ta kife a kan hanyar Lambata zuwa Lapai zuwa Agaie da ke Jihar Neja, lamarin da ya haifar da tsoro da fargaba a tsakanin mazauna yankin. An gano cewa tankar, wadda ta taso daga Legas tana kan hanyarta na zuwa Kano, ta kife ne da sassafe a garin Takalafiya...
      Masu sharhi na wasanni sun bayyana cewa wasan na yau zai kasance mai cike da fasaha da kwarewa, musamman ganin cewa kungiyoyin biyu na da ‘yan wasa matasa masu zafin guiwa kamar Vinicius Jr., Jude Bellingham, da Lamine Yamal, wadanda ke son rubuta sunayensu cikin jerin manyan taurarin da suka taba buga El Classico....
    Mataimakin shugaban ƙasar ya ƙara da cewa kwamitin shugaban ƙasa kan ba da tallafi ya ƙaddamar da rabon naira miliyan 50, inda mutum miliyan 1 za su samu naira dubu hamsin kowanensu tare da wasu shirye-shirye na bunƙasa ƙananan sana’o’i.  Ya ƙara da cewa ƙanana da matsaƙaitan sana’o’i a Jihar Katsina za su samu 250,000...
    Kwamitin Haɗin Gwiwa na Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai kan gyaran kundin tsarin mulkin Najeriya, ya amince da buƙatar ƙirƙiro sabbin jihohi guda shida. Wannan mataki na cikin abin da aka cimma a ƙarshen taron kwana biyu da aka gudanar a Legas, ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, da Mataimakin Kakakin...
    Dasuki, wanda shine shugaban rikon kwarya na Shirin Makomar Matasa A Yanzu, wani shiri na hada matasa da harkokin siyasa da aka kaddamar a ranar 1 ga Oktoba, 2025 a Abuja, ya bayyana cewa sanarwar shirin na cewar kashi 70% na kujerun majalisar wakilai a zaben 2027 su kasance na ‘yan Nijeriya kasa da shekaru...
    Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Cif Femi Fani-Kayode, ya bayyana cewa matsalar kashe-kashen da ake fama da su a sassa daban-daban na ƙasar nan ba ta da alaƙa da addini, illa dai ayyukan miyagu da ke kashe Musulmi da Kirista ba tare da la’akari da bambancin addini ba. Fani-Kayode ya bayyana hakan ne a yayin...
    Waɗannan matsalolin, sun sanya ake yin jigilar  kayan ta kan hanya, a manyan motoci, wanda hakan ya sanya masu ruwa da tsaki a fannin ke ci gaba da kokawa, saboda kuɗaɗen da suke kashewa masu yawa, wajen jigilar kayansu wanda hakan ya saɓawa manufar ta kafa Tashodhin  Jiragen Ruwan ta kantudu. Injiniya Kayode Opeifa Shugaban...
    Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci ya fadawa shugaban Amurka Trump cewa ya ci gaba da rayuwar cikin mafarkinsa! A jawabin da ya gabatar a gaban Majalisar Dokokin Isra’ila ta “Knesset”, Shugaban Amurka Donald Trump ya yi ikirarin cewa ya lalata cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran na zaman lafiya, amma kalmomi biyu kacal da Jagoran Juyin Juya...
    Kungiyar Kurdawa ‘yan tawaye ta PKK ta sanar da janye dukkan dakarunta daga Türkiyya zuwa arewacin Iraki Kungiyar kurdawa ‘yan tawaye ta PKK ta sanar da janye dukkan dakarunta daga cikin kasar Turkiyya zuwa arewacin Iraki a yau Lahadi. Kafafen yada labarai sun ambato wata sanarwa daga kungiyar ‘yan tawayen kurdawar tana cewa: “Ta janye...
    Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta samu nasarar cafke wasu mutum 25 da ake zargi da shirya auren jinsi a samamen da ta kai wani wurin shagali a jihar. A cewar hukumar, an kama mutanen ne da yammacin Asabar a wani wurin taro da ke kan titin Hotoro Bypass a ƙaramar hukumar Tarauni. Sojoji sun...
    Ya ƙara da cewa Kaduna ita ce jihar da ta cika ƙa’idojin da aka shimfiɗa a yarjejeniyar Malabo kan saka hannun jari a harkar noma. Shugaban AUDA–NEPAD a Nijeriya, Honarabul Jabir Abdullahi Tsauni, ya yaba wa gwamnatin Jihar Kaduna bisa samar da kuɗaɗen haɗin gwiwa da suka bai wa shirin damar faɗaɗa zuwa dukkan ƙananan...
    Hukumar Tsaro ta Sibil Difens (NSCDC) reshen Jihar Gombe, ta bayyana alhini bisa rasuwar Kwamishinan Tsaron Cikin Gida na jihar, Laftanar Kanar Abdullahi Bello (mai ritaya). Haka kuma hukumar ta bayyana jimami kan da ɗan sandan da ke tsaron kwamishinan, Sajan Adamu Husaini, da direbansu, wadanda suka rasu a wani mummunan hadarin mota da ya...
    Gwamnatin Jihar Jigawa ta bayar da tallafin Naira miliyan biyu ga iyalan SC Bashir Adamu Jibrin, jami’in hukumar sibil difens (NSCDC) da ya rasu a bakin aiki a kasuwar Shuwarin da ke ƙaramar hukumar Kiyawa. Sakataren Gwamnatin Jihar, Malam Bala Ibrahim, ne ya miƙa tallafin ga matar marigayin a ofishinsa, inda ya ce wannan taimako...
    Babban sakataren Majalisar koli ta tsaron kasar Iran  Ali Larijani ya bayyana cewa; Bayan da aka dauki shekaru biyu ana yi wa mutanen Gaza kisan kiyashi, wanda mutane 70,000 su ka yi shahada, wasu fiye da 100,000 su ka jikkata, suna son a rufe wannan laifin da taron zaman lafiya. Ali Larijani ya kara da...
    A yau Asabar 25 ga wannan wata, ofishin kula da harkokin yankin Taiwan na kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin da ofishin kula da harkokin yankin Taiwan na majalisar gudanarwar kasar sun gudanar da liyafar murnar kebe ranar tunawa da kawo karshen mulkin mallakar Japan a yankin Taiwan, a dakin taro na Diaoyutai...
    Wannan shi ne daya daga cikin martanin NASENI da abokan huldarta don samar da CNG, wannan kuma na daga shirin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na daƙile tasirin cire tallafin man fetur ta hanyar samar da iskar gas mai rahusa. Manufar ita ce a rage dogaro da na’urorin lantarki da ake shigowa da su daga waje,...
    “Ban taba tunanin zan zama taurariya a duniya ba.” Daga Yobe Zuwa Fagen Duniya An haife ta a Jihar Kano kuma ta tashi a Yobe, labarin Nafisa ba shi da wuya kamar yadda yake da ban sha’awa. Mahaifinta ya rasu tun tana jaririya, kuma mijin mahaifiyarta mai suna Alhaji Yusuf Umar Kaigama ya rene ta,...
    Jami’ar Tarayya ta Dutsinma ta zabi Farfesa Muhammed Khalid Othman a matsayin sabon Shugaban Jami’ar na dindindin, tare da amincewar Majalisar Gudanarwar Jami’ar. Da yake zantawa da manema labarai a Dutse, babban birnin jihar Jigawa, Magatakardar Jami’ar, Dokta Musa Ajiya, ya bayyana cewa mai kula da jami’ar (Pro-Chancellor), Ali Abubakar-Jatau, ne ya sanar da nadin....
    Firaministan kasar Sin Li Qiang ya isa Singapore a yau Asabar don ziyarar aiki a kasar bisa gayyatar firaministan Singapore Lawrence Wong. Li ya bayyana cewa, a cikin shekaru 35 da suka gabata tun bayan kafa huldar diflomasiyya, dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu ta ci gaba da kasancewa mai kyau da samun ci gaba,...
    Wannan shi ne daya daga cikin martanin NASENI da abokan huldarta don samar da CNG, wannan kuma na daga shirin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na daƙile tasirin cire tallafin man fetur ta hanyar samar da iskar gas mai rahusa. Manufar ita ce a rage dogaro da na’urorin lantarki da ake shigowa da su daga waje,...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Wakilin Sin: Shawarar GGI Ta Nuna Yadda Za A Jagoranci Bunkasa Makomar MDD October 25, 2025 Daga Birnin Sin Kasar Sin Ta Tsara Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar-biyar Na 15 October 25, 2025 Daga Birnin Sin An Kaddamar Da Nuna Muhimman Shirye-shiryen CMG A Membobin...
    Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya (ABU,  ta ƙaryata labaran da ke yawo a kafafen sada zumunta, cewa tana aikin ƙera makamin nukiliya a ɓoye a cikin jami’ar. A wata sanarwa da ofishin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na jami’ar, ƙarƙashin Malam Auwalu Umar, ya fitar, jami’ar ta bayyana cewa labaran da ake yaɗawa...
    Ana haka ne Gwamna Babagana Umara Zulum ya kai ziyara ƙaramar hukumar, inda ya gana da Misis Duaka a cibiyar lafiya da misalin ƙarfe 8 na dare, lokacin da sauran ma’aikatan duk sun tashi. Wannan aiki na sadaukarwa, juriya da biyayya ga aikinta, ya sa Gwamna Zulum ya fahimci cewa ta himmatu wajen kula da...
    A gun cikakken zaman taro na hudu na kwamitin kolin JKS na 20 da aka gudanar tun daga ranar 20 zuwa 23 ga wannan wata a nan birnin Beijing, an yi bincike da zartas da shirin raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma na shekaru biyar-biyar karo na 15, inda aka gabatar da jagora da burika...
    Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya roƙi Gwamnatin Tarayya ta ɗauki matakin gaggawa a harkar tsaron sararin samaniya, domin hana ’yan ta’adda na amfani da jirage marasa matuƙa wajen kai hare-hare. Zulum, ya faɗi haka ne a ranar Juma’a a garin Mafa, bayan wani hari da Boko Haram suka kai. Sauke Hafsoshin Tsaro: Za...
    “Muna godiya ga sadaukarwar da sojoji da hukumomin tsaro ke yi. Wannan wasa tsakanin tsoffin ’yan wasan Barcelona da tsoffin ’yan wasan Afirka shaida ce ta nasarorin da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta samu wajen dawo da zaman lafiya,” in ji shi. Tsoffin ’yan wasan Barcelona sun isa Nijeriya domin buga wasa da tsoffin...