Leadership News Hausa:
2025-10-31@16:31:35 GMT

Sin Da Amurka Suna Taimaka Wa Juna Da Samun Wadata Tare

Published: 31st, October 2025 GMT

Sin Da Amurka Suna Taimaka Wa Juna Da Samun Wadata Tare

A ranar 30 ga wata ne shugabannin kasashen Sin da Amurka suka gana da juna a birnin Busan na kasar Koriya ta Kudu, lamarin da ya jawo hankulan kasa da kasa, inda shugabannin 2 suka yi musayar ra’ayoyi dangane da huldar da ke tsakanin kasashen 2 da al’amuran da suka jawo hankulansu. Sun amince da inganta hadin gwiwar kasashen 2 a fannonin tattalin arziki da cinikayya da makamashi da kyautata mu’amalar al’adu.

A yayin ganawar, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya jaddada cewa, yana son hada kai da shugaba Donald Trump na Amurka wajen aza harsashi mai kyau na raya huldar da ke tsakanin kasashen 2, tare da samar wa juna kyakkyawan yanayin samun ci gaba. A nasa bangaren, shugaba Trump ya ce, kasar Sin, abokiyar Amurka ce mafi girma. Kasashen 2 za su hada kansu wajen samun nasarar gudanar da manyan ayyuka da dama a duniya. Nan gaba Amurka da Sin za su kara samun nasara a hadin gwiwarsu. Shugabannin 2 sun amince su rika yin mu’amala da juna. Shugaba Trump yana sa ran kai ziyara a kasar Sin a farkon shekara mai zuwa, ya kuma gayyaci shugaba Xi ya ziyarci Amurka.

Masharhanta sun yi nuni da cewa, ganawar shugabannin 2 ta sanya tagomashi kan kyautatuwar huldar da ke tsakanin Sin da Amurka, ta kuma tsara manufar raya huldar kasashen 2 a nan gaba, tare da kwantar da hankulan kasashen duniya.

Abubuwan tarihi da kuma hakikanin abubuwa sun nuna cewa, wajibi ne Sin da Amurka su zama abokan juna. A wannan muhimmin lokaci, ganawar da shugabannin kasashen 2 suka yi ta sake tsara manufar kyautata da raya huldar da ke tsakanin kasashen 2. Muddin kasashen 2 suka aiwatar da muhimman daidaito da shugabannin 2 suka cimma, da mutunta ruhin adalci, tare da martaba juna da samun moriyar juna, to, za a raya huldar da ke tsakanin kasashen 2 ba tare da wata matsala ba, da kuma kara samar da kwanciyar hankali da tabbaci a duniya. (Tasallah Yuan)

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Xi Jinping Ya Halarci Kwarya-Kwaryan Taron Shugabannin APEC Na 32 Tare Da Gabatar Da Jawabi October 31, 2025 Daga Birnin Sin An Gudanar Da Taron Kasa Da Kasa Na Tattaunawa Kan Kirkire-kirkire Da Bude Kofa Da Raba Damar Samun Ci Gaba A Colombo October 30, 2025 Daga Birnin Sin Sin Ta Fitar Da Jerin Sakamakon Tattaunawar Tattalin Arziki Da Cinikayya Da Tawagar Kasar Da Ta Amurka Suka Cimma  October 30, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: huldar da ke tsakanin kasashen 2 raya huldar

এছাড়াও পড়ুন:

Karamar Hukumar Gwarzo Ta Karfafa Yaƙi Da Miyagun Kwayoyi Da Shan Magani Ba Bisa Ka’ida Ba

Shugaban karamar hukumar Gwarzo, Dr. Mani Tsoho, ya yi gargaɗi ga mazauna yankin kan mummunan ɗabi’ar shan magani ba tare da shawarar likita ba, yana mai bayyana hakan a matsayin babban haɗari ga lafiya da ka iya janyo matsalolin da ke barazana ga rai.

Dr. Tsoho ya yi wannan gargaɗi ne yayin da yake ziyarar duba asibitin Gwarzo General Hospital, inda ya gana da marasa lafiya, ya duba yadda ake gudanar da ayyuka, tare da yabawa ma’aikatan lafiya bisa jajircewarsu wajen kula da jama’a.

Ya nuna damuwa cewa, yawancin matsalolin lafiya da ake fuskanta a cikin al’umma na faruwa ne sakamakon amfani ko wuce gona da iri wajen shan magunguna ba tare da shawarwarin ƙwararru ba.

Ya shawarci jama’a da su nemi shawarar likitoci da masu magunguna kafin su sha kowanne irin magani.

Shugaban karamar hukumar ya yi kira ga mazauna yankin da su rika ziyarar asibiti mafi kusa da zarar sun ji wata alamar rashin lafiya don samun kulawa cikin lokaci.

Ya tabbatar da cewa akwai likitoci da nas-nas ƙwararru a cibiyoyin lafiya na yankin da za su samar da ingantacciya kulawa.

Yayin da yake jaddada kudirin gwamnatinsa na inganta harkokin lafiya a dukkan yankuna, Dr. Tsoho ya ce hukumar tana aiki don samar da isassun magunguna, kayan aiki na zamani da kuma horaswa ga ma’aikatan lafiya.

Baya ga batun lafiya, shugaban ya kuma yi kira ga jama’a da su kasance masu lura da tsaro, tare da yin gaggawar kai rahoton duk wani motsi ko mutum da ba su yarda da shi ba ga jami’an tsaro domin daukar mataki cikin lokaci.

 

Daga Khadijah Aliyu

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Manoma a Jigawa Sun Jinjinwa Kungiyar Sasakawa Africa Bisa Bada Tallafi a Harkar Noma
  • Kifewar Kwalekwale: Gwamnan Gombe Ya Jajanta Wa Al’ummar Nafada Kan Mutuwar Matasa Biyar
  • Xi Jinping Ya Halarci Kwarya-Kwaryan Taron Shugabannin APEC Na 32 Tare Da Gabatar Da Jawabi
  • Madagascar Ta Sanar da Kafa Sabuwar Gwamnati Tare da Manyan ‘Yan Adawa
  • Sin Ta Fitar Da Jerin Sakamakon Tattaunawar Tattalin Arziki Da Cinikayya Da Tawagar Kasar Da Ta Amurka Suka Cimma 
  • Karamar Hukumar Gwarzo Ta Karfafa Yaƙi Da Miyagun Kwayoyi Da Shan Magani Ba Bisa Ka’ida Ba
  • Xi Jinping: Sin Da Amurka Za Su Iya Hada Kai Don Sauke Nauyin Dake Wuyansu Na Manyan Kasashe Da Daukar Ainihin Matakai
  • Sulhu Da ’Yan Bindiga Ba Tare Da Sun Ajiye Makamai Ba Tamkar Miƙa Wuya Ne – Gwamna Lawal ga Hukumomin Tsaro
  • Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Yi Ajali Tare Da Jikkata Wasu A Gombe