Aminiya:
2025-10-31@18:03:13 GMT

Shugabannin Kudancin Kaduna za su karrama Janar  Christopher Musa 

Published: 31st, October 2025 GMT

Majalisar Shugabannin Kudancin Kaduna (SKLC) ta kammala shirye-shirye domin gudanar da gagarumar tarbar ga tsohon Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa (mai ritaya).

Za a yi bikin ne domin tunawa da kyakkyawar rawar da majalisar ta ce ya taka a aikin soja da kuma hidimarsa ga kasa.

An sake kama shi a cikin ’yan fashi kwana 5 da fitowa daga kurkuku Ana zargin ɗa da kashe mahaifinsa a Kano saboda hana shi ƙara aure

An shirya gudanar da bikin ne a ranar Asabar, 22 ga watan Nuwamba, 2025, a Babban Filin Wasan na garin Kafanchan, cibiyar kasuwancin Kudancin Kaduna.

A yayin taron majalisar karo na 19 da aka gudanar a Kafanchan, Shugaban SKLC, Ishaya Dare Akau, ya ce za a ba Janar Musa lambar yabo mafi girma ta majalisar wato GCSK.

Akau, ya ce wannan karramawar tana nuni da yadda Janar Musa ya wakilci Kudancin Kaduna, Jihar Kaduna, da Najeriya baki daya cikin kwarewa da cancanta, inda ya bayyana shi a matsayin jakada nagari.

A yayin taron, majalisar ta kuma kaddamar da kwamitin kula da harkokin kudi na Bikin Gargajiya na Shekara-shekara na Kudancin Kaduna (SKFEST), inda aka nada Shugaban Hukumar Haraji ta Jihar Kaduna (KADIRS), Comrade Jerry Adams, a matsayin shugaban kwamitin.

Manyan jami’an gwamnati da dama sun halarci taron karkashin jagorancin Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Rt. Hon. Henry Danjuma Magaji, tare da Mai ba Gwamna shawara kan harkokin siyasa, Hon. Ado Dogo Audu.

Sun yi wa majalisar bayani kan muhimman shirye-shiryen gwamnati, ciki har da amincewar da gwamnatin tarayya ta bayar na farfado da aikin gina hanyar Jere–Kagarko–Jaba–Kwoi–Kafanchan, wadda Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya taimaka wajen ganin tabbatuwarsa.

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

Ranar Foliyo Ta Duniya: Muna Fatan Ganin Karshen Cutar Foliyo A Jihar Katsina -Zulaihat Dikko Radda

A cewar ta a cikin shekarar 2024 jihar Katsina kawai ta samu masu wannan cuta mutum 17 tare da guda biyu a karamar hukumar Danmusa a cikin wannan shekara

Haka kuma Hajiya Zulaihat Radda ya bada tabbacin cewa kowane yaro an tabbatar da ya amshi allurar Riga-kafin shan Inna

Ana jawabin wakilin asusun tallafawa yara na UNICEF na ofishin Kano, Rahama Mohammed Farah ta yabawa kokarin jihar Katsina na dawo da sabon yunkurin kawar cutar shan Inna a Nijeriya baki daya

Ya kuma bayyana cewa asusun kula da kananan yara na UNICEF Yana hadin gwiwa da gwamnatoci da hukumomi da masu ruwa da tsaki a kananan hukumomi domin ganin wajen fadakar da al’umma akan allurar Riga-kafin shan Inna a jihar Katsina.

Shima da yake jawabi shugaban hukumar lafiya a matakin farko ta Jihar Katsina Dakta Shansudeen Yahaya ya yi alkawarin cigaba da wayar da kan al’umma akan wannan cuta ta shan Inna da sauran cututtuka masu kashe yara a kananan hukumomi 34 na jihar Katsina

Wadanda suka shaida wannan bikin ranar ‘Polio’ ta duniya sun hada da hukumar lafiya ta WHO da kuma masu lalurar cutar shan Inna da wakilan asusun UNICEF da matan shugabannin kananan hukumomi 34 na jihar Katsina

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Yan Nijeriya Na Ɗanɗana Kuɗarsu Kan Jinkirta Cire Tallafin Mai – Sarki Sanusi October 31, 2025 Manyan Labarai Allah Ya Kai Manzon Allah (SAW) Muƙami Na Babban Yabo A Cikin Komai October 31, 2025 Manyan Labarai Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP October 31, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Rundunar Sojin Nijeriya Ta Shirya Wa Janar Musa Faretin Gama Aiki
  • Ranar Foliyo Ta Duniya: Muna Fatan Ganin Karshen Cutar Foliyo A Jihar Katsina -Zulaihat Dikko Radda
  • Xi Jinping Ya Halarci Kwarya-Kwaryan Taron Shugabannin APEC Na 32 Tare Da Gabatar Da Jawabi
  • Tinubu Ya Yi Wa Shugabannin Tsaro Ado Da Sabbin Muƙamai
  • Gwamnan Bauchi na neman ƙirƙirar sabbin ƙananan hukumomi 29
  • An Yi Taron Tataunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Moscow, Manama, Da Budapest
  • An kai ƙarar malamai 2 kan zargin ɓatanci ga Annabi a Kaduna
  • ‘Yan Ta’adda Sun Yi Barazanar Sanya Wa Majalisa Bam – Ɗan Majalisa
  • An Kusa Kammala Shirye-shiryen Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas