Waye Zai Lashe Ƙyautar Gwarzon Ɗan Wasan Afrika Na 2025?
Published: 1st, November 2025 GMT
Dan wasan da ya lashe kyautar a bara, Ademola Lookman na Nijeriya ba ya cikin jerin ‘yan wasan da aka lissafo a bana, inda hukumar kwallon kafa ta Afirka (Caf) ta samar da kwamitin kwararru wanda ya zakulo masu horarwa da ‘yan wasan da suka “Taka rawar gani” a tsakanin 6 ga watan Janairu zuwa 15 ga watan Oktoban wannan shekara.
An bayyana sunan mai horar da tawagar ‘yan kwallon kafa ta kasar Cape Berde, Bubista a matsayin mai neman lashe kyautar mai horarwa mafi kwazo bayan jagorantar tawagar kasar ta Blue Sharks wajen samnun gurbin gasar kofin duniya a karon farko a tarihi.
Haka nan tawagar ta tsibirin Cape Berde na cikin masu gogayyar lashe kungiya mafi hazaka a shekarar, tare da Morocco wadda a baya-bayan nan ta lashe kofin duniya na gasar kwallon kafa ta ‘yan kasa da shekara 20.
‘Yanwasa mata na Nijeriya Esther Okoronkwo da Rasheedat Ajibade na cikin wadanda ke neman lashe kyautar zakarun ‘yanwasa mata na Afirka na wannan shekarar. Ya zuwa yanzu dai hukumar CAF ba ta bayyana ranar da za a yi bikin bayar da kyautar ba.
Dan wasa mafi Kwazo: Andre-Frank Zambo Anguissa (Napoli da Kamaru), Denis Bouanga (Los Angeles FC da Gabon), Serhou Guirassy (Borussia Dortmund da Guinea), Achraf Hakimi (Paris St-Germain da Moroko), Oussama Lamlioui (Renaissance Berkane), Fiston Mayele (Pyramids da DR Congo), Iliman Ndiaye (Eberton da Senegal), Bictor Osimhen (Galatasaray da
Nigeria), Mohamed Salah (Liberpool da Masar), Pape Matar Sarr (Tottenham Hotspur da Senegal).
Mai tsaron raga na maza: Yassine Bounou (Al Hilal da Moroko), Aymen Dahmen (CS Sfadien da Tunisia), Marc Diouf (TP Mazembe da Senegal), Edouard Mendy (Al-Ahli da Senegal), Munir Mohamedi (RS Berkane da Moroko), Stanley Nwabali (Chippa Utd da Nijeriya), Andre Onana
(Trabzonspor da Kamaru), Ahmed El Shenawy (Pyramids da Masar), Bozinha (Chabes da Cape Berde), Ronwen Williams (Mamelodi Sundowns da Afirka ta Kudu).
Mai horar da kungiyar maza: Bubista (Cape Berde), Moine Chaabani (Renaissance Berkane), Hossam Hassan (Masar), Krunoslab Jurcic (Pyramids), Mohamed Ouahbi (Moroko U20), Romuald Rakotondrabe (Madagascar), Walid Regragui (Moroko), Tarik Sektioui (Moroko U23), Pape Thiaw (Senegal), Sami Trabelsi (Tunisia).
Tawagar maza: Algeria, Cape Berde, Masar, Ghana, Ibory Coast, Moroko, Moroko U20, Senegal, Afirka ta Kudu, Tunisia. ‘Yan wasa Mata da ke takarar lashe zakarun Afirka na shekara ta 2025.
‘Yar wasa mafi kwazo: Rasheedat Ajibade (Paris St-Germain da Nijeriya), Barbra Banda (Orlando Pride da Zambia), Portia Boakye (Hapoel Petah Tikba da Ghana), Tabitha Chawinga (Lyon da Malawi), Temwa Chawinga (Kansas City da Malawi), Ghizlaine Chebbak (Al Hilal da Moroko), Mama Diop (Strasbourg da Senegal), Rachael Kundananji (Bay FC da Zambia),
Sanaa Mssoudy (AS FAR da Moroko), Esther Okoronkwo (AFC Toronto da
Nijeriya).
Mai tsaron raga na mace: Sedilame Boseja (Mamelodi Sundowns da Botswana), Andile Dlamini (Mamelodi Sundowns da Afirka ta Kudu), Habiba Emad (FC Masar da Masar), Khadija Er-Rmichi (AS FAR da Moroko), Fatoumata Karantao (MUSFAS Bamako da Mali), Cynthia Konlan (Swieki United da Ghana), Adji Ndiaye (AS Bambey da Senegal), Fideline Ndoy (TP
Mazembe da DR Congo), Chloe N’Gazi (Marseille da Algeria), Chiamaka Nnadozie (Brighton & Hobe Albion da Nijeriya).
Mai horar da kungiyar mata: Genobeba Anonman (15 de Agosto), Kim Bjorkegren (Ghana), Lamia Boumehdi (TP Mazembe), Desiree Ellis (Afirka ta Kudu), Carol Kanyemba (Zambia U17), Adelaide Koudougnon (Ibory Coast U17), Justin Madugu (Nijeriya), Bankole Olowookere (Nijeriya U17), Siaka Gigi Traore (ASEC Mimosas), Jorge Bilda (Moroko).
Tawagar mata: Kamaru U17, Ghana, Ibory Coast U17, Mali, Morocco, Nijeriya, Nijeriya U17, Afirka ta Kudu, Tanzania, Zambia U17. Za ku iya ganin cikakken jerin wadanda ke neman lashe kyautukan a shafin hukuma Caf. [1]
ShareTweetSendShare MASU ALAKAকীওয়ার্ড: da Nijeriya
এছাড়াও পড়ুন:
Super Falcons ta samu gurbin buga Kofin Afrika
Babbar tawagar ƙwallon ƙafa ta matan Najeriya Super Falcons ta samu tikitin buga gasar cin kofin nahiyyar Afrika ta mata ta 2026 da ƙasar Morocco zata karɓi baƙunci.
Super Falcons ta samu nasarar ne bayan tashi kunnen doki 1 da 1 da takwararta ta jamhuriyyar Benin a filin wasa na MKO Abiola da ke birnin Abeokuta a yammacin jiya Talata.
Gwamnatin Gombe ta fara tantance ma’aikata don kawar da na bogi An ceto jaririya ’yar mako daya da haihuwa da aka sayar a AnambraKunnen doki ya bai wa Najeriya nasarar shiga cikin jerin ƙasashen da zasu buga kofin na Afrika, bayan Falcons ta doke Benin da ci 2 – 0 a makon jiya a birnin Cotonou.
Hakan na nufin a wasanni biyu da ƙungiyyoyi suka fafata Najeriya ta samu nasara da ci 3-1.
Wannan dai shi ne karo na 14 da Falcons zata buga kofin nahiyyar Afrika da ƙasar Morocco zata karɓi baƙunci daga 17 ga watan Maris zuwa 3 ga watan Afrilu na 2026.
Najeriya ta lashe gasar sau 10 cikin gasanni 14 da aka buga a tarihi.