Majalisar Dinkin Duniya ta damu da hare-haren Amurka a Caribbean da Pacific
Published: 1st, November 2025 GMT
Babban Kwamishinan Kare Hakkin Dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya ya soki hare-haren sama da Amurka ta kai wa jiragen ruwa a yankin Caribbean da Pacific, wanda ya kasance keta dokokin kare hakkin dan adam na duniya.
“An ruwaito cewa an kashe mutane sama da 60 a jerin hare-haren da sojojin Amurka ke kai wa jiragen ruwa a Caribbean da Pacific tun farkon watan Satumba, wadanda ake zargin suna da hannu a safarar miyagun kwayoyi, a cikin wani yanayi da ba su da hujja a karkashin dokokin kasa da kasa,” in ji Volker Turk a cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Juma’a.
Babban jami’in Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana hare-haren a matsayin “abin da ba za a yarda da shi ba” kuma ya bukaci Washington da ta “kawo karshen irin wadannan hare-hare ta kuma dauki dukkan matakan da suka dace don hana kisan gillar da ake yi wa mutanen da ke cikin wadannan jiragen ruwa ba bisa ka’ida ba, ba tare da la’akari da laifukan da ake zarginsu da aikatawa ba.”
Amurka ta yi ikirarin cewa wadannan ayyuka wani bangare ne na yaki da safarar miyagun kwayoyi da ta’addanci.
Duk da haka, Turk ya nuna cewa yaki da safarar miyagun kwayoyi a kan iyakoki “al’amari ne na tilasta bin doka.”
“Dangane da ƙarancin bayanai da hukumomin Amurka suka bayyana a bainar jama’a, da alama mutanen da ke cikin jiragen ruwan da aka kai hari ba su da wata barazana ga rayukan wasu, kuma ba a yi amfani da karfin soji mai tsanani a kansu ba a karƙashin dokokin kasa da kasa,” in ji shi.
Volker Turk ya yi kira da a “yi bincike mai zaman kansa cikin sauri, kuma ya yi kira ga Amurka da ta yaki fataucin na haramtacciyar hanya ta hanyar kamawa, da gurfanar da wadanda ake tuhuma cikin adalci, da kuma bin ka’ida.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Israila Ta Kai Hari Kan Ofishin kungiyar UNICEF Dake Gaza A November 1, 2025 Amurka Na Shirin Kai Hari Kan Kasar Venzuwela A Kowanne Lokaci November 1, 2025 Iran Ta Sanya Da Ranar 30 Ga Watan Nuwamba A Matsayin Ranar Kasa Ta Tsibirai 3 October 31, 2025 Isra’ila Na Ci Gaba Keta Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta A Gaza October 31, 2025 An Tube Yarima Mai Jiran Gado Na Birtaniya Bayan Da Aka Tabbatar Da Laifinsa October 31, 2025 Kasashen Pakistan Da Afghanistan Sun Tsawaita Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta October 31, 2025 M D Duniya Tayi Gargadi Game Da Gwajin Nukiliya Da Amurka Ta Sanar Za ta yi October 31, 2025 Sudan Ta Yi Kira Ga Kwamitin Tsaro Da Ya Ayyana RSF A Matsayin Kungiyar ‘Yan Ta’adda October 31, 2025 Araqchi: Gwajin Makaman Nukiliya Na Amurka Babbar Barazana Ce Ga Duniya October 31, 2025 Masar da Eritrea Sun Tattauna Bukatar Tallafawa Kasar Sudan October 31, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Rasha Da Amurka Sun Sake Dawo Da Gwaje-gwajen Makaman Nukiliya
Kasar Rasha ta sanar da samun nasarar gwajin jirgi maras matuki na nukiliya wanda yake ninkaya a cikin ruwa.
Gwajin dai ya biyo bayan wasu gwaje-gwajen da Rashan ta yi ne na makamai masu linzami samfura mabanbanta masu iya daukar makaman Nukiliya.
Jirgin maras matuki mai daukar makamin Nukiliya yana a karkashin rundunar sojan ruwan kasar,da aka bai wa sunan; Bosidon. Bugu da kari shi kanshi jirgin yana aiki ne da nukiliya a matsayin makamanshin da yake tafiyar da shi.
Shugaban kasar Rasha Vladmir ya ce; babu wata na’ura wacce za ta iya dakatar da wannan jirgin mai ninkaya a cikin ruwa na Nukiliya.
Shugaban kasar ta Rasha ya kara da cewa; Wannan sabon makamin babu kwatankwacinsa a duniya saboda saurinsa da kuma nisan inda zai iya isa.
A gefe daya shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bai wa sojojin kasar umarnin sake bude gwaje-gwajen makaman Nukiliya.
Shugaban kasar ta Amurka Donald Trump ya rubuta a shafinsa na “Truth Social” cewa, ya bayar da umarnin sake dawo da gwaje-gwajen makaman Nukiliya.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kasar Czech Ta Hana Wa Wani Sojan HKI Shiga Kasar Bisa Gargadin Faransa October 30, 2025 Lebanon HKI Sun Kutsa Cikin Kasar Lebanon October 30, 2025 Adadin Falasdinawan Da Su Ka Yi Shahada A Cikin Sa’o’i 24 Sun Haura 100 October 30, 2025 Amurka Ta Hana Marubuci Dan Nigeria Wole Soyinka Izinin Shiga Amurka October 30, 2025 Pakistan Tayi Barazanar Daukar Mataki Bayan Rushewar Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta Da Afghanistan. October 29, 2025 IRS: Sanya Sabbin Takunkumi Kan Kasar Iran Zai Haifar Da Mummunan Sakamakon A Yankin October 29, 2025 An saka dokar Ta Baci Bayan Barkewar Zanga-zanga A Zaben Shugaban Kasar Tanzaniya October 29, 2025 Majalisar Dattawa A Najeriya Ta Tantance Sabbin Manyan Hafsoshin Sojin Kasar October 29, 2025 Shugaban kasar Iran Ya Taya Takwaransa Na Turkiya Murnar Zayowar Ranar Samun Yancin Kai October 29, 2025 Bayan Kwace Birnin Al-Fasher Kungiyar Rapid Support Forces Suna Ci Zarafin Al’Umma October 29, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci