2025-09-24@11:18:36 GMT
إجمالي نتائج البحث: 7425

«Lewandowski»:

    Kamfanin GTCO, mamallakin bankin GT, ya bayyana samun ribar Naira biliyan 601 a watanni shida na farkon shekarar 2025. Sai dai bankin ya ce duk da haka ribar tasa raguwa ta yi a kan ta Naira tiriliyan daya da ya ci a farkon shekarar da ta gabata. Kotun Indiya ta daure dan Najeriya shekara 10...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci a cikin jawabinsa ya bayyana cewa: Dangane da hadin kan al’ummar Iran, batu na farko shi ne cewa a lokacin yakin kwanaki goma sha biyu, hadin kai da hadin kan al’ummar Iran ya sanya makiya kunya. Jagoran ya jaddada cewa tun tsakiyar tsakiyar yakin makiya sun gane cewa ba za...
    Ali Larijani, sakataren majalisar koli ta tsaron kasa, ya rubuta a daren Talata a wani sako da ya wallafa a dandalin sada zumunta na X:“Da farko dai Amurka ta fice daga JCPOA, sannan Turai ta kasa cika alkawuran da ta dauka, a karshe ma sun kai harin bama-bamai, yanzu haka jam’iyyu suna yin kamar su...
    Babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa ya sanar da cewa: Masu binciken hukumarsa suna kan hanyarsu ta zuwa Iran Babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa Rafael Grossi ya bayyana cewa: Masu sa ido na hukumar IAEA na kan hanyarsu ta zuwa Iran. Rafael Grossi ya...
    Kasashen Burkina Faso, Nijar, da Mali sun fice daga kotun hukunta manyan laifuka ta duniya Kasashen Burkina Faso, Mali, da Nijar sun sanar a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar na ficewa daga yarjejeniyar Rome ta kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC. Sanarwar wadda wakilin gwamnati kuma ministan sadarwa na Burkina Faso,...
    Wata kotu ta musamman a Coimbatore da ke kasar Indiya, ta yanke wa wani dan Najeriya mai suna Samson Chukwunonso hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari kan laifin safarar miyagun kwayoyi. Jaridar Times of India ta ruwaito cewa lamarin ya faro tun a watan Yuli na shekarar 2012, lokacin da jami’an hukumar hana sha...
    A yau Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bukaci hada karfi da karfe wajen gina yankin Xinjiang ya zama mafi kyau a cikin tsarin zamanantar da kasar Sin. Ya bukaci hakan ne yayin da ya gana da wakilai daga dukkan kabilu da sauran fannonin rayuwar al’umma a yankin Xinjiang mai cin gashin kansa na...
    Rundunar ’yan sanda a Jihar Kano ta sanar da cafke wani mutum da ke yi mata sojan-gona yana yaudarar jama’a domin karɓar musu kuɗi. An cafke wanda ake zargin ne a ranar Lahadi, 21 ga Satumbar 2025 a yankin Kofar Dawanau, sanye da kayan ’yan sanda, wanda bayanai suka ce ya daɗe yana aika-aikar. An yi...
    Mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana cewa tuni gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta ɗauki manyan matakai na gyara tattalin arziki, ciki har da cire tallafin man fetur, haɗa farashin musayar kuɗi, da kuma sabunta tsarin haraji da kwastam.   Ya ƙara da cewa waɗannan sauye-sauye sun fara samar da yanayi mai kyau ga masu zuba jari,...
    Ya zuwa ranar 23 ga watan Satumba agogon Beijing, kasashe 152 cikin 193 na Majalisar Dinkin Duniya sun amince da Falasdinu a matsayin kasa. A cikin kasashe biyar masu kujerun dindindin a kwamitin sulhun MDD, Amurka ce kadai ba ta amince da kafuwar kasar Falasdinu ba. Wannan guguwar ta amincewa da kafuwar kasar Falasdinu ta...
    Wata Kotun Soji ta yanke wa wasu sojoji uku hukuncin ɗaurin rai da rai kan sayar da makamai da harsasai ba bisa ka’ida ba a Maiduguri, Jihar Borno. Kotun sojin ƙarƙashin jagorancin Birgediya-Janar Mohammed Abdullahi, ta bayyana cewa an yanke wa mutum uku daga cikin sojojin huɗu hukuncin ɗaurin rai da rai yayin da aka...
      Wannan ne dai karo na farko da adadin gejin kuɗin ruwa ya yi ƙasa, wato mafi ƙaranci a cikin shekaru biyar.   Gwamnan na CBN ya ce an yanke shawarar rage kuɗin ruwan ne domin ci gaba da bunkasuwar tattalin arzikin cikin gida (GDP), da karyewar hauhawar farashi, wanda tsawon watanni biyar kenan ana...
    Hassan Jibril wanda ke zaune a yankin Pata da ke fama da ambaliyar ruwa a duk shekara, ya ce a yanzu haka suna cikin fargaba, duk da cewa a ko wace shekara sun saba yin gudun hijira tun bayan afkuwar ambaliyar ruwa ta 2012 da ta mamaye wasu al’ummomi a wasu kananan hukumomin jihar.  ...
      A cewar kakakin rundunar ‘yansandan Kano, binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa, Shitu ba jami’in ‘yansanda ba ne kuma ba konstabulari na musamman ba ne.   Ya kara da cewa, za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu, yayin da ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike domin...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa dandalin jawabi a MDD wata dama ce ta kasashen duniya su bayyana ra’ayinsu kuma Iran zata bayyana ra’ayinta a gobe Laraba 23 ga watan Satumba na wannan shekara ta 2025. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka jim kadan fafin ya...
    Tom Barrack, jakadan Amurka a turkiya sannan manzonta na musamman a Siriya da Lebanon ya amince da cewa gwamnatin Trump tana son ta hada mutanen kasar Lebanon da sojojin kasar yaki. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Tom Barrack yana fadar haka a wata hirar da yayi da yan jaridu a birnin...
    Ana zargin wata matar aure, Rabi Nuhu da ke garin Magama Gumau a ƙaramar hukumar Toro ta Jihar Bauchi, da cin zarafin wata yarinya ’yar shekara biyar ta hanyar ƙone mata al’aura, saboda zargin tana yawan yin fitsarin kwance. Wakilinmu ya gano cewa yarinyar marainiya ce wadda mahaifiyarta ta rasu kusan shekara ɗaya da ta...
    Ana zargin wata matar aure, Rabi Nuhu da ke garin Magama Gumau a ƙaramar hukumar Toro ta Jihar Bauchi, da cin zarafin wata yarinya ’yar shekara biyar ta hanyar ƙone mata al’aura, saboda zargin tana yawan yin fitsarin kwance. Wakilinmu ya gano cewa yarinyar marainiya ce wadda mahaifiyarta ta rasu kusan shekara ɗaya da ta...
    Kwamitin da ke kula da tsare-tsare da manufofin kuɗi na Babban Bankin Najeriya (CBN) ya zaftare maki 60 daga nauyin kuɗin ruwa da ke kan masu karɓar basussuka.  Wannan dai shi ne karo na farko cikin shekaru biyar da aka samu babban bankin ya yi rangwamin kuɗin ruwa a ƙasar. CBN ɗin ya ce kwamitin a...
    Haka kuma sun tabbatar da cewa manoma da suka koma gonakinsu kwanan nan sun samu kariya. Babu wanda aka sace ko ɗaya, yayin da jama’ar yankin ke ci gaba da zama lafiya. A ranar 19 ga watan Satumba, Birigediya Janar Ugochukwu Unachukwu, wanda shi ne muƙaddashin kwamandan rundunar sojojin 7 Division, ya kai ziyara Banki...
    An kashe wani ɗan sanda mai muƙamin Sajan a wani hari da ’yan bindiga suka kai wani shingen bincike, inda suka ɗauke bindigarsa bayan sun halaka shi a Jihar Taraba. Wata majiyar ta bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10 na dare a garin Tella, cikin Ƙaramar Hukumar Gassol, lokacin da ’yan...
    Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da ɗan Majalisar Dokokin Jihar Filato, mai wakiltar Mazaɓar Pankshin ta Kudu, Laven Denty Jacob. A yammacin ranar Litinin aka yi garkuwa da shia gidansa da ke Anguwan Kagji, a Unguwar Dong, a Ƙaramar hukumar Jos ta Arewa. Wani na kusa da shi ya tabbatar wa manema labarai cewa...
    Sojojin HKI sun amabci cewa sojoji biyu sun halaka a wani kwanton bauna da mayaka a Gaza su ka yi, daga ciki har da kwamandan rundunar “Folcan”. Kakakin sojan HKI ya bayyana cewa wanda aka kashe din shi ne Manjo Shahir Natna’il, sai kuma Midgal Haimik a wani fada da aka yi a arewacin Gaza....
    ‘Yan bindiga sun sace ɗan majalisar dokokin Jihar Filato, mai wakiltar Pankshin Kudu, Laven Denty, a gidansa da ke unguwar Dong na ƙaramar hukumar Jos ta Arewa. A makon da ya gabata ma, Jaridar LEADERSHIP ta ruwaito yadda ‘yan bindiga suka kutsa cikin unguwar Dong, inda suka yi garkuwa da wani mai yi wa ƙasa...
    Ya ce Kano na cikin hatsari saboda cunkoson jama’a da kuma zirga-zirgar mutane daga wurare daban-daban. KNCDC ta gudanar da cikakken bincike a Ungogo, inda aka duba unguwar da marar lafiyan yake da kuma asibitocin da ya ziyarta. Duk wanda aka bincika yana cikin ƙoshin lafiya kuma babu wanda ya kamu da cutar. Farfesa Abbas...
    Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta yi wa tsohon Ministan Shari’a kuma Antoni-Janar na Gwamnatin Tarayya, Abubakar Malami, tambayoyi a kan harin da aka kai wa ayarin motocinsa a Jihar Kebbi. An gudanar da tambayoyin ne a ofishin hukumar na Birnin Kebbi a ranar Litinin, inda Malami ya bayyana cewa an yi masa tambayoyin...
    Ya ce Kano na cikin hatsari saboda cunkoson jama’a da kuma zirga-zirgar mutane daga wurare daban-daban. KNCDC ta gudanar da cikakken bincike a Ungogo, inda aka duba unguwar da marar lafiyan yake da kuma asibitocin da ya ziyarta. Duk wanda aka bincika yana cikin ƙoshin lafiya kuma babu wanda ya kamu da cutar. Farfesa Abbas...
    Majalisar Dokoki ta Kasa ta ɗage ranar dawowarta daga hutu zuwa 7 ga watan Oktoba, 2025. Karin bayani na tafe..
    Masana da shugabanni da suka halarci taron, ciki har da Farfesa Isah Ali Pantami, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, da sauran fitattun malamai, sun yaba da wannan ƙudiri na gwamnatin Katsina. Rahotanni sun nuna cewa sama da yara 300,000 ne ba sa zuwa makaranta a Katsina, ciki har da dubban almajirai da ‘yan mata. Wannan ne...
    Rundunar ’Yan sandan Jihar Kebbi ta cafke wasu mutum huɗu a yankin Kamba da ke jihar, bisa zargin su da shigar da babura uku da suka saya daga Jamhuriyar Benin domin kai wa kungiyar ta’addanci ta Lakurawa. Haka kuma an kama wani Mubarak Ladan bayan ya yi tayin cin hancin naira dubu dari shida (₦600,000)...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Kisan jami’an tsaro na cigaba da zama ruwan dare a Najeriya, lamarin da ya daɗe yana tayar da hankali, amma a ‘yan kwanakin nan abin ya ƙara muni.   Misali, kwanan nan a an kashe wasu jami’an ‘yan sanda a kananan hukumomin Katsina-Ala da Ukum a jihar Benue, inda...
    Mataimakin firaministan kasar Sin He Lifeng ya gana da tawagar ‘yan majalisar wakilan Amurka karkashin jagorancin Adam Smith a yinin yau Litinin 22 ga wata a birnin Beijing. He Lifeng ya ce, a ranar 19 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping da shugaba Donald Trump sun yi wata tattaunawa ta wayar tarho, kuma sun...
    Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya ayyana gobe Talata, a matsayin ranar ɗaya ga watan Rabi’ul Thani, 1447 bayan hijira, wanda ya kawo ƙarshen watan Rabi’ul Awwal, 1447, daidai da ranar 23 ga Satumba, 2025. Sanarwar ta fito ne a wata takarda da Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaid, wanda shi ne shugaban kwamitin da...
    Sanarwar ta ƙara da cewa, Gwamna Lawal ya jaddada cewa tsarin dimokuraɗiyyar Kanada, ƙarfafan tattalin arziƙi, hakar ma’adinai ta hanyar da ta dace, da kuma harkokin kasuwanci masu zaman kansu masu kirkire-kirkire sun sanya ta zama abokiyar haɗin guiwar da ta ta dace ga Afrika.   Ya ce, “Idan Afrika za ta cika burinta gaba...
      Haddadiyar Kungiyoyin Makiyaya na kasashen Africa (CORET) ta bayyana cewa an samu karin yawan ɗalibai a makarantun makiyaya cikin watanni goma da aka fara shirin ciyar da ɗalibai.   Babban Sakataren CORET, Muhammed Bello Tukur, ya bayyana haka a taron kwana ɗaya da aka gudanar a Kaduna domin ƙara wa ma’aikata da abokan hulɗarsu...
    Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta ce a karon farko za ta shirya taron zuba jari da samar da masana’antu na Arewacin Najeriya, wanda aka shirya gudanarwa a ranakun 29 da 30 ga watan Satumba a Abuja. Taron wanda aka shirya tare da hadin gwiwar jihohin arewa 19 da kuma kamfanin raya yankin – NNDC, na...
    Tawagar jami’an diflomasiyyan Falasɗinu ta gudanar da bikin ɗaga tutar ƙasar a Litinin ɗin nan a birnin Landan kamar yadda kafar labarai ta DW ta ruwaito. Bikin ɗaga tutar na zuwa ne kwana guda bayan da Birtaniya ta amince da Falasɗinu a matsayin kasa mai cin gashin kanta. CAC ta soma yi wa kamfanoni rijista...
    A halin yanzu, shugaba Bola Tinubu yana ganawa da gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara a fadar shugaban kasa dake Abuja a yammacin yau Litinin. Ganawar na zuwa ne kwanaki kadan bayan Fubara ya koma ofis a ranar 19 ga watan Satumba bayan da Shugaba Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci da aka kafa a jihar Ribas...
    Iran ta bakin kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar, ta bayyana cewa “Kisan kare dangi da ake ci gaba da yi a zirin Gaza ya zama babban gwaji ga Majalisar Dinkin Duniya. Idan muna son kungiya mai inganci kuma mai amfani, dole ne mambobinta su dauki matakin gaggawa tare da tsayin daka wajen dakatar da wannan...
    Iran ta yi Allah wadai da harin da aka kai kan wani masallaci a Sudan tare da yin kira da a kawo karshen hare-haren da ake kai wa fararen hula cikin gaggawa. Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta yi Allah-wadai da harin na baya-bayan nan da aka kai da jirage marasa matuka a wani masallaci a...
    Majalisar Wakilai ta bayyana cewa ta amince da duk wasu tsare-tsare da dabarun karɓo rancen kuɗaɗe na Shugaba Bola Tinubu, bisa la’akari da ƙoƙarin da yake yi na farfaɗo da tattalin arziki da kuma rage talauci a ƙasar nan. Shugaban Majalisar, Abbas Tajudeen ne ya bayyana hakan a yayin da yake jawabi ranar Litinin, a...
    Hukumar da ke kula da yi wa Kamfanoni Rajista ta Najeriya (CAC) ta ƙaddamar da sabon shafin intanet mai amfani da fasahar ƙirƙirarriyar basira wato AI domin sauƙaƙa rajistar harkokin kasuwanci da kamfanoni a Najeriya. Shugaban Hukumar, Hussaini Ishaq Magaji (SAN), ne ya bayyana a yayin taron masu ruwa da tsaki da hukumar ta shirya...
    Yayin da “bikin girbi na manoman kasar Sin” na takwas ke karatowa, babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin wato JKS, shugaban kasar, kuma shugaban kwamitin kolin soja Xi Jinping, a madadin kwamitin kolin JKS, ya mika gaisuwar bikin, da fatan alheri ga manoma da ma’aikatan dake gudanar da ayyukan da suka shafi...
    Majalisar Wakilai ta bayyana cewa ta amince da duk wasu tsare-tsare da dabarun karɓo rancen kuɗaɗe na Shugaba Bola Tinubu, bisa la’akari da ƙoƙarin da yake na farfaɗo da tattalin arziki da kuma rage talauci a ƙasar nan. Shugaban Majalisar, Abbas Tajudeen ne ya bayyana hakan a yayin da yake jawabi ranar Litinin, a taron...
    Mataimakin shugaban jami’ar ya ja hankalin gwamnati da cewa, yawan al’ummar Nijeriya kusan miliyan 230, kusan kashi 30 cikin 100 na matasa ne a halin yanzu ke makaranta ko kuma suke koyon sana’o’i.   Don haka, ya yi gargadin cewa, hakan ya bar wani kaso mai tsoka na matasa da ba su zuwa makaranta ko...
    Na hudu, an yi ta samu ci gaban sayayya sakamakon masu yawon bude ido daga ketare. Bisa ga manufar rage haraji lokacin barin kasa da kasar Sin ke gudanarwa, an shirya shirin “Sayayya a Sin” yadda ya kamata, wanda hakan ya canza fa’idar yawan baki daga ketare da suke yawon shakatawa a kasar zuwa habaka...
    A yau Litinin Allah Ya yi wa Sarkin Ruman Katsina kuma Hakimin Batsari, Alhaji Tukur Ma’azu, rasuwa. Marigayin, wanda ya shafe shekaru 74 a duniya, ya daɗe yana fama da jinya gabanin rasuwarsa. Hisbah ta kama masu safarar mata zuwa Saudiyya a Kano Jariri ya mutu a bayan uwarsa yayin tsere wa ’yan bindiga a...
    Mutune 70 da aka yi garkuwa da su sun samu ƴanci a Jihar Katsina, bayan yarjejeniyar sulhu da aka ƙulla da fitaccen shugaban ƴan bindiga, Isiya Kwashen Garwa. A wani faifan bidiyo da ya bayyana, Garwa ya saki mutane 40 a ƙaramar hukumar Faskari, kwanaki biyu bayan ya fara sakin wasu 30, wanda hakan ya...
    Wani jariri ya rasu a bayan mahaifiyarsa a yayin da take guje wa harin ’yan bindiga a kauyen Allawa da ke Karamar Hukumar Shiroro a Jihar Neja. Sarkin yankin Bassa, Bagudu Amos, ne ya bayyana hakan a lokacin taron tattaunawa da mata kan zaman lafiya da kare su daga cin zarafi, mai taken: “Ƙarfafa kariya...
    Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama gungun wasu mutane da ake zargi da safarar mata zuwa kasar Saudiyya. Hisbah ta dakile yunkurin mutanen ne a yayin da suke kokarin safarar wasu mata hudu daga jihohin Kano da Jigawa da Yobe, ta hannun wakilansu da ke sassan kasashen Yammacin Afirka? Mataimakin Babban Kwamnand Hukumar, Dakta...