“Amurka ba za ta tsaya kawai tana kallo ba yayin da irin waɗannan ta’addancin ke faruwa a Nijeriya da sauran ƙasashe.

“Mun shirya, muna da ƙarfi da niyyar kare Kiristoci a faɗin duniya,” in ji Trump.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai An Tsare Wani Mutum A Gidan Yari Kan Zargin Kashe Matarsa Saboda Ƙuli-Ƙuli A Kano October 31, 2025 Manyan Labarai Makarantar Kogi Poly Ta Bankaɗo Masu Ƙirƙirar Takardun Kammala Karatu na Bogi October 31, 2025 Manyan Labarai Kifewar Kwalekwale: Gwamnan Gombe Ya Jajanta Wa Al’ummar Nafada Kan Mutuwar Matasa Biyar October 31, 2025.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Babu wani uzuri da za a yi wa sabbin hafsoshi kan matsalar tsaron Nijeriya — Tinubu

Shugaba Bola Tinubu ya nemi sabbin hafsoshin tsaron ƙasar su zage damtse domin magance duk wata barazanar tsaro da ake fuskanta a halin yanzu da ma wadda ka iya kunnowa nan gaba.

Shugaban ya gargadi sabbin hafsoshin tsaron cewa ’yan Nijeriya sakamako kawai suke buƙata, ba uzuri ba, saboda haka dole ne su cika aikin da aka ɗora musu.

Gwamnatin Gombe ta saurari ra’ayoyin jama’a kan kasafin kuɗin 2026 Ƙwallo ta kashe ɗan wasan Cricket

Tinubu ya bayyana hakan ne bayan bikin ƙara wa sabbin hafsoshin tsaron da shugabannin rundunonin soji girma da aka gudanar a fadar shugaban ƙasa yau Alhamis a Abuja.

A cewarsa, “Barazanar tsaro na ƙara sauyawa a kodayaushe, kuma abin da ya fi damun gwamnatinmu shi ne ɓullar sababbin ƙungiyoyin ’yan bindiga a Arewa ta Tsakiya, da Arewa maso Yamma, da wasu sassa a Kudanci.”

A ranar Laraba ce Majalisar Dattawa da ta Wakilai suka amince da naɗin Laftanar Janar Olufemi Oluyede a matsayin Babban Hafsan Tsaro; Manjo Janar Waidi Shaibu a matsayin Hafsan Sojan Ƙasa; Rear Admiral Idi Abbas Hafsan Sojan Ruwa; Air Marshall Kennedy Aneke Hafsan Sojan Sama; da Manjo Janar Emmanuel Undiendeye a matsayin Shugaban Tattara Bayanai na Soja.

“Ba zai yiwu mu ƙyale wannan sabuwar barazanar ta ci gaba ba. Dole ne mu ɗauki mataki da wuri. Mu sare kan macijin.

“’Yan Najeriya suna sa rana ganin sakamako, saboda haka babu wani uzuri da za su karɓa. Ina kuma kira da ku kasance masu dabaru da hangen nesa da kuma jarumta.

“Mu kasance mun tari hanzarin duk waɗanda ke neman tayar da zaune tsaye a ƙasarmu,” in ji Tinubu.

Yayin bikin, an ƙara wa Olufemi Oluyede muƙami zuwa Janar, Waidi Shaibu zuwa Laftanar Janar, Idi Abbas zuwa Vice Admiral, da Kevin Aneke zuwa Air Vice marshall, da kuma Emmanuel Undiendeye zuwa Laftanar Janar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Amurka ta sanya Najeriya cikin ƙasashen da ake yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi
  • An Tsare Wani Mutum A Gidan Yari Kan Zargin Kashe Matarsa Saboda Ƙuli-Ƙuli A Kano
  • Sudan Ta Yi Kira Ga Kwamitin Tsaro Da Ya Ayyana RSF A Matsayin Kungiyar ‘Yan Ta’adda
  • Matsalar Talauci Da Rashin Tsawon Rai Da ‘Yan Nijeriya Ke Fuskanta
  • Babu wani uzuri da za a yi wa sabbin hafsoshi kan matsalar tsaron Nijeriya — Tinubu
  • Sheikh Gumi Ya Yabi Tinubu Kan Afuwar Da Ya Yi Wa Maryam Sanda 
  • Yadda Ta Gudana A Taron Karɓar Ƴan Majalisa Shida Da Suka Koma APC
  • Majalisar Dattawa Ta Tabbatar Da Bernard Doro A Matsayin Ministan Harkokin Jin Ƙai
  • Wata 3 Da Naɗin Shugaban APC, Sunan Yilwatda Har Yanzu Na Nan A Matsayin Minista A Shafin Ma’aikatar