Ya Kamata Sin Da Amurka Su Zama Kawayen Juna Ba Abokan Gaba Ba
Published: 31st, October 2025 GMT
Sai dai don neman cimma burinta na “sake mayar da kasar Amurka zakaran gwajin dafi”, kasar Amurka ta sha daukar matakai na dakile ci gaban kasar Sin, ciki har da katse huldar tattalin arziki da ita da ma sanya takunkumai ga kamfanoninta masu ci gaban kimiyya da sauransu, duk da hakan, kasar Sin ta kiyaye bunkasar tattalin arzikinta yadda ya kamata, har ma karuwar tattalin arzikinta ta kai kaso 5.
Ganawar da aka yi a wannan karo ta kasance ta farko a tsakanin shugabannin kasashen biyu tun bayan da shugaba Trump ya sake hawa karagar mulkin kasar Amurka. Kafin wannan kuma, shugabannin biyu sun taba tattaunawa da juna ta wayar tarho har sau uku, don nuna alkiblar bunkasar huldar kasashensu. Tun bayan watan Mayun da ya gabata, bisa daidaiton da shugabannin biyu suka cimma, tawagogin kasashen biyu sun gudanar da shawarwarin tattalin arziki da cinikayya har sau biyar. A sabon zagayen shawarwarin da aka gudanar a baya bayan nan a birnin Kuala Lumpur, sassan biyu sun yi musayar ra’ayoyi kan batutuwan tattalin arziki da ciniki da ke janyo hankulansu duka, tare da cimma matsaya daya a kan matakan da za a dauka. Lallai ta hanyar yin shawarwari da juna cikin daidaito, sassan biyu sun kai ga karfafa fahimtar juna da amincewa da juna, hakan kuma ya shaida cewa, yin shawarwari da juna ya fi yin gaba da juna, kuma Sin da Amurka suna iya raya kansu tare da tabbatar da ci gabansu na bai daya.
Kasancewarsu kasashe biyu mafiya karfin tattalin arziki a duniya, alhakin da ke rataya a wuyan Sin da Amurka ne su gano hanyar da ta dace ta cudanya da juna. Kasashen biyu za su iya karfafa ginshikin huldarsu da samar da kyakkyawan yanayi na bunkasa kansu, tare da samar da karin tabbas da kwarin gwiwa ga duniya, muddin sun tabbatar da daidaiton da shugabanninsu suka cimma, kuma suka yi hangen nesa tare da nacewa ga yin shawarwari da juna wajen daidaita sabaninsu, da kuma inganta hadin gwiwarsu da mu’amala da juna a kai a kai.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAকীওয়ার্ড: tattalin arziki da
এছাড়াও পড়ুন:
Qalibaf: Amurka Tana Yaudarar Duniya Da Zaman Lafiya, Alhalin Tana Ci Gaba Da Kai Harin Wuce Gona Da Iri
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya bayyana cewa: Amurka ta ɗaga tutar zaman lafiya yayin da muggan makamanta suke ci gaba da kai hare-hare kan al’ummun duniya
Kakakin Majalisar Dokokin Iran Muhammad Baqir Qalibaf ya tabbatar da cewa: Taken zaman lafiya da Amurka ke gabatarwa a yanzu karya ne, yana mai cewa: Yayin da Amurka ke ba da shawarar zaman lafiya da tattaunawa a lokacin yakin da ya gabata, jiragen yakinta B-2 suna shirin kai hare-hare kan cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran a lokaci guda.
A lokacin da ya ziyarci lardin Khorasan ta Arewa da ke arewa maso gabashin Iran, Qalibaf ya yi jawabi a wani taro na tunawa da shahidan lardin a ranar Laraba da yamma, yana mai cewa: “Idan suka tsaya a yau kan masu girman kai na duniya da kuma Amurka mai laifi, mai cin amana, mai yaudara, da kuma ha’inci, to godiya ce ga al’adar shahada.”
Ya ci gaba da cewa: “Dole ne a tuna cewa: Kowa ya shaida a lokacin yakin da ya gabata cewa, yayin da Amurka ke ba da shawarar zaman lafiya da tattaunawa, jiragen yakin B-2 nata suna shirin kai hare-hare kan cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran a lokaci guda.”
Qalibaf ya ci gaba da cewa, “A lokacin yakin kwanaki 12, tun daga kwanaki na biyar da shida zuwa gaba, kowa, daga Amurka zuwa ga ‘yan sahayoniyya, yana rokon a rage girman hare-haren da Iran ke kaiwa kan haramtaciyar kasar Isra’ila. Wannan yana daya daga cikin tasirin al’adar shahada; al’adar da ke wargaza karshen rayuwa kuma tana samar da iko, arziki, da ilimi.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Ci Gaba Da Killace Gaza Bayan Tsagaita Bude Wuta Ya Janyo Mutuwar Mutane 1000 A Yankin October 30, 2025 Kungiyar Rapid Support Forces Ta Sanar Da Kafa Kwamitin Bincike Kan Cin Zarafin Al’umma A El Fasher October 30, 2025 An Kafa Dokar Ta Baci A Darul-Salam Saboda Tarzoman Zaben Shugaban Kasa A Tanzania October 30, 2025 Rasha Da Amurka Sun Sake Dawo Da Gwaje-gwajen Makaman Nukiliya October 30, 2025 Kasar Czech Ta Hana Wa Wani Sojan HKI Shiga Kasar Bisa Gargadin Faransa October 30, 2025 Sojojin HKI Sun Kutsa Kudancin Lebanon October 30, 2025 Adadin Falasdinawan Da Su Ka Yi Shahada A Cikin Sa’o’i 24 Sun Haura 100 October 30, 2025 Amurka Ta Hana Marubuci Dan Nigeria Wole Soyinka Izinin Shiga Amurka October 30, 2025 Pakistan Tayi Barazanar Daukar Mataki Bayan Rushewar Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta Da Afghanistan. October 29, 2025 IRS: Sanya Sabbin Takunkumi Kan Kasar Iran Zai Haifar Da Mummunan Sakamakon A Yankin October 29, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci