Aminiya:
2025-10-31@20:25:58 GMT

An raba wa iyalan jami’an ’yan sandan da suka rasu a bakin aiki a Borno N63.4m

Published: 31st, October 2025 GMT

Rundunar ’yan sandan Jihar Borno ta raba zunzurutun kuɗi naira miliyan 63.4 ga iyalan jami’anta 84 da suka rasa rayukansu a bakin aiki.

Rundunar ta raba kudin ne a ƙarƙashin tsarin inshorar rayuwa da kuma tsarin kula da lafiyar iyali na Sufeto Janar na ’yan sanda.

 

An gudanar da rabon kuɗin ne a ranar Alhamis a Maiduguri babban birnin jihar kamar yadda Kakakin rundunar a jihar, ASP Nahum Kenneth Daso, ya bayyana a cikin wata sanarwa.

A cewar sanarwar, Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, CP Naziru Abdulmajid, wanda ya wakilci Sufeto Janar na ‘yan sanda, IGP Kayode Egbetokun, shi ne ya gabatar da takardun cakin kudin ga iyalan waɗanda suka ci gajiyar tallafin.

“Harkokin da suka shafi jami’anmu da iyalansu ya kasance babban fifiko ga rundunar,” in ji CP Abdulmajid yayin taron.

Ya ce wannan shiri na nuna tausayi da rikon amana, da kuma jagoranci mai nagarta daga Sufeto Janar wajen girmama jaruman da suka sadaukar da rayukansu domin tabbatar da zaman lafiya da tsaron ƙasa.

Kwamishinan ya kuma yi kira ga iyalan da suka amfana da tallafin da su yi amfani da kuɗaɗen yadda ya dace, musamman wajen tallafa wa ilimi, kiwon lafiya, da jin daɗin rayuwar iyalansu gaba ɗaya.

Ya yaba wa Sufeto Janar bisa ci gaba da tsare-tsaren jin daɗin jami’an rundunar, yana mai bayyana su a matsayin muhimman hanyoyin da ke samar da agaji da kwanciyar hankali ga iyalan waɗanda suka rasa masoyansu.

A nata jawabin a madadin iyalan da suka amfana, Misis Nana Goni ta nuna godiya ga Sufeto Janar bisa goyon bayan da ya bayar, tana mai tabbatar da cewa za su yi amfani da kuɗaɗen yadda ya kamata don inganta rayuwar iyalansu.

Rundunar ta bayyana cewa wannan rabon tallafi ya sake tabbatar da jajircewarta wajen kula da walwala da mutuncin jami’anta da iyalansu, musamman waɗanda suka sadaukar da rayukansu wajen kare al’umma.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Sanda Sufeto Janar

এছাড়াও পড়ুন:

Shugabannin Kudancin Kaduna za su karrama Janar  Christopher Musa 

Majalisar Shugabannin Kudancin Kaduna (SKLC) ta kammala shirye-shirye domin gudanar da gagarumar tarbar ga tsohon Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa (mai ritaya).

Za a yi bikin ne domin tunawa da kyakkyawar rawar da majalisar ta ce ya taka a aikin soja da kuma hidimarsa ga kasa.

An sake kama shi a cikin ’yan fashi kwana 5 da fitowa daga kurkuku Ana zargin ɗa da kashe mahaifinsa a Kano saboda hana shi ƙara aure

An shirya gudanar da bikin ne a ranar Asabar, 22 ga watan Nuwamba, 2025, a Babban Filin Wasan na garin Kafanchan, cibiyar kasuwancin Kudancin Kaduna.

A yayin taron majalisar karo na 19 da aka gudanar a Kafanchan, Shugaban SKLC, Ishaya Dare Akau, ya ce za a ba Janar Musa lambar yabo mafi girma ta majalisar wato GCSK.

Akau, ya ce wannan karramawar tana nuni da yadda Janar Musa ya wakilci Kudancin Kaduna, Jihar Kaduna, da Najeriya baki daya cikin kwarewa da cancanta, inda ya bayyana shi a matsayin jakada nagari.

A yayin taron, majalisar ta kuma kaddamar da kwamitin kula da harkokin kudi na Bikin Gargajiya na Shekara-shekara na Kudancin Kaduna (SKFEST), inda aka nada Shugaban Hukumar Haraji ta Jihar Kaduna (KADIRS), Comrade Jerry Adams, a matsayin shugaban kwamitin.

Manyan jami’an gwamnati da dama sun halarci taron karkashin jagorancin Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Rt. Hon. Henry Danjuma Magaji, tare da Mai ba Gwamna shawara kan harkokin siyasa, Hon. Ado Dogo Audu.

Sun yi wa majalisar bayani kan muhimman shirye-shiryen gwamnati, ciki har da amincewar da gwamnatin tarayya ta bayar na farfado da aikin gina hanyar Jere–Kagarko–Jaba–Kwoi–Kafanchan, wadda Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya taimaka wajen ganin tabbatuwarsa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Rundunar Sojin Nijeriya Ta Shirya Wa Janar Musa Faretin Gama Aiki
  • Kifewar Kwalekwale: Gwamnan Gombe Ya Jajanta Wa Al’ummar Nafada Kan Mutuwar Matasa Biyar
  • Shugabannin Kudancin Kaduna za su karrama Janar  Christopher Musa 
  • An Gudanar Da Taron Kasa Da Kasa Na Tattaunawa Kan Kirkire-kirkire Da Bude Kofa Da Raba Damar Samun Ci Gaba A Colombo
  • Borno ta fara fitar da kayan robobi zuwa ƙasashen waje – Zulum
  • Gwamnatin Gombe ta saurari ra’ayoyin jama’a kan kasafin kuɗin 2026
  • Gwamnati ta bai wa ASUU N2.3bn domin biyan bashin albashin malamai
  • Uwa da ’yarta sun nitse a hatsarin jirgin ruwa a Borno
  • Zamfara Ta Fara Sauyawa Zuwa Jihar Fasahar Zamani, In ji Gwamna Lawal