Zaɓen Tanzania: Shugaba Samia Suluhu Hassan ta yi tazarce
Published: 1st, November 2025 GMT
Shugaba Samia Suluhu Hassan ta kasar Tanzania ta sake lashe zaɓen shugaban ƙasar mai cike da ruɗani.
Hukumomin zaɓen ƙasar sun sanar da cewa Shugaba Samia Suluhu ta lashe zaɓen ne da kashi 97 na kuri’un da aka jefa.
Hukamar zaɓen ƙasar ta bayyana cewa mutum 31,913,866 ne suka kaɗa kuri’a a zaɓen, wanda ya gudana a yayin da kasar ke fama da ƙazamar zanga-zanga.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Zaɓe
এছাড়াও পড়ুন:
Ƙasashe 12 da suka samu tikitin Kofin Nahiyyar Afrika na mata
A ci gaba da wasannin neman shiga gasar cin kofin Nahiyyar Afirka na 2026 da ƙasar Morocco zata karɓi baƙunci, yanzu haka ƙasashe 6 sun samu nasarar shiga gasar.
Ƙasashen da suka samu tikitin sun haɗa da mai masaukin baƙi: Morocco da Najeriya da Zambia da Tanzania da Malawi da Algeria da Ghana da Senegal da Kenya da Burkina Faso da Cape Verde da Afrika ta Kudu.
Gwamnan Bauchi na neman ƙirƙirar sabbin ƙananan hukumomi 29 ACF ta mara wa gwamnatin Tinubu bayaWannan dai ita ce gasa karo na 14 da za a buga a tarihi daga ranar 17 ga watan Maris zuwa 3 ga watan Afrilu na 2026.
Ƙasashen da suka kai wasan kusa da na ƙarshe a Kofin Nahiyyar Afirkan za su wakilci nahiyar a Kofin duniya na mata da za a buga a ƙasar Brazil a 2027.