Gwamnatin Jihar Kwara Ta Kafa Kwamitoci 2 Don Tantance Wadanda Suka Yi Ritaya
Published: 1st, November 2025 GMT
Daga Ali Muhammad Rabi’u
Gwamnatin Jihar Kwara ta kafa kwamitoci biyu domin tantance bayanan wadanda suka yi ritaya a matakin jiha da kananan hukumomi.
A cikin wata sanarwa da Kwamishinar Kudi ta jihar, Dakta Hauwa Nuru ta fitar, ta bayyana cewa kwamitocin za su tantance tare da tabbatar da sahihancin bayanan wadanda suka yi ritaya, domin a biya su bisa lokacin da suka bar aikin gwamnati.
A cewarta, kwamitin mutum takwas da aka kafa don kula da kudaden ritaya na matakin jiha zai kasance karkashin jagorancin Mai Duba Asusun Jiha, wato (Auditor General), yayin da wanda ke kula da matakin kananan hukumomi zai kasance karkashin Mai Duba Asusun Kananan Hukumomi.
Sanarwar ta bayyana cewa babban burin kwamitocin shi ne tabbatar da cewa an tattara bayanan masu ritaya bisa gaskiya da adalci, tare da biyan su kai tsaye ta asusun ajiyar banki.
Ta kara da cewa, mambobin kwamitocin sun hada da wakilan tsofaffin manyan sakatarorin, kungiyar tsofaffin ma’aikata, Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC), da kungiyar kwadago ta TUC, da sauransu.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Ba Matakan Tinubu Ne Suka Karyar Da Farashin Abinci Ba – ADC
Sai dai gwamnatin Tinubu ta mayar da martani, tana cewa jam’iyyar ADC kawai tana adawa ne da nasarorin da gwamnati ke samu.
Hadimin shugaban kasa, Abdulaziz Abdulaziz, ya ce: “Da farko ‘yan adawa suna ƙorafi cewa abinci ya yi tsada. Yanzu da gwamnati ta ɗauki matakai don rage tsada, sai kuma suke kuka.”
A watan Satumba 2025, Shugaba Tinubu ya umarci kwamiti na musamman na gwamnati da ya ɗauki matakan gaggawa don rage tsadar abinci a faɗin ƙasar nan.
Duk da haka, wasu manoma na kukan cewa matakan sun jawo musu asara saboda tsadar kayan noman da suke amfani da su.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA