Aminiya:
2025-10-31@21:34:22 GMT

Kotu ta tsige dan majalisar da ya sauya sheka zuwa APC

Published: 31st, October 2025 GMT

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta tsige dan majalisar wakilai, Abubakar Gummi daga kujerarsa saboda sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Gummi yana wakiltar mazabar Gummi/Bukkuyum ta Jihar Zamfara a majalisar wakilai.

An raba wa iyalan jami’an ’yan sandan da suka rasu a bakin aiki a Borno N63.

4m An sake kama shi a cikin ’yan fashi kwana 5 da fitowa daga kurkuku

Mai shari’a Obiora Egwuatu ne, ya yanke hukuncin, inda ya umarci kakakin majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, da ya daina amincewa da Gummi a matsayin dan majalisar da ke wakiltar mazabar Gummi/Bukkuyum.

Haka kuma ya umarci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ta shirya sabon zabe cikin kwanaki 30 domin cike gurbin kujerar dan majalisar.

Jam’iyyar PDP tare da shugaban ta na jihar Zamfara, Jamilu Jibomagayaki, ne suka shigar da karar dan majalisar.

Sun ce bai dace Gummi ya ci gaba da zama a kujerar ba bayan barin jam’iyyar da ta tsayar da shi takara.

Gummi, ta bakin lauyansa ya ce ya fice daga PDP ne saboda rikicin cikin gida da jam’iyyar ke fama da shi a matakin kasa da kuma a mazabarsa.

Amma kotu ta yi watsi da wannan hujjar, inda ta bayyana cewa babu takaddama da za ta ba shi damar ya sauya sheka.

A hukuncin da ya yanke, Mai shari’a Egwuatu ya ce ’yan siyasa dole su mutunta zabin jama’ar da suka kada musu kuri’a a karkashin jam’iyyar da ta tsayar da su takara.

Ya ce doka ba ta yadda da dan siyasa ya bar jam’iyyar da ta taimaka masa wajen lashe zabe sannan ya koma wata jam’iyya ba tare da ajiye mukaminsa ba.

Ya kara da cewa kuri’un da aka kada don dan takarar na jam’iyya ne, ba nasa ne na kashin kansa ba.

“Idan mutum yana son sauya sheka, ka da ya dauki amanar jama’ar da ta zabe shi ya tafi da ita,”  in ji alkalin.

Kotu ta kuma umarci Gummi da ya daina karbar albashi da wasu hakkoki a matsayin dan majalisa, tare da mayar da duk kudaden da ya karba daga ranar 30 ga watan Oktoba, 2024, zuwa ranar da aka yanke hukuncin.

Haka kuma, ya gabatar da hujjar mayar da kudaden ga kotu cikin kwanaki 30.

Mai shari’a Egwuatu ya kuma ci Gummi tarar Naira N500,000, domin biyan PDP kudaden da ta kashe wajen shigar da kara.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Dan siyasa sauya sheka Takara dan majalisar sauya sheka

এছাড়াও পড়ুন:

Tinubu Ya Amince Da Ƙara Harajin Shigo Da Man Fetur Da Dizal Zuwa Kashi 15

Masana sun bayyana cewa wannan sabon haraji zai iya sa wa farashin mai ya tashi.

Gwamnati ta ce wannan mataki na daga cikin ƙoƙarinta na ƙara samun kuɗaɗen shiga da rage yawan kashe kuɗi wajen shigo da man fetur daga ƙasashen waje.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Xi Jinping: Sin Da Amurka Za Su Iya Hada Kai Don Sauke Nauyin Dake Wuyansu Na Manyan Kasashe Da Daukar Ainihin Matakai October 30, 2025 Manyan Labarai Bai Kamata Gwamnati Ta Ke Ciyo Bashi Bayan Cire Tallafin Man Fetur Ba – Sanusi II October 30, 2025 Manyan Labarai Atiku Ya Soki Gwamnatin Tinubu Kan Sauya Sunayen Waɗanda Aka Yi Wa Afuwa October 30, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kotu ta dakatar da gudanar da babban taron PDP
  • ’Yan bindiga sun sace fasinjoji a cikin motocin bas a Kogi
  • Kotu ta dakatar da babban taron PDP na ƙasa
  • Kotu ta dakatar da babban taron PDP
  • Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP
  • Tinubu Ya Amince Da Ƙara Harajin Shigo Da Man Fetur Da Dizal Zuwa Kashi 15
  • Sabon Ingantaccen Hadin Gwiwar “Sin-ASEAN 3.0″ Ya Kafa Sabon Misali Na Hadin Kan Yanki
  • Kotu Ta Umarci Ƙwace Dala 49,700 Daga Tsohon Jami’in INEC
  • DAGA LARABA: Dalilan Da Suka Sa PDP Ta Ki Sayarwa Sule Lamido Fom Din Takarar Shugaban Jam’iyya