Zaben 2027 Zai Kasance Ne Tsakanin Mulkin Tinubu Da Zabin Ƴan Nijeriya —Atiku Abubakar
Published: 31st, October 2025 GMT
“Ana kiransa da suna dokar binciken tntanet ta tsoratarwa, wadda kasashen da suka ci gaba da dama suka dade da yin watsi da ita. A karni na 21, ba za a iya tunanin cewa gwamnatin Nijeriya za ta tauye ‘yancin fadin albarkacin baki, wanda shi ne ginshikin mulkin dimokuradiyya.”
Atiku ya ce duk wata doka da ke take ‘yancin ‘yan kasa na yin tsokaci mai muhimmanci game da shugabanninsu ko a hanyoyin sadarwar zamani ko ta hanyar magana ba dimokuradiyya ba ce kuma kai tsaye take hakkokin Dan’adam ne.
“A cikin shekaru biyu da rabi da suka gabata tun bayan da gwamnatin Tinubu ta fara daukan matakan da ke janyo kuncin tattalin arziki da yunwa da bakin ciki ga mutanen Nijeriya, mun shaida zanga-zanga da koke-koke daga ‘yan kasa da ba za su iya daukar mulkin rashin gaskiya ba. Duk da haka, maimakon sauraron ‘yan kasa sai gwamnatin ta zabi hanyar amfani da karfin hukumo da tsoratarwa wadda ta juya lamarin zuwa wani abu daban.
“Lallai abin bakin ciki ne na ganin ana take hakkin ‘yan kasa da kundin tsarin mulki ya tabbatar a lokacin da ya kamata dimokuradiyyarmu ta kasance mai bin tsari. Dole ne mu tunatar da gwamnatin Tinubu cewa babu gwamnati a lokacin da ta kasa kare ‘yancin ‘yan kasarta, komai karfinta kuwa. Yin haka abun ta da hankali ne kuma hakan yana nuna gazawar gwamnati a fili.”
Atiku ya ce tabbas gwamnati na da alhakin kula da doka da oda, babu ingantacciyar gwamnati da za ta harbi masu zanga-zangar lumana da harsashi mai rai ko ta boye a bayan dokoki tana musguna wa ‘yan kasa.
Ya ce rashin kulawar gwamnati Tinubu ga dokar kasa da kuma ci gaba da kin bin umarnin kotu sun zama shahararrun siffofinta mafiya suna a kasar nan a halin yanzu.
Tsohon mataimakin shugaban kasa ya kara da cewa tun farkon wannan gwamnati, kungiyar kare hakkin Dan’ada ta Amnesty ta soke wannan gwamnatin da take hakkin Dan’adam.
Ya ce haka ma wasu kungiyoyi masu muhimmanci kamar irinsu kungiyar ‘yan jaridu ta Nijeriya da kungiyar kare ajandar kafafen yada labarai sun yi korafi kan cin zarafin ‘yan jarida da ‘yan kasa ta hannun jami’an gwamnati.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
Ba daidai ba ne Tinubu ya ci gaba da ciyo bashi duk da cire tallafin mai – Sanusi
Sarkin Kano kuma tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Muhammadu Sanusi II, ya bai dace gwamnatin Shugaban Kasa Bola tinubu ta ci gaba da ciyo bashi ba bayan ta cire tallafin man fetur.
Yayin da yake jawabi a Abuja ranar Talata, a taron Oxford Global Think Tank Leadership da ƙaddamar da wani littafi, Sanusi ya ce cire tallafin man ya haifar da ƙaruwar kuɗaɗen shiga na gwamnati.
Netanyahu ya ba da umarnin kai mummunan farmaki a Gaza Amurka ta soke bizar Wole SoyinkaSanusi ya kuma yaba wa gwamnatin Tinubu kan cire tallafin man fetur da daidaita farashin musayar kuɗi, yana mai bayyana matakan a matsayin “masu raɗaɗi amma na wajibi.”
Sai dai ya yi gargaɗin cewa waɗannan gyare-gyare ba za su yi tasiri ba sai an haɗa su da tsari mai kyau na kashe kuɗi da gaskiya a cikin gudanar da gwamnati.
“In ka daina biyan tallafi amma ka ci gaba da yin rance, hakan na nufin ka rufe rami guda ne sai ka buɗe wani. Kalubalen da ke gabanmu yanzu shi ne ingancin yadda gwamnati ke kashe kuɗi da kuma yadda ake tafiyar da kuɗaɗen da aka ce an ajiye,” in ji shi.
Sanusi, wanda ya jagoranci CBN daga 2009 zuwa 2014, ya ce matsalolin tattalin arzikin Najeriya a yanzu sun faru ne a sakamakon rashin daidaito a manufofi da siyasar neman sai an faranta wa jama’a da aka dade ana yi.
“A shekarar 2012, mun yi gargaɗin cewa tallafin mai ba zai dore ba, amma siyasa ta shigo. Yanzu, waɗanda suka jagoranci zanga-zangar adawa da cire tallafin su ne suka gaji matsalar, kuma ba su da wani zaɓi sai su yi abin da ya dace,” in ji shi.
Ya yaba wa ƙwararrun da ke cikin tawagar tattalin arzikin gwamnati kan matakan da suka ɗauka don daidaita hauhawar farashi da rage canjin farashin kuɗi, amma ya jaddada cewa dole ne a dakile ɓarna da almubazzaranci cikin gaggawa.
Yayin da yake tambaya kan yadda gwamnati ke kashe kuɗi, Sanusi ya ce: “Me ya sa muke da ministoci 48? Me ya sa ake da jerin motocin gwamnati masu yawa? Me ya sa har yanzu ana yin rance bayan cire tallafi? In ka rufe rami guda, me ya sa za ka buɗe wani?
“Wannan gwamnati na bukatar ta duba hukumomi da yadda ake amfani da kuɗi a dukkan matakai. Domin in ka ci gaba da samun kuɗi amma kana kashewa ba daidai ba, za ka lalata duk wani ci gaba da aka samu.
“Amma irin mu da za mu ce, ‘Ya Shugaban Ƙasa, wannan ba daidai ba ne,’ ana ɗaukarmu a matsayin abokan gaba. Don haka, idan shugabanni sun kewaye kansu da masu yabon kai, ba za su taɓa samun shawara mai kyau ba.
“Shi ya sa irin su Aigboje Aig-Imoukhuede da ni kan zama kamar abokan gaba ga gwamnati, domin mutane ba sa son jin gaskiya.”
Sanusi ya ƙara da cewa: “Mun faɗa wa Buhari komai, game da buga kuɗi, almubazzaranci, farashin musayar kuɗi da tallafi, amma duk lokacin da muka yi hakan, ana ɗauka a matsayin hari kai tsaye. Waɗanda ke kewaye da shi sun sa ya ɗauke mu a matsayin abokan gaba. Shugabanni dole su fara tambaya: wa nake kewaye da kaina da su?,” in ji Sanusi.