Kotu ta dakatar da babban taron PDP na ƙasa
Published: 31st, October 2025 GMT
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta dakatar da jam’iyyar PDP daga gudanar babban taronta na ƙasa da aka shirya yi a Ibadan, Babban Birnin Jihar Oyo, a watan gobe.
Mai shari’a James Omotosho ne, ya bayar da wannan umarni, yayin da yake yanke hukunci kan wata ƙara da aka shigar domin sanin ko jam’iyyar PDP na da ikon ci gaba da shirya taron da aka tsara gudanarwa a ranakun 15 da 16 ga Nuwamba.                
      
				
Waɗanda suka shigar da ƙarar sun haɗa da Austine Nwachukwu, shugaban PDP na Jihar Imo; Amah Abraham Nnanna, shugaban PDP na Jihar Abiya da Turnah George, sakataren PDP na yankin Kudu maso Kudu.
Waɗanda ake ƙarar sun haɗa da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), PDP, Sakataren Jam’iyyar na Ƙasa, Samuel Anyanwu, Sakataren shirya taruka na jam’iyyar, Umar Bature, Kwamitin Ayyuka na jam’iyyar na Ƙasa (NWC) da Kwamitin Zartarwa na jam’iyyar na Ƙasa (NEC).
Masu shigar da ƙarar sun kasance ’yan tsahin Nyesom Wike ne.
Sun roƙi kotu da ta hana gudanar da taron, inda suka bayyana cewar jam’iyyar ta saɓa wa dokokinta, Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999, da kuma Dokar Zaɓe wajen shirya taron.
Lauyansu ya shaida wa kotu cewa: “Ba a gudanar da taron wakilai a jihohi 14 ba don haka shirin taron ya saɓa wa doka.”
Sai dai PDP ta kare kanta, inda ta ce lamarin na harkokin cikin gidan jam’iyyar ne, don haka bai kamata kotu ta tsoma baki ba.
Jam’iyyar ta zargi masu ƙarar da ƙoƙarin tayar da rikici domin hana ta gudanar da sabon zaɓen shugabanni.
Aminiya ta ruwaito cewa wannan rikici ya ƙara dagula al’amura a jam’iyyar PDP.
Sakataren jam’iyyar na ƙasa, Sanata Samuel Anyanwu, a baya ya yi zargin cewa an yi amfani da hannunsa na bogi a takardun da aka aike wa INEC game da shirya taron.
Amma shugabancin jam’iyyar ya ƙaryata wannan zargi.
A halin yanzu, Kwamitin Shirya Taron na Ƙasa (NCOC) ya ɗage tantance ’yan takara da aka tsara gudanarwa a ranar 28 ga watan Oktoba.
Mutane da dama na ganin ɗage tantance ’yan takarae na da nasaba da jiran sakamakon hukuncin kotu kafin a ci gaba da shirye-shirye.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Babban taro shirya taron jam iyyar na a jam iyyar
এছাড়াও পড়ুন:
Afuwar Tinubu Ga Fursunoni: Saura Ƙasa Da Shekaru 6 Maryam Sanda Ta Shaƙi Iskar ‘Yanci
Don haka, an mayar da hukuncin kisa na Maryam Sanda zuwa shekaru 12 a gidan yari, wanda hakan ya nuna tana da kasa da shekaru shida na zama a gidan gyaran halin.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA HKI Ta Ci Gaba Da Kai Hare-Hare Kan Kudancin Kasar Lebanon
HKI Ta Ci Gaba Da Kai Hare-Hare Kan Kudancin Kasar Lebanon