Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Koriya Ta Kudu Lee Jae-myung
Published: 1st, November 2025 GMT
A wannan rana, a gun taron manema labarai da aka gudanar bayan kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar APEC, Lee Jae-myung ya ce hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin Sin da Koriya ta Kudu yana da matukar muhimmanci, ya kuma yi imanin cewa birnin Shenzhen na kasar Sin zai karbi bakuncin kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar APEC cikin nasara a shekara mai zuwa.
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Uba Sani Ya Bayyana Tsare-tsaren Ci Gaban Kaduna a Taron Duniya a Dubai.
Daga Abdullahi Shettima
Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya wakilci Nijeriya a taron ƙoli na biranen Asiya da ya gudana a ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), inda ya gabatar da kudirorin sauyin ci gaban Kaduna.
Taron ya samu halartar manyan baki daga ƙasashe sama da 150, ciki har da gwamnoni, shugabannin birane da jagororin kasuwanci daga Asiya, Fasifik, Turai da Afirka. Taken taron shi ne “Haɗin Gwiwa. Ƙarfafawa. Sauyi.”
A jawabinsa mai taken “Gina Haɗin Gwiwa Domin Ci Gaban Kowa,” Gwamna Uba Sani ya bayyana yadda Kaduna ke samun nasara a fannoni da dama kamar gyaran birane, bunƙasa noma da tallafawa jama’a. Ya ce tsarin ci gaban jihar yana dogara ne kan faɗaɗa damar tattalin arziki, kare marasa ƙarfi, da ƙarfafa jama’a su cim ma nasara a rayuwarsu.
Haka kuma, ya halarci baje kolin birnin Dubai mai taken “Sauya Arewa a Nijeriya: Jagoranci, Ƙirƙira da Tasirin Zamantakewa,” inda ya jaddada muhimmancin jagoranci mai nagarta da amfani da fasaha wajen buɗe damarmaki ga al’umma.
A yayin taron, Gwamnan ya gudanar da ganawa ta musamman da Marwan Bin Galita, Darakta-Janar na birnin Dubai, inda suka tattauna batutuwan kirkirar makamashin sharar gida, kula da sharar zamani, da tsare-tsaren gine-ginen birane na zamani.
Duk ɓangarorin biyu sun amince da zurfafa haɗin kai a fannin fasaha da musayar ƙwarewa domin tallafawa sauyin tattalin arzikin Kaduna zuwa mai ɗorewa.
Gwamna Sani ya bayyana cewa halartar Kaduna a taron (APCS 2025) na nuna shirin jihar na shiga sahun gaba wajen yin haɗin kai, ƙirƙira da zama abin koyi a fannin ci gaba mai ɗorewa — a Najeriya da duniya baki ɗaya.
Karshe.