Aminiya:
2025-11-01@18:49:33 GMT

PDP ta dakatar da Anyanwu da wasu ’yan tsagin Wike

Published: 1st, November 2025 GMT

Rikici a babbar jam’iyyar adawa ta PDP, na ƙara ƙamari, bayan da jam’iyyar ta dakatar da sakatarenta na ƙasa, Sanata Samuel Anyanwu, da wasu da ake ganin ’yan tsagin Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike ne.

Mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, Debo Ologunagba ne, ya sanar da dakatarwar bayan wani taro da Kwamitin Ayyuka na Ƙasa (NWC), ya gudanar a hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja.

Zargin Kisan Kiristoci: Maganar Trump a kan Najeriya tsagwaron ƙarya ce — Shehu Sani Zaɓen Tanzania: Shugaba Samia ta yi tazarce da kashi 97 an ƙuri’u

Sauran da aka dakatar sun haɗa da Mai Bai wa jam’iyyar Shawara kan Harkokin Shari’a, Kamaldeen Ajibade (SAN); Sakataren Tsara Harkokin Jam’iyya, Umar Bature; da Mataimakin Mai Bai wa jam’iyyar Shawara kan Harkokin Shari’a.

Rahotanni sun bayyana cewa waɗanda aka dakatar ba sa halartar tarukan jam’iyyar.

An dakatar da su na tsawon wata ɗaya, sannan aka miƙa lamarinsu ga Kwamitin Ladabtarwa na jam’iyyar PDP domin gudanar da bincike.

Waɗanda aka dakatar ’yan tsagin Wike ne, kuma sun raba ƙafa a rikicin da jam’iyyar ke fuskanta tun bayan zaɓen 2023.

Idan ba a manta ba, a ranar Juma’a ne, wata Babbar Kotu a Babban Birnin Tarayya, ta dakatar da PDP daga shirin gudanar da babban taronta da aka tsara yi a Ibadan, Jihar Oyo, a ranar 15 da 16 ga watan Nuwamba, 2025.

Sai dai jam’iyyar ta ce za ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin, kuma hakan ba zai hana ta ci gaba da shirye-shiryen gudanar da taron ba.

Wasu daga cikin ’ya’yan jam’iyyar sun ce rashin jituwa a PDO shi ne babban dalilin da ya sa aka kai ƙarar taron’ kotu.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Anyanwu Babban taro dakatarwa Sakatare

এছাড়াও পড়ুন:

HKI Na Ci Gaba Keta Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta A Gaza Inda Take Kashe Falasdinawa

Rahotanni sun bayyana cewa Isra’ila ta kashe wasu falasdinawa guda 5  yankin gaza a ci gaba da keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta da suka cimma tsakaninta da kungiyar Hamas a farkon watan oktoba,

A yau juma’a kafar yada labarai ta falasdinu ta bayyana cewa sojojin Isra’ila sun harbe wani bafalasdine a yankin jabaliya dake arewacin yankin Gaza, haka zalika wani bafalasdine mai suna Mahmud suleman al- wadiya sojojin isaraila sun kashe shi a gabashin shuja’iyya dake makwabtaka da gabashin gaza, gari mafi girma a gaza kuma an jikkata wani dan uwansa,

Har ila yau  hamdi al-barim da mohamma salem qadi sun ji mummunan rauni sakamakon harin da sojojin Isra’ila suka kai musu a khan yunus dake yammacin gaza a yan kwanakin nan,

Tun daga lokacin da Isra’ila ta kaddamar da hare-hare a yankin Gaza zuwa yanzu a shekara ta 2023 sojojin Isra’ila na ci gaba da kai hare – hare a yankuna daban – daban inda akalla sun kashe mutane 1062 tare da jikkata wasu dubbai fiye da 20,000 kuma da suka hada da yara kana 1600 an cafkesu ana tsare da su .

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka An Tube Yarima Mai Jiran Gado Na Birtaniya Bayan Da Aka Tabbatar Da Laifinsa October 31, 2025 Kasashen Pakistan Da Afghanistan Sun Tsawaita Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta October 31, 2025 M D Duniya Tayi Gargadi Game Da Gwajin Nukiliya Da Amurka Ta Sanar Za ta yi October 31, 2025 Sudan Ta Yi Kira Ga Kwamitin Tsaro Da Ya Ayyana RSF A Matsayin Kungiyar ‘Yan Ta’adda October 31, 2025 Araqchi: Gwajin Makaman Nukiliya Na Amurka Babbar Barazana Ce Ga Duniya October 31, 2025 Masar da Eritrea Sun Tattauna Bukatar Tallafawa Kasar Sudan October 31, 2025 Shugaban Lebanon Ya Umarci Sojoji Da Su Fuskanci Kutsen Na Isra’ila A Kudancin Kasar October 31, 2025 Madagascar Ta Sanar da Kafa Sabuwar Gwamnati Tare da Manyan ‘Yan Adawa October 31, 2025 Iran ta yi fatali da kalamman IAEA Kan Shirin Nukiliyarta October 30, 2025 Trump Ya Umarci Ma’aikatar Yakin Amurka Ta koma gwajin makaman nukiliya October 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya
  • PDP ta dakatar da Anyanwu da wasu da ke da alaƙa da Wike
  • Za mu ci gaba da shirye-shiryen babban taronmu — PDP
  • Kotu ta dakatar da gudanar da babban taron PDP
  • HKI Na Ci Gaba Keta Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta A Gaza Inda Take Kashe Falasdinawa
  • Kasashen Pakistan Da Afghanistan Sun Tsawaita Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta
  • Kotu ta dakatar da babban taron PDP na ƙasa
  • Kotu ta dakatar da babban taron PDP
  • Majalisar Dattawa Ta Tabbatar Da Bernard Doro A Matsayin Ministan Harkokin Jin Ƙai