Rundunar Sojin Nijeriya Ta Shirya Wa Janar Musa Faretin Gama Aiki
Published: 31st, October 2025 GMT
Rundunar Sojojin Nijeriya (AFN) za ta gudanar da bikin kammala aiki na tsohon Shugaban Tsaron Ƙasa (CDS), Janar Christopher Gwabin Musa (mai ritaya) a ranar Jumma’a, 31 ga Oktoba, 2025, domin girmama ayyukan da ya gudanar a lokacin hidimarsa.
A cewar sanarwar da shalƙwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta fitar a ranar Alhamis, an shirya bikin Pulling Out Parade ɗin ne da ƙarfe 09:00 na safe, inda manyan hafsoshin Soja, da jami’an gwamnati da ƴan uwa za su halarta.                
      
				
Janar Musa ya yi aikin Soja na tsawon shekaru masu yawa, kuma ya yi shugabanci a matsayin Shugaban Tsaron Ƙasa daga Yuni 2023 zuwa Oktoba 2025. A wannan lokaci, ya jagoranci manyan hare-haren yaƙi da ta’addanci tare da ƙarfafa hulɗar haɗin gwuiwa tsakanin sassan Sojojin Nijeriya.
A ranar 24 ga Oktoba, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanar da sabon tsarin jagorancin rundunar Soja, inda ya naɗa Manjo Janar Olufemi Oluyede a matsayin sabon Shugaban Tsaro, wanda hakan ya kawo ƙarshen wa’adin Janar Musa.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
Yan Nijeriya Na Ɗanɗana Kuɗarsu Kan Jinkirta Cire Tallafin Mai – Sarki Sanusi
“A lokacin, mun yi lissafin adadi a Babban Bankin. Na tashi na kafa sharuda bisa ga ka’idodi, inda na ce a cire tallafin yau. Farashin kaya zai tashi daga kashi 11 zuwa kashi 13, zan rage shi a cikin shekara guda. Ba za mu samu hauhawar farashin kaya na kusan kashi 30 ba,” in ji shi.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Akwai Bukatar Hada Kai Da Aiki Tare Tsakanin Hukumomin Tsaro
Akwai Bukatar Hada Kai Da Aiki Tare Tsakanin Hukumomin Tsaro