“Haka kuma an kama wata mata mai shekaru 34 da ake zargi da hannu a lamarin, tare da wasu masu gidan marayu guda biyu da ke Abuja da Jihar Nasarawa, inda aka gano wasu yaran da ake kyautata zaton an yi safarar su. Wasu daga cikin gidajen marayun da aka gano ana amfani da su ne a matsayin cibiyoyin ajiye yara, inda ake jiran ‘kwace’ ko sayar da su da sunan daukar nauyin marayu.

Ya ce, “An gano gidajen marayu guda hudu da ke Kaigini, Kubwa Edpressway Abuja; Masaka Area 1, Mararaba kusa da Abaca Road; da kuma Mararaba bayan Kasuwar Duniya suna da alaka da wannan kungiya, kuma ana ci gaba da bincike a kansu.”

Ya kara da cewa, daya daga cikin masu korafin ya bayyana cewa ya biya Naira miliyan 2.8 a matsayin kudin daukar yaro, sannan ya biya Naira 100,000 a matsayin kudin shawara ga daya daga cikin ‘yan kungiyar.

Sanarwar ta kara da cewa, “Wani mai korafi ya ce shi ma ya biya Naira miliyan 2.8 kudin daukar yaro da Naira 100,000 kudin shawara ga wani dan kungiyar.

“An canza sunayen yawancin yaran da aka ceto, lamarin da ya kara wahalar da bincike da gano asalinsu,” in ji sanarwar.

Darakta Janar ta NAPTIP, Binta Adamu Bello, ta bayyana damuwarta kan wannan lamari, inda ta ce safarar yara ta zama babbar matsala a kasa.

Ta hanyar Adekoye, DG din ta nuna damuwa game da yadda wasu gidajen marayu ke amfani da raunin jama’a wajen aiwatar da safarar yara.

Ta ce, “Abin takaici ne yadda wasu masu mugunta da ke da sunayen kwararru da matsayi a cikin al’umma, suke amfani da matsayin su wajen yaudarar mutanen da ke cikin mawuyacin hali, su yi safarar ‘ya’yansu, da dama daga cikinsu ma sun tsira ne daga halaka a lokacin rikice-rikicen al’umma ko na manoma da makiyaya, sannan a sayar da su ga iyaye masu neman haihuwa a matsayin daukar yaro ba tare da sahihin izinin iyayensu ba.

“Wannan abin ba za a yarda da shi ba, kuma wadanda aka kama kan wannan mugun aiki za su fuskanci hukuncin doka yadda ya kamata.

“’Ya’yanmu ba kayayyaki ba ne da za a ajiye su a gidajen marayu a sayar ga mai biyan mafi tsada. Wannan dole ya tsaya,” in ji ta.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Yadda Gwamnatin Tarayya Ta Dakile Yaɗuwar Ɓarkewar Cutar Dabbobi A Jihar Jigawa November 1, 2025 Manyan Labarai Jerin Gwarazan Taurarinmu November 1, 2025 Manyan Labarai Trump Ya Ayyana Nijeriya A Matsayin Ƙasar Da Rayuwar Kiristoci Ke Cikin Hatsari October 31, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: gidajen marayu

এছাড়াও পড়ুন:

Trump Ya Ayyana Nijeriya A Matsayin Ƙasar Da Rayuwar Kiristoci Ke Cikin Hatsari

“Amurka ba za ta tsaya kawai tana kallo ba yayin da irin waɗannan ta’addancin ke faruwa a Nijeriya da sauran ƙasashe.

“Mun shirya, muna da ƙarfi da niyyar kare Kiristoci a faɗin duniya,” in ji Trump.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai An Tsare Wani Mutum A Gidan Yari Kan Zargin Kashe Matarsa Saboda Ƙuli-Ƙuli A Kano October 31, 2025 Manyan Labarai Makarantar Kogi Poly Ta Bankaɗo Masu Ƙirƙirar Takardun Kammala Karatu na Bogi October 31, 2025 Manyan Labarai Kifewar Kwalekwale: Gwamnan Gombe Ya Jajanta Wa Al’ummar Nafada Kan Mutuwar Matasa Biyar October 31, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kofin kofi mafi tsada a duniya ya shiga kasuwa a kan Naira miliyan 1.5m
  • Trump Ya Ayyana Nijeriya A Matsayin Ƙasar Da Rayuwar Kiristoci Ke Cikin Hatsari
  • An Yi Wa Yara Sama Da Miliyan Biyu Allurar Rigakafin Mashaƙo Da Sankarau A Zamfara
  • Sin Ta Fitar Da Jerin Sakamakon Tattaunawar Tattalin Arziki Da Cinikayya Da Tawagar Kasar Da Ta Amurka Suka Cimma 
  • Yadda Ta Gudana A Taron Karɓar Ƴan Majalisa Shida Da Suka Koma APC
  • Majalisar Dattawa Ta Tabbatar Da Bernard Doro A Matsayin Ministan Harkokin Jin Ƙai
  • Xi Jinping: Sin Da Amurka Za Su Iya Hada Kai Don Sauke Nauyin Dake Wuyansu Na Manyan Kasashe Da Daukar Ainihin Matakai
  • Gwamnati ta bai wa ASUU N2.3bn domin biyan bashin albashin malamai
  • Gwamnatin Gombe ta fara tantance ma’aikata don kawar da na bogi