Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya soki Shugaban Amurka, Donald Trump, bisa kiran Najeriya “ƙasa mai matsala ta musamman” kan zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi.

Sani, ya ce kalaman Trump sun samo asali ne daga bayanan da ba su da tushe, da wasu mutane suka ba shi domin su tayar da fitina a Najeriya.

Sharrin son auren Mai Wushirya aka yi min — Mansura Isa Zaɓen Tanzania: Shugaba Samia ta yi tazarce da kashi 97 an ƙuri’u

A ranar Juma’a ne, Trump ya wallafa rubutu a shafinsa na sada zumunta cewar Kiristanci yana cikin hatasri a Najeriya.

Ya yi iƙirarin cewa ’yan ta’adda sun kashe dubban Kiristoci, amma ya ce Amurka za ta yi duk mai yiwuwa wajen “ceto Kiristoci” a Najeriya da wasu ƙasashe.

Shehu Sani, ya mayar da martani da cewa wannan magana ba gaskiya ba ce, domin matsalar tsaro a Najeriya ba ta da nasaba da addini.

Ya ce Musulmai da Kiristoci dukkaninsu suna fuskantar hare-haren’yan ta’adda da garkuwa da su.

“Wannan zargi ƙarya ne. ’Yan ta’adda da ’yan bindiga a Najeriya suna kashe mutane ba tare da la’akari da addininsu ba. Wannan abin na faruwa tun kusan shekaru 15 da suka wuce,” in ji shi.

Sani, ya ƙara da cewa, saboda yawan Musulmai da Kiristoci a Najeriya, ba zai yiwu addini ɗaya ya zalunci ɗaya ba.

“Idan aka duba yadda Musulmai da Kiristoci suke kusan daidai a Najeriya, ba zai yiwu ɗaya ya zalunci ɗaya ba. Najeriya kamar zaki da damisa ce, dukkanin ɓangarorin suna da ƙarfi,” in ji shi.

Ya zargi waɗanda suka zuga Trump da amfani da rikice-rikicen cikin gida na Najeriya.

“Trump ya samu bayanan ƙarya daga mutanen da ke son raba Najeriya domin su ci moriya daga wannan,” in ji shi.

“Wannan makirci da aka yi wa ƙasar nan ba zai yi nasara ba.”

Sani, ya roƙi ƙasashen duniya su taimaka wa Najeriya wajen yaƙar ta’addanci, maimakon yaɗa labaran ƙarya.

“Najeriya na buƙatar taimako da haɗin kai wajen shawo kan matsalar tsaro, kamar sauran ƙasashen da ke fama da ta’addanci,” a cewarsa.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: yan ta adda zargi

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamna Uba Sani Ya Bayyana Tsare-tsaren Ci Gaban Kaduna a Taron Duniya a Dubai.

Daga Abdullahi Shettima

Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya wakilci Nijeriya a taron ƙoli na biranen Asiya da ya gudana a ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), inda ya gabatar da kudirorin sauyin ci gaban Kaduna.

Taron ya samu halartar manyan baki daga ƙasashe sama da 150, ciki har da gwamnoni, shugabannin birane da jagororin kasuwanci daga Asiya, Fasifik, Turai da Afirka. Taken taron shi ne “Haɗin Gwiwa. Ƙarfafawa. Sauyi.”

A jawabinsa mai taken “Gina Haɗin Gwiwa Domin Ci Gaban Kowa,” Gwamna Uba Sani ya bayyana yadda Kaduna ke samun nasara a fannoni da dama kamar gyaran birane, bunƙasa noma da tallafawa jama’a. Ya ce tsarin ci gaban jihar yana dogara ne kan faɗaɗa damar tattalin arziki, kare marasa ƙarfi, da ƙarfafa jama’a su cim ma nasara a rayuwarsu.

Haka kuma, ya halarci baje kolin birnin Dubai mai taken “Sauya Arewa a Nijeriya: Jagoranci, Ƙirƙira da Tasirin Zamantakewa,” inda ya jaddada muhimmancin jagoranci mai nagarta da amfani da fasaha wajen buɗe damarmaki ga al’umma.

A yayin taron, Gwamnan ya gudanar da ganawa ta musamman da Marwan Bin Galita, Darakta-Janar na birnin Dubai, inda suka tattauna batutuwan kirkirar makamashin sharar gida, kula da sharar zamani, da tsare-tsaren gine-ginen birane na zamani.

Duk ɓangarorin biyu sun amince da zurfafa haɗin kai a fannin fasaha da musayar ƙwarewa domin tallafawa sauyin tattalin arzikin Kaduna zuwa mai ɗorewa.

Gwamna Sani ya bayyana cewa halartar Kaduna a taron (APCS 2025) na nuna shirin jihar na shiga sahun gaba wajen yin haɗin kai, ƙirƙira da zama abin koyi a fannin ci gaba mai ɗorewa — a Najeriya da duniya baki ɗaya.

Karshe.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamna Uba Sani Ya Bayyana Tsare-tsaren Ci Gaban Kaduna a Taron Duniya a Dubai.
  • Najeriya ta musanta ikirarin Trump, na cewa Kristoci na fuskantar babbar barazana a kasar
  • Kofin kofi mafi tsada a duniya ya shiga kasuwa a kan Naira miliyan 1.5m
  • Amurka ta sanya Najeriya cikin ƙasashen da ake yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi
  • Trump Ya Ayyana Nijeriya A Matsayin Ƙasar Da Rayuwar Kiristoci Ke Cikin Hatsari
  • NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Daliban Makarantar Kudi Suka Fi Na Gwamnati Kokari
  • ‘Yansanda Sun Ceto Mutum Ɗaya, Sun Kama Mace Da Zargin Garkuwa Da Mutane A Dajin Kwara 
  • Sojoji Sun Ceto Wani Mutum Da Aka Sace A Taraba
  • Zargin Kisan Kiristoci: ’Yan majalisar Amurka sun yi amfani da bayanai marasa tushe — Gwamnati