Barcelona ta shiga zarwacin Victor Osimhen
Published: 31st, October 2025 GMT
Kungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona da ke Sipaniya na ƙoƙarin ɗauko Victor Osimhen a matsayin wanda zai maye gurbin Robert Lewandowski wanda ke fama da matsalar raunuka
Ɗan jaridar ƙasar Sifaniya, Gabriel Sans na Mundo Deportivo ya bayyana cewar, Barcelona na neman wanda zai maye gurbin Robert Lewandowski a matsayin mai jefa ƙwallo a raga, hakan ne ya sa ƙungiyyar ta amince da ɗaukar Osimhen.
A ƙarshen kakar bana ne ake tunanin up Lewandowski zai bar Barca, wanda zai tilasta wa ƙungiyyar neman wani zaƙaƙurin ɗan wasan gaba mai ciyo ƙwallo.
Victor Osimhen dai a bazarar nan ne ya koma Galatasaray bayan barin Napoli ta Italiya.
Osimhen dai ba ya ɓoye aniyarsa ta buga wasa a ɗaya daga cikin manyan gasannin Nahiyyar Turai biyar ba, ciki har da Firimiya ta Ingila da LaLiga ta Sifaniya, inda Barcelona ke cikin manyan ƙungiyoyin gasar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Barcelona da ke Sipaniya Robert Lewandowski
এছাড়াও পড়ুন:
Za a rataye wanda ya kashe ɗan uwansa a Ekiti
Wata babbar kotun Jihar Ekiti da ke zamanta a Ado Ekiti ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataye wani mai suna Stephen Adamu mai shekara 34 bisa laifin kashe ɗan uwansa.
An gurfanar da wanda ake tuhuma a gaban mai shari’a Adekunle Adeleye a ranar 31 ga watan Junairu, 2025, kan tuhumar kashe wani David Adamu, a sashi na 234 na dokar laifuka ta jihar Ekiti 2021.
Gobara ta tashi a babban kanti a Abuja Ƙasashe 12 da suka samu tikitin Kofin Nahiyyar Afrika na mataDomin tabbatar da ƙarar sa, mai gabatar da ƙara Funmi Bello, ya kira shaidu shida da waɗanda ake ƙara da su gabatar da jawabi, da fom ɗin shaida da kuma wuƙa a matsayin nunin shaida.
Wanda ake tuhumar ya yi magana ta bakin Lauyansa, S.K Idowu, kuma bai kira wani shaida ba.
Da yake yanke hukuncin, mai shari’a Adeleye ya ce daga dukkan yanayin wannan shari’a, Stephen Adamu ya daɓa wa David Adamu wuƙa a wuya.
“Na sami wanda ake tuhuma da laifi kamar yadda ake tuhumarsa, wanda ake ƙara Stephen Adamu an yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya,” in ji shi.