Ofishin kula da zirga-zirgar kumbuna masu dauke da mutane na kasar Sin ya ce, an harba kumbon Shenzhou-21 mai dauke da ‘yan sama jannatin kasar Sin 3 cikin nasara, a daren jiya Juma’a, agogon Beijing.

Daga baya kumbon ya sarrafa kansa wajen hade jikinsa da na tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin, ta yadda ‘yan saman jannatin suka shiga tashar, inda tsoffin ‘yan saman jannati 3 da suka dade a cikin tashar, suka yi musu maraba.

Hakan ya shaida haduwar sabbi da tsoffin ‘yan sama jannatin kasar Sin karo na 7 a tashar binciken sararin samaniya ta kasar.

Bisa shirin da aka yi, wadannan ‘yan sama jannati 6 za su kwashe kimanin kwanaki 5 suna aiki tare a cikin tashar, kafin tsoffin ‘yan saman jannatin 3 su kama hanyar dawowa gida.

Zuwa yanzu, kasar Sin ta riga ta tura ‘yan sama jannati 44 zuwa sararin samaniya. (Bello Wang)

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Koriya Ta Kudu Lee Jae-myung  November 1, 2025 Daga Birnin Sin Xi: A Hada Kai Wajen Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik November 1, 2025 Daga Birnin Sin CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka October 31, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Sin Za Ta Harba Kumbon Shenzhou-21

Hukumar kula da zirga-zirgar kumbuna masu dauke da ‘yan sama jannati ta kasar Sin ko CMSA, ta ce an shirya harba kumbon Shenzhou-21 da karfe 12 saura mintuna 16 na daren gobe Juma’a, daga tashar harba kumbuna ta Jiuquan dake arewa maso yammacin kasar Sin.

Yayin taron manema labarai da ya gudana a yau Alhamis, CMSA ta sanar da cewa, ‘yan sama jannati Zhang Lu, da Wu Fei da Zhang Hongzhang, za su kasance cikin kumbon na Shenzhou-21, kuma Zhang Lu ne zai jagoranci tawagar. Dalilan harba kumbon na wannan lokaci su ne kammala sauyin aiki da tawagar ‘yan sama jannatin kumbon Shenzhou-20, da kasancewarsu a tashar sararin samaniya ta Sin na kimanin watanni shida, da gudanar da ayyukan kimiyyar samaniya, da gwaje-gwaje masu nasaba da sai sauransu.

A cewar kakakin CMSA Zhang Jingbo, Sin na rike da kudurinta na sauka kan duniyar wata kafin shekarar 2030, ta kuma tsara jadawalin samar da ci gaba, da gwajin babban aikinta na sauke ‘yan sama jannatinta kan doron wata.

A wani ci gaban, CMSA ta ce ‘yan sama jannati biyu na kasar Pakistan za su samu horo tare da takwarorinsu na Sin, kuma za a zabi daya daga cikinsu don kasancewa tare da kumbon Sin na dakon ‘yan sama jannati na dan wani lokaci a matsayin kwararren jami’i. (Saminu Alhassan)

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Xi Jinping: Sin Da Amurka Za Su Iya Hada Kai Don Sauke Nauyin Dake Wuyansu Na Manyan Kasashe Da Daukar Ainihin Matakai October 30, 2025 Daga Birnin Sin Sakamakon Nazarin CGTN Ya Yabawa Gudunmuwar Sin Ga Dunkulewar Yankin Asiya Da Pasifik October 29, 2025 Daga Birnin Sin Sabon Ingantaccen Hadin Gwiwar “Sin-ASEAN 3.0″ Ya Kafa Sabon Misali Na Hadin Kan Yanki October 29, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kamaru: Jagroan ‘Yan Hamayya Ya Yi Kira Da A Tsayar Da Harkoki A Fadin kasar
  • MDD Tana Sa Ido Akan Kashe-kashen Da Ake Yi A Zaben Kasar Tanzania
  • Shugaban Kasar Najeriya Ya Mayar Da Martani Ga Takwaransa Na Amurka Akan Rikicin Addini
  • Sin Ta Fitar Da Jerin Sakamakon Tattaunawar Tattalin Arziki Da Cinikayya Da Tawagar Kasar Da Ta Amurka Suka Cimma 
  • Kasar Sin Ce Ke Da Sama Da Rabin Muhimman Makaloli Na Duniya
  • Ƙasashe 12 da suka samu tikitin Kofin Nahiyyar Afrika na mata
  • Sin Za Ta Harba Kumbon Shenzhou-21
  • Rasha Da Amurka Sun Sake Dawo Da Gwaje-gwajen Makaman Nukiliya
  • Kasar Czech Ta Hana Wa Wani Sojan HKI Shiga Kasar Bisa Gargadin  Faransa