Aminiya:
2025-07-10@19:23:43 GMT

Isra’ila ta kashe Falasdinawa 24 a Zirin Gaza

Published: 10th, July 2025 GMT

Sojojin Isra’ila sun kashe Falasdinawa 24 daga cikin dare zuwa wayewar garin ranar Alhamis a Zirin Gaza.

Majiyoyi a yankin sun shaida wa gidan talabijin na Al-Jazeera cewa akasarin mutum 24 din da aka kashe a zirin na Gaza mata ne da kananan yara.

NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Sa Cin Kifi Yadda Ya Kamata Ba Tinubu kaɗai ne ya sa Buhari ya ci zaɓe a 2015 ba – Boss Mustapha

Akasarin mutanen dai an kashe su ne a tsakiya da kudancin zirin na Gaza.

Ma’aikatan lafiya a asibitin Al-Aqsa da ke Gaza sun ce a yankin Deir el-Balah kawai akwai Falasdinawa 13 da aka kashe sannan an jikkata wasu da dama.

Gabanin nan ma, Isra’ila ta kashe mutum hudu a harin da ta kai sansanin ’yan gudun hijira na Bureij, shi ma wanda ke tsakiyar Gaza.

Sama da mutum 700 ne Isra’ila ta kashe Falasdinawa 700 da ke kokarin karbar tallafi a wuraren karbar tallafi na Gidauniyar GHF wanda Amurka da Isra’ilar suke goya wa baya tun lokacin da aka kaddamar da shi a watan Mayu.

Daga cikin mutanen dai akwai yara kanana da dama, ciki har da wani jariri dan kwana 10 da haihuwa.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Falasdinawa Isra ila

এছাড়াও পড়ুন:

Zagaye na 5 A Tattaunawar Gaza da HKI  Ya tashi ba tare da Sun Dai-daita ba A Doha

Tattaunawa na baya-bayan nan tsakakin HKI da Hamas ya tashi ba tare da wani ci gaba ba a birnin Doha na kasar Qatar. Idan an cimma wannan yarjeniyar dai ana saran musayan fursinoni 10 na HKI sannan za’a saki wasu da dama dake hannun HKI,

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa rashin nasarar wannan taron ya sanya makomar yaki a Gaza cikin rudu don yanzun kuma ba’a san abinda zai faru ba. Kuma bamu san manufar HKI ba a wannan yakin.

Wani jami’in Falasdinawa ya fadawa tashar talabijin ta Al-Sharq kan cewa da alamun tawagar yahudawan sunzo ba taren da niyyar cimma wani Abu ba, tunda duk abunda aka  tambayesu sai suce sai sun tambayi tel-Aviv, wanda ya nuna basu zo don cimma wata yarjeniya ba.

Don haka jami’in ya zargi HKI da wargaza tattaunawar. Mai yuwa kuma suna kan shirin na korar Falasdinawa daga Gaza gaba daya,

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  •  HKI Tana Cigaba Da Yi Wa Mutanen Gaza Kisan Kiyashi
  • An gurfanar da wasu kan zargin kashe matafiya bikin aure a Jos
  • Zagaye na 5 A Tattaunawar Gaza da HKI  Ya tashi ba tare da Sun Dai-daita ba A Doha
  • ’Yan bindiga sun kashe mutum 13 a ƙauyukan Neja
  • HOTUNA: Obi ya ziyarci iyalin Ɗantata don yi musu ta’aziyya
  • Kungiyar Hamas Ta Yi Fatali Da Mahangar Yahudawan Sahayoniyya Ta Neman Falasdinawa Su Rusuna Musu
  • HKI Ta Kashe Falasdianwa 6 A Gaza, Kuma Tsoffin Fursinoni
  • ‘Yan Gwagwarmayar Falasdinu Sun Halaka Sojojin Mamaya Biyar Tare Da Jikkata Wasu Goma Na Daban
  • Falasdinawa 13 Ne Suka Yi Shahada Wasu Da Dama Suka Jikkata A Hare-Haren Sojojin Mamayar Isra’ila A Gaza