Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, yace nasarorin da gwamnatin Tinubu ta samu cikin shekaru biyu kadai shaida ce ta shugabanci mai hangen nesa da jaruntaka.

 

Ya bayyana haka ne a yayin taron farko na National Dialogue on Citizen Engagement and National Security da aka gudanar a Abuja, mai taken “One Voice, One Vision: Uniting Perspectives for a Stronger Nigeria.

 

A cewar Ministan, wannan taro ya zo a daidai lokacin da Najeriya ke kokari yi amfani da damamaki da ke gabanta.

 

Ya jaddada cewa wannan dandali da Voice of Nigeria (VON) ta shirya ba kawai taron tattaunawa kan manufofi bane, sai dai wata kafa ce da aka tanada domin hada ra’ayoyi da abubuwan da talakawa ke fuskanta a rayuwarsu ta yau da kullum.

 

“Ko a makon da ya gabata,” in ji Idris, “mun yi bikin cikar gwamnatin Tinubu shekaru biyu da hujjoji masu dama na irin ci gaba da sauyi da aka samu.”

 

Ministan ya bayyana cewa babu wata gwamnati a tarihin dimokuradiyyar Najeriya da ta samu irin wadannan nasarori da sauye-sauye cikin shekaru biyu.

 

“Babu wata gwamnati da ta riga ta aiwatar da abin da gwamnatin Tinubu ta yi: Da farko, jarumtakar kawar da tallafin man fetur da magudin canjin kudi, sannan gina hanyoyi da dama, tsarin bayar da rancen karatu ga dalibai na farko a tarihin Najeriya, da kuma CreditCorp – manufofin da ke dawo da kwarin gwiwar matasa a fadin kasa.”

 

Ya kara da cewa manufofin gwamnatin Tinubu sun fara haifar da gagarumin sakamako.

 

“Duk da kalubalen farko, farashin abinci na sauka, kuma muna ci gaba da dakile matsalar rashin tsaro. Har ila yau, tasirin mulki na fara tabuka abubuwa ta hanyar: ‘yancin kan kananan hukumomi, kirkiro ma’aikatun ci gaban yankuna, da kuma babban cigaba a fannin noma – wato kafa Ma’aikatar Raya Noman Dabbobi ta Tarayya.”

 

“Ina tabbatar da cewa ƙarƙashin shugabancin Bola Ahmed Tinubu, muradun al’umma na kara hade, suna goyon bayan shugaba mai hangen nesa da jaruntaka,” in ji shi.

 

Yayin da yake fayyace muhimmancin taron, Ministan ya bayyana cewa haɗin kan ƙasa da amincewar jama’a sune ginshiƙan tsaron ƙasa.

 

“Ba za a samu tsaro ba idan ba a samu haɗin kai ba. Kuma ba za a samu haɗin kai ba idan babu amincewa. A lokacin rashin tabbas da barazana, makaminmu mafi ƙarfi ba bindiga ba ce – ita ce amincewa tsakanin masu mulki da wadanda ake mulkawa.”

 

Ya ce manufar Renewed Hope Agenda ta ginu ne akan shiga da tasirin al’umma, inda duk wani dan Najeriya ya zama mai muhimmanci, a saurare shi, a ganshi, a kuma darajanta shi.

 

Ministan ya kuma yaba da rawar da Voice of Nigeria ke takawa, inda ya ce tana kara wuce matsayin kafar yada labarai kawai.

 

“VON ba wai kawai tana watsa labarai ba ce – tana gina labari da gina matsayin kasa tana tabbatar da cewa ko da a cikin Hausa, Yarbanci, Igbo ko Turanci ne, ko a Berlin ko a Birnin Kebbi ne, muryar Najeriya na ji da daraja, kuma ana girmama ta daga cikin ƙasa daya mai haɗin kai da tsaro.”

 

Yayin da yake kiran hadin gwiwa tsakanin dukkan bangarorin kasa, Idris ya ce:

“Wannan dandalin yana nuna wannan hangen nesa – yana haɗa gwamnati, kafafen yada labarai, kungiyoyin fararen hula, da jami’an tsaro, ba cikin kangi ba, sai dai cikin hadin kai. Ba don a yi wa juna magana ba ne, sai dai a saurari juna.”

 

Ministan ya jaddada cewa Nigerians ba sai sun zama daya ba kafin su hada kai; za su iya karbar bambance bambancen juna, tare da ci gaba da zama tsintsiya madauri daya.

 

“Wannan tattaunawar ita ce misalin irin wannan dama – dandalin da ba a gogewa bambance bambance ba, sai dai a rungume su a matsayin mafita ta hadin gwiwa. Ina kira gare mu da mu fita daga nan ba da tunani kawai ba – sai dai da niyyar aiki. Sabuwar niyya ga gaskiya a kafafenmu, adalci a manufofinmu, gaskiya a mulkinmu, da jin kai a cikin al’ummarmu.”

 

Wadanda suka halarci taron sun hada da Ministan Harkokin Jin Kai da Rage Talauci, Farfesa Nentawe Goshe Yilwatda; Babban Hafsan Tsaro, Janar Christopher Musa; Shugaban Hukumar Kiyaye Hadurran Hanya (FRSC), Shehu Mohammed; Daraktan Hukumar Kula da Jaridu, Dr. Dili Ezugha; Daraktan Hukumar Wayar da Kan Jama’a, Malam Lanre Issa-Onilu; Shugaban Hukumar Masana Yada Labarai (NIPR), Dr. Ike Neliaku; Tsohon Babban Hafsan Sojojin Kasa, Janar Yusuf Tukur Buratai; da Babban Sakatare na Ma’aikatar Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a ta Tarayya, Mista Ogbodo Chinasa Nnam, da sauransu.

 

Adamu Yusuf

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Labarai Nasarorin Shekaru Yada

এছাড়াও পড়ুন:

Zan Ci Gaba da Taka Leda A Kano Pillars Duk da Matsayin Da Na Samu — Ahmed Musa

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Zan Ci Gaba da Taka Leda A Kano Pillars Duk da Matsayin Da Na Samu — Ahmed Musa
  • Tinubu na amfani da ƙarfin mulki wajen tsoratar da ’yan adawa — Sule Lamido
  • Tinubu Ba Zai Taɓa Tauye ’Yancin Kafafen Yaɗa Labarai Ba, In ji Ministan Yaɗa Labarai
  • Shugaban Amurka Trump Ya Bukaci Gurfanar Da Tsohon Shugaban Amurka Barack Obama A gaban Kuliya
  • Kasar Sin Tana Da Dokoki Da Ka’idoji Sama Da 180 Dake Kare Nakasassu
  • Yanzu-Yanzu: Majalisa Ta Amince Wa Tinubu Ciwo Bashin Dala Biliyan 21
  • NAJERIYA A YAU: Yadda tsadar taki ke hana noman masara da shinkafa
  • Jihohin da za a samu ruwan sama da iska mai ƙarfi a sassan Nijeriya — NiMet
  • Kasar Sin Na Fatan EU Za Ta Yi Aiki Da Ita Bisa Alkibla Guda Da Tsara Hadin Gwiwa Na Shekaru 50 Masu Zuwa
  • Wata Kungiyar Ta Bukaci Shugaban Kasa Ya Cika Alkwarin Marigayi Shugaba Buhari Game Da Shehu Usman Aliyu Shagari