Jihohin Da Za Su Iya Fuskantar Ambaliyar Ruwa A Watan Yuni – NiMet
Published: 3rd, June 2025 GMT
Hukumar ta buƙaci jama’a da su kasance cikin shiri tare da bibiyar sabbin rahotannin yanayi da ta ke fitarwa.
Ta kuma ja hankalin hukumomin da ke kula da madatsun ruwa da su saka ido kan matakin ruwa domin gujewa cike-ciken da ka iya haddasa ambaliya.
Rahoton ya ƙara da cewa jihohin kudancin Nijeriya da kuma na Arewa ta Tsakiya za su riƙa samun ruwan sama da iska a kai a kai.
Sai dai NiMet ta ce jihohin Kwara, Kogi, Neja, Nasarawa, Benuwe, Taraba, Adamawa, Kaduna, Kano, Katsina, Sakkwato, Edo, Delta da Abuja ba za su samu ruwan sama da yawa kamar yadda aka saba ba.
Hukumar ta buƙaci manoma da su yi amfani da dabarun zamani da ilimin kimiyya wajen gudanar da harkokin noma a wannan daminar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Ambaliyar Ruwa
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Namadi Ya Sanya Hannu Kan Dokar Kafa Hukumar Hisba Ta Jihar Jigawa
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya sanya hannu kan kudurin dokar da ta kafa Hukumar Hisba a matsayin hukuma ta dindindin a ƙarƙashin gwamnatin jihar.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na gwamnan Hamisu Muhammad Gumel ya fitar ga manema labarai a Jigawa.
Sanarwar ta bayyana cewa bikin sanya hannun ya gudana ne a zauren majalisar zartarwa na fadar gwamnati dake Dutse, inda manyan jami’an gwamnati suka halarta, ciki har da Mataimakin Gwamna, Injiniya Aminu Usman, da mambobin Majalisar Dokokin Jihar Jigawa karkashin jagorancin Mataimakin Kakakin Majalisar, Hon. Sani Isyaku.
Ta ce Gwamna Namadi ya bayyana cewa wannan rana na ɗaya daga cikin manyan nasarorin da aka cimma, bayan kai-komo na sama da watanni takwas da bangaren majalisar dokoki da majalisar zartarwa suka yi domin kaiwa ga gaci.
“Yau mun kammala aikin da muka fara kusan watanni bakwai zuwa takwas da suka gabata. Da ikon Allah, an kammala kudurin da ya kafa hukumar Hisba a matsayin cikkakiyar hukuma a Jihar Jigawa,” in ji gwamnan.
Gwamnan ya yi wa hukumar fatan alkhairi, tare da fatan za ta kawo ƙarin daidaito da tarbiyya a cikin al’umma.
Ya kuma shawarci ma’aikatan Hisba da su kasance masu tsoron Allah, adalci da kuma jajircewa a yayin gudanar da aikinsu.
Gwamna Namadi ya yaba wa kwamitin da ya shirya kudurin bisa himma da sadaukarwa wajen kammala wannan aiki mai muhimmanci.
Bayan sanya hannu kan wannan doka, yanzu hukumar Hisba ta samu cikakken iko na gudanar da aikinta a duk fadin Jihar Jigawa bisa tsarin da aka shimfiɗa na inganta tarbiyya, adalci da walwalar al’umma.
Usman Muhammad Zaria