Arakci: Cinikayya A Tsakanin Iran Da Masar Za Ta Kara Bunkasa
Published: 2nd, June 2025 GMT
Ministan harkokin wajen Jamhuriyar musuluinci ta Iran wanda ya kai Ziyarar aiki kasar Masar ya bayyana cewa, cinikayya a tsakanin kasashen biyu za ta karu.
Ministan harkokin wajen na Iran wanda ya gabatar da taron manema labaru na hadin gwiwa da takwaransa na kasar Masar ya ce: “A bisa yarjejeniyar da bangarorin biyu su ka cimmawa za a kara girman kasuwancin da ake tsakanin Iran da Masar.
Abbas Aragchi ya godewa mai masaukinsa na Masar Badar Abdulatif, saboda tattaunawa mai muhimmanci da su ka yi.”
Bugu da kari Abbas Arakci ya yi wa shugaban kasar Masar godiya saboda ganawa da ya yi da shi, yace: Wannan Shi ne ganawata ta hudu da shugaban da shi daga sheakarar da ta gabata’.
Har ila yau, ministan harkokin wajen na Iran ya yaba ganawar da aka yi a tsakanin shugabannin kasashen Iran da na Masar, a taron kungiyar kasashen musulmi da aka gudanar a bara. Sannan ya kammala da cewa wannan yana nuna irin muhimmancin da kasashen biyu suke daukar juna.
Da yake Magana akan yakin Gaza kuma, ministan harkokin wajen na Iran ya jinjinawa Masar da Qatar saboda kokarin da suke yi na ganin an dakatar da yaki.”
Dangane da tattaunawar Nukiliya tsakanin Iran da Amurka kuma, ministan harkokin wajen na Iran ya ce: Manufar tattaunawar ita ce tabbatar da cewa Iran baa ta nufin kera makamin Nukiliya, kuma akwai yiyuwar a kai ga cimma yarjejeniya.”
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Kano Ta Inganta Cibiyoyin Horas Da Sana’o’i Domin Dakile Aikata Laifuka Tsakanin Matasa
Gwamnatin Kano ta raba kayayyakin aiki na zamani na kimanin Naira Miliyan 250 ga cibiyoyin horas da sana’o’in hannu biyu da ke Kofar Mata da Gwale, domin yaƙi da shan miyagun kwayoyi da aikata laifuffuka a tsakanin matasa, ta hanyar samar da aikin yi.
Kwamishinan Kimiyya da Fasaha, Dakta Yusuf Kofarmata, ya ce an amince da tallafin ne bisa umarnin Gwamna Abba Kabir Yusuf don bunƙasa tsare-tsaren ƙarfafa matasa a jihar.
Ya bayyana cewa an samar da injinan sarrafa fata guda 26 domin cibiyoyin wadanda al’ummar yankunan suka kafa, amma ba su da isassun kayayyakin aiki.
Ya ce Gwamna Yusuf ne ya gina Cibiyar Horaswar ta Gwale kasancewar nan ce mazabarsa, yayin da Dakta Yakubu Adam ya taka rawa wajen gina ta Kofar-Mata.
Ya ce cibiyoyin za su samar da daruruwan ayyukan yi tare da rage matsalolin zaman kashe-wando da ta’addanci a tsakanin matasa.
A nasa jawabin, Ali Musa Kofar-Mata na ƙungiyar IKMA ya gode wa gwamnati bisa wannan gudummawar da ya kira mai sauya rayuwa.
Ya ce cibiyar ta fara ɗaukar matasa maza da mata, kuma horon zai ɗauki watanni uku kafin a shiga sabon zagaye.
Abdullahi Jalaluddeen