HausaTv:
2025-09-17@23:17:12 GMT

Turkiya: An Bude Tattaunawa A Tsakanin Rasha Da Ukiraniya

Published: 2nd, June 2025 GMT

Ministan harkokin wajen Turkiya Hakan Fidan ya jaddada goyon bayan da kasarsa take bai wa tattaunawar da ake yi a tsakanin Rasha da Ukiraniya, ya kuma kara da cewa; Ana yin nazarin yadda za a gana, a kuma tattauna tsakanin shugabannin kasashen biyu.”

Fidan ya kuma bayyana fatansa na ganin cewa tattaunawar da aka bude a yau ta kai ga haifar da daa mai ido.

Haka nan kuma ya ce, kasarsa za ta yi duk abinda za ta iya, domin ganin cewa kasashen biyu sun kai ga cimma yarjejeniyar zaman lafiya a tsakaninsu.

 Kafar watsa labaru ta Axios; ta ambato majiyar Ukiraniya na cewa, Rasha ta gabatar da tsarin zaman lafiya wanda ya kunshi yadda za a kawo karshen yaki.

A yau Litinin ne aka yi ganawa a tsakanin tawagogin kasashen biyu a birnin Istanbul domin lalubo hanyoyin zaman lafiya tsakanin Rasha da Ukraniya.

 Gabanin zaman Istanbul dai, ministan harkokin wajen Rasha Sergey Lavrov ya ce; kasarsa tana da tsarin yadda za a kawo karshen yaki ta hanyar magance matsalar daga tushe.

Tattaunawar tana zuwa ne, kwana guda bayan da Ukiraniya ta kai wasu munanan hare-hare a yankuna masu nisa na cikin kasar Rasha da su ka hada da cibiyar muhimman jiragen Rasah masu kai hari a yankin Siberia tare da tashin gobara a cikin wasu jiragen.

Yankuna biyar ne dai a Rasha ,kasar Ukiraniya ta kai wa hare-hare daga ciki har da wurin da ya kai nisan kilo mita 4000 daga kan iyakar kasashen biyu.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Sojoji sun harbe mayaƙan ISWAP 8 a Borno

Sojojin Najeriya sun kashe aƙalla mayakan ƙungiyar ISWAP 8, ciki har da manyan kwamandojinta biyu a Jihar Borno.

Wata majiyar leƙen asiri daga rundunar haɗin kai ta OPHK ta bayyana cewa an kashe ’yan ta’addan ne a wata arangama da suka yi da sojojin a kan hanyar Maiduguri zuwa Baga a safiyar ranar Litinin.

DSS ta maka Sowore da Facebook a Kotu kan cin zarafin Tinubu Gwamnatin Kano ta gayyaci Mai Dubun Isa da Shehi Tajul-Izzi kan shirya muƙabala

A cewar majiyoyin, an yi arangamar ce a kusa da Garin Giwa da ke gab da ƙauyen Kauwa, lokacin da ’yan ta’addan suka yi wa dakarun da ke sintiri kwanton ɓauna.

“A yayin wannan artabu, an kashe ’yan ta’adda takwas, ciki har da Munzirs biyu (kwamandojin filin daga na ƙungiyar) da kuma Qaid ɗaya (shugaban sashe).

“An kashe Modu Dogo, Munzir daga Dogon Chukun, wani Munzir da ba a bayyana ba, da Abu Aisha, shugaban sashe (Qaid) daga Tumbun Mota,” in ji wata majiya.

Majiyar ta ƙara da cewa wasu mayaƙa da dama sun samu raunuka, musamman waɗanda suka tsere da ƙafa bayan sun yi watsi da babura 14 da sojojin suka ƙwato.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Kano Ta Inganta Cibiyoyin Horas Da Sana’o’i Domin Dakile Aikata Laifuka Tsakanin Matasa
  • Sojoji sun harbe mayaƙan ISWAP 8 a Borno
  • Yawan Hatsin Da Aka Girbe A Kasar Sin Tsakanin Shekarar 2021-2025 Ya Kai Wani Sabon Matsayi
  • Gwamnatin Kano ta gayyaci Mai Dubun Isa da Shehi Tajul-Izzi kan shirya muƙabala
  • Baqa’i: Kowace Kasa A Duniya Tana Da Hakkin Mallakar Makamashin Nukiliya Na Zaman Lafiya
  • ’Yan bindiga sun kai wa sojoji hari a ranar da ake zaman sulhu
  • Hadin Gwiwar Raya Tattalin Arziki Da Cinikayya Da Makamashi Tsakanin Sin Da Rasha Ba Abun Zargi Ba Ne
  • Tawagogin Sin Da Na Amurka Sun Sake Tattaunawa Game Da Batutuwan Tattalin Arziki Da Cinikayya A Rana Ta Biyu
  • Ɗan Majalisar Tarayya Ya Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-haren Ta’addanci A Sakkwato 
  • Kasashen Larabawa da na Musulmi na taron gaggawa kan harin Isra’ila a Qatar