Aminiya:
2025-11-02@03:37:26 GMT

Ma’aikatan Kotu Koli sun janye yajin aikin da suka shirya tafiya

Published: 2nd, June 2025 GMT

Ma’aikatan shari’a a Kotun Koli da sauran kotuna sun jinginr shirinsu na fara yajin aiki daga yau Litinin 2 ga watan Yuni domin matsa lamba kan aiwatar da sabbin albashi.

Ma’aikatan, a karkashin kungiyar Ma’aikatan Shari’a ta Najeriya (JUSUN), sun ce sun janye shiga  yajin aikin ne bayan wani taro da suka yi da Alkalin Alkalan Najeriya, Kudirat Kekere-Ekun inda aka ba su tabbaci mai ƙarfi.

Haka zalika, ma’aikatan Hukumar Shari’a ta Kasa (NJC) da Kotun Koli ta Tarayya (FHC) sun kuma yanke shawarar ba za su ci gaba da yajin aikin ba.

A cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na reshen NJC na JUSUN, Joel Ebiloma, ya bayar, ya ce kungiyar ta ba hukumomi wa’adin makonni biyu don ba su damar kintsawa don biyan buƙatunsu.

Uba ya harbe ɗansa har lahira saboda zaton biri ne Jirgin soji ya kashe ’yan sa-kai 20 da ke fatattakar ’yan bindiga a Zamfara

Sanarwar ta ƙara da cewa an dakatar da yajin aikin ne domin bai wa Ofishin Akanta Janar na Tarayya damar fitar da kasafin kudi ga ɓangaren shari’a bisa kasafin kudin 2025 wanda ya haɗa da biyan bashin ƙarin albashi, mafi ƙarancin albashi, da kuma ƙarin kashi 25%/35% na albashi.

Sai dai, Kotun Koli a cikin wata sanarwa da ta fitar a ƙarshen taronta ta ce ma’aikatan sun cimma matsaya na ba za su shiga yajin aikin ba bayan nazarin batutuwan da ƙoƙarin CJN na biyan buƙatunsu.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Ma aikatan Shari a Yajin aiki yajin aikin

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Jihar Kwara Ta Kafa Kwamitoci 2 Don Tantance Wadanda Suka Yi Ritaya

Daga Ali Muhammad Rabi’u 

 

Gwamnatin Jihar Kwara ta kafa kwamitoci biyu domin tantance bayanan wadanda suka yi  ritaya a matakin jiha da  kananan hukumomi.

A cikin wata sanarwa da Kwamishinar Kudi ta jihar, Dakta Hauwa Nuru ta fitar, ta bayyana cewa kwamitocin za su tantance tare da tabbatar da sahihancin bayanan wadanda suka yi ritaya, domin a biya su bisa lokacin da suka bar aikin gwamnati.

A cewarta, kwamitin mutum takwas da aka kafa don kula da kudaden ritaya na matakin jiha zai kasance karkashin jagorancin Mai Duba Asusun Jiha, wato (Auditor General), yayin da wanda ke kula da matakin kananan hukumomi zai kasance karkashin Mai Duba Asusun Kananan Hukumomi.

Sanarwar ta bayyana cewa babban burin kwamitocin shi ne tabbatar da cewa an tattara bayanan masu ritaya bisa gaskiya da adalci, tare da  biyan su kai tsaye ta asusun ajiyar banki.

Ta kara da cewa, mambobin kwamitocin sun hada da wakilan tsofaffin manyan sakatarorin, kungiyar tsofaffin ma’aikata, Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC), da kungiyar kwadago ta TUC, da sauransu.

 

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Cafke Ma’aikatan Gidan Marayu Da Suka Sayar Da Yara 4 A Kan Naira Miliyan 3
  • Gwamnatin Jihar Kwara Ta Kafa Kwamitoci 2 Don Tantance Wadanda Suka Yi Ritaya
  • Kotu ta dakatar da gudanar da babban taron PDP
  • Kotu ta dakatar da babban taron PDP na ƙasa
  • Kotu ta dakatar da babban taron PDP
  • Rundunar Sojin Nijeriya Ta Shirya Wa Janar Musa Faretin Gama Aiki
  • Kotu ta tsige dan majalisar da ya sauya sheka zuwa APC
  • Majalisar Dattawa Ta Tabbatar Da Bernard Doro A Matsayin Ministan Harkokin Jin Ƙai
  • Jihar Jigawa Ce Ta Fara Biyan Kudaden Kujerun Aikin Hajjin 2026- NAHCON
  • Majalisar Dokokin Kano Ta Ce An Yi Rashin Adalci Wajen Ɗaukar Aikin Kwastam A Nijeriya