Nukiliya : Iran ta gargadi kasashen yamma akan daukar duk wani irin mataki kan ta
Published: 2nd, June 2025 GMT
Iran ta gargadi kasashen yamma aka daukar duk wani irin mataki kan ta a daidai lokain da ake shirin gudanar da taron gwamnonin hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya a mako mai zuwa.
Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin shari’a da na kasa da kasa ya yi watsi da rahoton da hukumar ta IAEA ta fitar kan shirin nukiliyar Iran na zaman lafiya, yana mai gargadin daukar matakin da ya dace.
Kazem Gharibabadi ya yi wadannan kalamai ne, bayan da hukumar ta IAEA ta yi zargi a cikin wani rahotonta na sirri ga kasashe mambobinta cewa Iran ta gaza bayar da rahoton ayyukanta na nukiliya a wasu wurare uku da ba a bayyana ba, tare da bayyana damuwarta game da tarin uranium da ake zargin an wadatar da shi zuwa kashi 60 cikin dari.
Ya ce rahoton ya dogara ne kan “jerin bayanan karya da gwamnatin sahyoniya ta bayar” tun sama da shekaru ashirin.
Ya kara da cewa, an yi watsi da dukkan tuhume-tuhume kan ayyukan nukiliyar Iran da suka gabata a karkashin kudurin kwamitin sulhu na MDD mai lamba 2231, wanda a hukumance ya amince da yarjejeniyar nukiliyar Iran ta 2015.
Gharibabadi ya kuma lura cewa rahoton na hukumar ya sake nuna yadda IAEA ke siyasantar da ayyukanta a kan Iran.
Ya sake nanata cewa “Iran ba ta neman makaman nukiliya kuma ba ta da wani makaman nukiliya.” Kamar yadda ake ta yayatawa.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran: Sojojin Ruwan Iran Sun Kori Jirigin Yakin Amurka Daga Tekun Oman
Sojojin ruwan Iran sun sanar da cewa, wani jirgin ruwan Amurka na yaki da ya yi kokarin shiga tekun Oman, ya fuskanci gargadi daga sojojin ruwan Iran tare da tilasta masa janyewa.
Da saiyar yau Laraba ne dai jirgin sama mai saukar angulu mallakin sojojin ruwa, ya yi gargadi ga jirgin ruwan na Amurka da a karshe ya tilasta masa janyewa.
Da fari, jirgin ruwan yakin na Amurka ya yi wa jirgin sama mai saukar angulu na Iran barazanar kai masa hari, said ai duk da haka sojojin ruwan na Iran sun ci gaba da yin gargadi ga Amurkawan da su kar su shiga cikin ruwan tekun Oman.
Bayan wannan barazana ne aka aikewa jirgin ruwan Amurkan sako daga dakarun tsaron sararyin samaniyar Iran akan cewa, wannan jirin mai saukar angulu yana da cikakkiyar kariya, don haka wajibi ne ga jirgin ruwan na Amurka mai suna “DDG Fitzgerald ya janye.