Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Kai Hari kan Falasdinawa Masu Karban Agajin Jin Kai A Rafah
Published: 2nd, June 2025 GMT
Sojojin mamayar Isra’ila sun kai hari kan fararen hula da suka yi tawaga zuwa wajen raba kayan agajin jin kai a garin Rafah
Rahotonni sun bayyana cewa: A rana ta biyu a jere, sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da aiwatar da kisan kiyashi kan al’ummar zirin Gaza da ke fama da yunwa.
Shafin yanar gizo na Falestine Today ya watsa rahoton cewa: A safiyar yau Litinin 2 ga watan Yunin shekara ta 2025, sojojin mamayar Isra’ila sun aiwatar da wani sabon laifi ta hanyar kai hare-hare kan Falasdinawa a kusa da cibiyar bada agajin Amurka da ke birnin Rafah.
Majiyoyin cikin gida sun tabbatar da cewa: An kai wa daruruwan Falasdinawa hare-hare ne a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa cibiyar ba da agaji da ke Rafah, inda hare-haren suka yi sanadaiyyar shahadar Falasdinawa 3, sannan wasu fiye da 60 suka jikkata.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Isra ila sun
এছাড়াও পড়ুন:
A Kalla Falasdinawa 10 Yunwa Ta Kashe A Gaza A Cikin Sa’o’i 24
Ma’aikatar kiwon lafiya ta Gaza ta sanar da cewa a cikin sa’o’i 24 da su ka gabata adadin falasdinawan da su ka yi shahada saboda yunwa sun kai 10.
Daga lokacin da HKI ta fara amfani da yunwa a matsayin makamin yaki,adadin falasdinawan da su ka yi shahada sun kai 111.
Wannan adadin yana nuni da yadda rashin abinci ya tsananta a cikin yankin na Gaza saboda yadda Isra’ila ta killace yankin ta hana a shigar da abinci a ciki.
A gefe daya, HKI tana ci gaba da kashe Falasdinawa ta hanyar yi musu kisan kiyashi, da a yau kadai fiye da mutane 80 ne su ka yi shahada. Mafi yawancin wadanda su ka yi shahada a cikin sa’oin nan na baya suna a unguwannin Tallul-Hawa, da Deir-Balah. Haka nan kuma ‘yan sahayoniyar sun kai wasu hare-haren a sansanin ‘yan hijira dake Mukhayyam-Shadhi.
Kungiyoyin kasa da kasa suna ta ci gaba da yin kira da a bude iyakokin Gaza domin a shigar da kayan abinci, sai dai babu faruwar hakan.
A cikin zirin Gaza dai, mutane suna faduwa suna somewa, wani lokaci mutuwa saboda yunwa, ba kuma babba babu yaro.
Mafi yawancin mutanen da suke mutuwa dai kananan yara ne, jarirai da matasa.