Shafin Watsa Labaran Amurka Ya Bankado Illar Da Sojojin Yemen Suka Yi Wa Jirgin Truman Na Amurka
Published: 2nd, June 2025 GMT
Wani shafin yanar gizo na sojojin Amurka ya tabbatar da cewa dakarun kasar Yemen ne suka kaiwa jirgin Truman mai dakon jiragen sama hari
Wani shafin yanar gizo na sojojin Amurka ya amince da cewa: Dakarun kasar Yemen ne suka lalata jirgin Truman.
Shafukan yanar gizo na rundunar sojin Amurka Stars and Stripes sun watsa rahoton a yau Litinin cewa: Jirgin dakon jiragen sama USS Harry S da Truman sun dawo Amurka bayan da rikici ya yi tsanani a yankunan da suke shawagi.
An lura cewa manyan bangarorin jirgin dakon jiragen saman Amurka a teku sun samu matsalolin fashe-fashe wanda hakan ke bayyana cewa; Jirgin Ruwan Truman da ma’aikatansa sun samu matsalolin ne a cikin tekun Bahar Maliya.
Shafukan Stars and Stripes sun jaddada cewa: Rundunar sojin Ruwan Amurka ta ki ta tattauna batutuwan da suka shafi jirgin Ruwan Truman a tekun Bahar Maliya a hannun sojojin Yemen, inda suka ce ana ci gaba da gudanar da bincike.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sojoji sun harbe mayaƙan ISWAP 8 a Borno
Sojojin Najeriya sun kashe aƙalla mayakan ƙungiyar ISWAP 8, ciki har da manyan kwamandojinta biyu a Jihar Borno.
Wata majiyar leƙen asiri daga rundunar haɗin kai ta OPHK ta bayyana cewa an kashe ’yan ta’addan ne a wata arangama da suka yi da sojojin a kan hanyar Maiduguri zuwa Baga a safiyar ranar Litinin.
DSS ta maka Sowore da Facebook a Kotu kan cin zarafin Tinubu Gwamnatin Kano ta gayyaci Mai Dubun Isa da Shehi Tajul-Izzi kan shirya muƙabalaA cewar majiyoyin, an yi arangamar ce a kusa da Garin Giwa da ke gab da ƙauyen Kauwa, lokacin da ’yan ta’addan suka yi wa dakarun da ke sintiri kwanton ɓauna.
“A yayin wannan artabu, an kashe ’yan ta’adda takwas, ciki har da Munzirs biyu (kwamandojin filin daga na ƙungiyar) da kuma Qaid ɗaya (shugaban sashe).
“An kashe Modu Dogo, Munzir daga Dogon Chukun, wani Munzir da ba a bayyana ba, da Abu Aisha, shugaban sashe (Qaid) daga Tumbun Mota,” in ji wata majiya.
Majiyar ta ƙara da cewa wasu mayaƙa da dama sun samu raunuka, musamman waɗanda suka tsere da ƙafa bayan sun yi watsi da babura 14 da sojojin suka ƙwato.