NAJERIYA A YAU: Mokwa: Tsakanin Taraddadin Rashin Matsuguni Da Jimamin Rashin ’Yan-Uwa
Published: 2nd, June 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Shin wanne ya fi zafi – takaicin rasa matsuguni ko alhinin rashin sanin halin da ɗan uwa na jini yake ciki?
Wannan ne halin da wasu al’ummomi a Ƙaramar Hukumar Mokwa ta Jihar Neja suke ciki, bayan da suka tsinci kansu tsamo-tsamo a tsakiyar wata mummunar ambaliyar ruwa.
Wasu mutanen da dama dai sun yi batan dabo a wannan ibitila’i, wanda ya yi sanadiyyar rayukan mutanen da adadinsu ya haura 150.
NAJERIYA A YAU: Yaya Girman Matsalar Rashin Tsaro A Shekaru Biyun Tinubu? DAGA LARABA: “Sai Na Tara Kudin Cin Abinci Na Nake Iya Siyan Audugar Al’ada”Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan yadda wadannan dubban mutane suka kai labari da halin da suke ciki.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ambaliyar ruwa Mokwa
এছাড়াও পড়ুন:
Sheikh Qasem: Nuna Halin Ko In-Kula Na Duniya Ne Ya Jawo Kisan Kiyashi A Gaza
Sakatare-janar na kungiyar Hizbullah Sheikh Naim Qasem ya fitar da wata sanarwa inda ya yi kakkausar suka da Allah wadai da abin da ya bayyana a matsayin yakin kisan kare dangi da Amurka da Isra’ila ke yi wa al’ummar Palasdinu a Gaza, yana mai zargin kasashen duniya da yin shiru a kan laifukan da suka zarce dukkan matakan jin kai da kuma kyawawan dabi’u na ‘yan adataka.
“Abin da al’ummar Falasdinawan da ake zalunta ke jurewa a Gaza, tun daga cin zarafi na Amurka da Isra’ila, zuwa ta’addanci, kisan kiyashi, jefa su a cikin yunwa, da kashe jama’a, ya wuce duk wani mataki na lamirin dan adam,” in ji Sheikh Qassem.
Ya kuma yi kakkausar suka ga gazawar manyan kasashen duniya da gaza aiwatar da dokokin kasa da kasa, yana mai cewa, “Shiru da kasashen duniya suka yi, abin Allah wadai ne ga gwamnatocin kasashen duniya, musamman na kasashen musulmi da larabawa.
Da yake ishara da kiraye-kirayen baya-bayan nan da kasashe sama da ashirin suka yi na a dakatar da yakin, Sheikh Qassem ya yi ishara da cewa irin wadannan kalamai da cewa ba su isa ba ko kadan, Ya ce, “bai isa ba a ce kasashe 25 sun yi kira da a dakatar da yakin Gaza, wannan furucin kadai bai wadatar ba.
Sheikh Qassem ya yi kira da a kakaba takunkumi kan “Isra’ila”, da gurfanar da su a gaban shari’a, da kuma dakatar da duk wani nau’i na hadin gwiwa da ita.