Uba ya harbe ɗansa bisa saboda zaton biri ne
Published: 2nd, June 2025 GMT
Wani yaro ɗan shekara 15 ya rasa ransa bayan mahaifinsa ya harbe shi bisa kuskure, yana zaton biri ne.
Wannan lamari mai ban tausayi ya faru ne a gonar magidancin inda shi da ɗan nasa suke aiki, a yankin Iye Ekiti da ke Ƙaramar Hukumar Ilejemeje ta Jihar Ekiti.
Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Ekiti, Joseph Eribo, ya tabbatar da faruwar lamarin a yau a Ado-Ekiti.
Ya bayyana cewa manomin ya daɗe yana fama da hare-haren birai a gonarsa kuma ya kai bindiga domin kare amfanin gonarsa.
Jirgin soji ya kashe ’yan sa-kai 20 da ke fatattakar ’yan bindiga a Zamfara An lakaɗa wa Mataimakin Firinsifal duka saboda hana satar a jarabawaBinciken farko ya nuna cewa mahaifin ya lura da motsi a wata bishiya da ke kusa da shi, sai ya harba bindiga yana zaton biri ne. Bayan ya yi harbin sai ya gano cewa ya harbi dansa da ke kan bishiyar har lahira.
Tuni dai ’yan sanda suka tsare mahaifin domin yi masa tambayoyi yayin da bincike ke ci gaba kan wannan lamari mai ban tausayi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Sanda Harbe ɗansa
এছাড়াও পড়ুন:
Sojoji Sun Harbe Wasu ‘Yan Ta’adda 2 A Taraba
Danja ya ce, sojojin a yayin da suke aiki da sahihan bayanan sirri dangane da shirin kai hari kan al’ummar Chanchangi da kungiyar ta’adda ta Bojo ke shirin yi a ranar 15 ga Satumba, 2025, sun yi artabu da ‘yan ta’addan a kan hanyar Demeva zuwa Chanchangi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp