Za A Yi Taron Kasa Da Kasa Akan Mahangar Imam Khumaini Dangane Da Falasdinu
Published: 1st, June 2025 GMT
A gobe Litinin ne dai za a bude taron karawa juna sani anan Tehran mai taken; Imam Khumaini da batun Falasdinu” wanda zai sami halartar masana na cikin gida da kuma waje.
Jawabin bude taro zai fito ne daga shugaban kungiyar kare hakkokin al’ummar Falasdinu, Hujjatul-Islam Muhammad Hassan Rahimiyan, haka nan kuma magajin garin Tehran Ali Ridha Zakani zai gabatar da jawabi.
Bugu da kari a yayin wannan taron za a girmama jagororin gwgawarmaya da su ka yi shahada da su ka hada, Sahid Sayyid Hassan Nasrallah, shahid Isma’ila Haniyya, sai shahid Yahya Sinwar. Shi ma shugaban kungiyar Ansarullah ta Yemen Sayyid Abdulmalik Husi yana cikin wadanda taron na Tehran za karrama.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Namadi Ya Jinjinawa Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Bisa Ayyukan Raya Kasa
Gwamnatin Jihar Jigawa ta nuna matukar gamsuwa tare da yabawa Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu, Dr Builder Muhammad Uba bisa kokarin sa na ayyukan raya kasa.
Gwamna Umar Namadi ya bayyana hakan ne a lokacin kaddamar da bude ofishin shugaban karamar hukumar da kuma dakin taro na karamar hukumar da aka gudanar a sakatariyar karamar hukumar ta Birnin Kudu.
Ya ce shugaban karamar hukuma, Dr Builder Muhammad Uba mutum ne mai kwazo da himma wanda ya zamto abin koyi a bangaren shugabanci.
A don haka, Malam Umar Namadi ya yi kira ga sauran shugabanin kananan hukumomin jihar da su tashi tsaye wajen gudanar da ayyukan kyautata rayuwar al’ummar su domin sharbar romon mulkin dimokradiyya.
A jawabinsa na godiya shugaban ƙaramar hukumar, Dr Builder Muhammad Uba ya godewa Gwamnan bisa samun damar bude ofishin da kuma dakin taro na karamar hukumar.
Wakilinmu ya ba mu rahoton cewar, Gwamnan ya sami rakiyar Mataimakinsa, Injiniya Aminu Usman Gumel da Shugaban Majalisar Dokokin Jihar, Alhaji Haruna Aliyu Dangyatun da Sakataren Gwamnati Alhaji Bala Ibrahim da Shugaban Jami’yya na Jihar Alhaji Aminu Sani Gumel da Kwamishinoni da sauran mukarraban gwamnatin jihar.
Usman Mohammed Zaria