Ma’aikatar Lafiyar Sudan Ta Ce: An Dan Samu Ja Da Baya A Cutar Kwalara Da Ta Kunno Kai A Kasar
Published: 1st, June 2025 GMT
Ma’aikatar lafiyar kasar Sudan ta bayyana cewa: Ana ci gaba da daukan matakan ganin an shawo kan ci gaba da yaduwar masifar kwalara a kasar
Gidan talabijin na Al-Alam ya watsa rahoton cewa: A halin da ake ciki a fannin kiwon lafiya a birnin Khartoum fadar mulkin kasar bayan bullar cutar kwalara yana ta kokarin ya shawo kan matsalar tare da killace mutanen da suka kamu da cutar a wurare na musamman a babban birnin kasar Khartoum, rahotonni sun bayyana cewa: Cutar ta bazu cikin sauri a birnin.
Wakilin gidan talabijin na Al-Alam na kasar Iran ya yi nuni da cewa: Akwai kuma jahohi da dama a yankin Darfur, wadanda wasu daga cikinsu suka kamu da cutar kwalara, inda ya ce daya daga cikin abubuwan da ke kawo wannan cuta shi ne yanayin da ake fama da shi a yankin Al-Salha, inda aka shafe fiye da wata guda ana gwabza fada tsakanin sojojin Sudan da ‘yan tawayen kasar na dakarun kai daukin gaggawa, inda gawarwakin mutane suke kwance a gefen hanya, kuma sun kwashe sama da wata guda, babu wani yunkurin kwashe su, don haka suke wari tare da gurbata yanayi, wasu gawarwakin kuma aka kai su cikin teku. Duk wannan na daya daga cikin dalilan da suka haifar da yaduwar wannan cuta, amma ta dan ja da baya, a cewar ministan lafiya na tarayya, wanda ya zo musamman Khartoum domin fayyace lamarin.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Jigawa Za Ta Gina Gidaje 52 A Babban Birnin Jihar
Daga Usman Muhammad Zaria
Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da bayar da rancen kudi ga hukumar gidaje ta jihar domin gina gidaje 52 a Dutse.
A cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ya fitar, ya bayyana cewa gidajen za su kunshi masu dakuna uku da kuma dakuna biyu kowanne.
Ya ce aikin zai kasance a gaban tsohuwar unguwar majalisar dokoki, kusa da hanyar wucewa ta Jami’ar Tarayya da je Dutse, a matsayin wani shiri na asusun gina gidaje karkashin ma’aikatar gidaje, ci gaban birane da tsare-tsaren yankuna, ta hannun hukumar gidaje ta jihar.
Alhaji Sagir ya bayyana cewa, wannan mataki na nuna kudirin gwamnati wajen magance matsalar gidaje a babban birnin jihar, kara habaka ci gaban birane, tare da samar da ayyukan yi ga matasan jihar.
Ya ce an tsara wannan asusu ne domin tabbatar da dorewa, ta yadda za a ci gaba da zuba jari a ayyukan samar da gidaje masu araha a fadin jihar.
Haka kuma ya kara da cewa, gwamnatin jihar tana da kudirin ci gaba da inganta rayuwar al’ummarta, ta hanyar ayyuka masu amfani da jama’a, da ke inganta walwala, karfafa tattalin arziki, da tallafa wa matasa.
Kwamishinan ya kuma bayyana cewa, majalisar ta amince da bayar da kwangilar gyara da inganta gidan baki guda biyu (Malam Adamu Chiroma House da kuma Senator Francis Ella House) da ke cikin G9 Quarters a Dutse, da kudin sama da naira miliyan 219.7.
Ya ce aikin zai haɗa da cikakken gyara da inganta gine-ginen, gyaran hanyoyin ruwa da kuma girka tankokin ruwa ga kowanne daga cikin gidajen biyu.
Ya ce hakan na da nufin tabbatar da wadataccen ruwan sha mai dorewa a wuraren.
Alhaji Sagir Musa Ahmed ya kara da cewa, amincewar da aka yi da wannan kwangila na nuna jajircewar gwamnatin jihar wajen kula da dukiyar jama’a da kuma tabbatar da cewa gine-ginen gwamnati suna cikin yanayi mai kyau da nagarta.