Kungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afrika ECOWAS, tare da haɗin gwiwar Kungiyar Haɗin Kan Masu Kiwon Gargajiya ta Afrika CORET, ta shirya taron horaswa domin ƙarfafa fahimta kan tsarin ciyar da ɗalibai a makarantu, musamman a cikin al’ummomin makiyaya a Jihar Kaduna.

 

Da yake ƙaddamar da taron a Ladugga, cikin Karamar Hukumar Kachia ta Jihar Kaduna, Ko’odinetan Shirin na CORET, Dr.

Abdu Umar Ardo, ya bayyana cewa wannan horo wani bangare ne na ƙoƙarin tallafa wa shirin ciyar da ɗalibai a wasu makarantun Fulani da aka zaɓa.

Wannan shiri, wanda ke samun goyon bayan haɗin gwiwa daga Swiss Cooperation, na nufin tallafa wa makarantun Fulani da ke Ladugga a Kaduna da kuma Maigatari a Jihar Jigawa, inda ita kuma CORET ke zama jagorar aiwatar da shirin a jihohin biyu.

 

Ko’odinetan Shirin, Dr. Abdu Umar Ardo ya ce horon yana da nufin ƙarfafa ƙwarewar Kwamitocin Gudanar da Makarantu (SBMC), Ƙungiyoyin Iyaye Mata da na PTA, domin tallafa wa ilimin ‘ya’ya mata da rage yawan yaran da ke zaman gida ba tare da zuwa makaranta ba, musamman a cikin al’ummomin makiyaya.

 

Dr Ardo wanda ya samu wakilincin Baban Jami’in Sa Ido da Kimantawa na CORET, Alhaji Bimbi Adamu Tahir, ya shawarci mahalarta taron su yi amfani da ilimin da suka samu domin amfanar da al’ummominsu.

 

A nata jawabin, Shugabar Ƙungiyar Reube Fulbe Development Rights Initiative, Hajiya Halima Yoman, ta jaddada muhimmancin haɗa Ƙungiyoyin Iyaye Mata da Kwamitocin Gudanarwar Makarantu domin kara yawan yaya mata a makarantu.

 

Ta ce hakan zai taimaka wajen shawo kan matsalar ƙarancin halartar ‘ya’ya mata a makarantun Fulani, tana mai cewa “Ilmantar da mace kamar ilmantar da gaba ɗaya al’umma ne.”

 

A nata jawabin, Wakiliyar Hukumar Ba da Ilimin Bai Ɗaya ta Jihar Kaduna (SUBEB), Hajiya Hauwa’u Muhammad, ta yi karin bayani game da aikin Kwamitin kula da makarantu kamar haka.

 

“Kwamitocin Gudanar da Makarantu suna zama hanyar sadarwa tsakanin makaranta da al’umma, inda suke ƙarfafa shiga tsakanin iyaye da shugabannin al’umma da ƙungiyoyi na cikin gida wajen gudanar da harkokin makaranta.”

 

“Suna kuma marawa baya shigar ‘ya’ya mata da sauran marasa galihu makaranta, ta hanyar warware matsalolin al’ada da na zamantakewa da ke hana su halarta.”

 

“Kwamitocin na taimakawa wajen sa ido kan ingancin koyarwa da karatun ɗalibai da malamai, domin tabbatar da gaskiya da inganci a harkar ilimi.”

 

Wasu daga cikin mahalarta taron da suka yi magana da Radio Nigeria Kaduna sun nuna farin cikinsu, inda suka bayyana taron a matsayin mai matuƙar amfani kuma daidai lokacin da ake bukata.

Sun kuma tabbatar wa CORET cewa za su yi amfani da ilimin da suka samu wajen inganta halartar makaranta da gudanar da ita a al’ummominsu.

 

Taron ya mayar da hankali ne kan manyan al’ummomin Fulani guda uku da ke Ladugga a Kachia: Wuro Nyako da Mbela Biradam da kuma Tiggirde.

 

COV: Adamu Yusuf

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: ECOWAS Makarantun Shirya Taro

এছাড়াও পড়ুন:

NECO Ta Saki Sakamakon Jarrabawar 2025

A cewarsa, ɗalibai 1,367,210 ne suka yi rajistar jarrabawar; maza 685,514 da mata 681,696.

Daga cikinsu, ɗalibai 1,358,339 ne suka rubuta jarrabawar, waɗanda suka haɗa da maza 680,292 da mata 678,047.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An tattauna yadda za a inganta walwalar malamai a Gombe
  • Gwamna Namadi Ya Taya Malaman Makarantu Da Suka Yi Fice A Jihar Murna
  • Gwamnatin Kano Ta Inganta Cibiyoyin Horas Da Sana’o’i Domin Dakile Aikata Laifuka Tsakanin Matasa
  • NECO Ta Saki Sakamakon Jarrabawar 2025
  • Babban Jirgin Ruwan Kasar Sin Ya Nufi Yankin Tekun Kudancin Kasar Domin Gwaji Da Samar Da Horo
  • Iran Ta Gabatar Da Sabbin Kayayyaki Guda 5 A Wajen Taron Kolin kere-kere .
  • Ɗan Majalisar Tarayya Ya Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-haren Ta’addanci A Sakkwato 
  • Fizishkiyan:  Wajibi Ne Musulmi Su Hada Kai Domin Dakatar Da Laifukan HKI
  • An kama tsohon minista kan zargin kisan kai domin tsafi a Nijar
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Gana Da Takwarorinsa Na Kasashen Qatar, Turkiyya, Pakistan Da Labanon A Doha