Nijar : Kasashen Faransa da Amurka ne ke kitsa mana hare-haren ta’addanci
Published: 1st, June 2025 GMT
Shugaban Nijar Janar Abdourahmane Tiani ya ce har yanzu ana wa kasarsa zagon kasa ta fuskar tsaro musamman daga kasashen yamma.
Janar Tiani ya ambato kasar Faransa da tsohuwar gwamnatin Amurka a matsayin wadanda ke da hannu a matsalolin tsaro da ake fama da su.
Ya bayyana hakan ne a wata hira ta musamman da gidan talabijin na kasar RTN da aka watsa a yammacin ranar Asabar.
Ya dai yi bayyani ne kan batutuwa daban daban ciki har da halin da kasar ke ciki.
Shugaban kasar ta Nijar, ya kuma jinjinawa sojojin kasar dake bakin daga domin tsare kasar dare da rana, ya kuma isar da ta’aziyya ga sojojin da suka rasa rayukansu a kokarin kare kasar daga sha’anin ta’addanci.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Da Amurka Suna Taimaka Wa Juna Da Samun Wadata Tare
A ranar 30 ga wata ne shugabannin kasashen Sin da Amurka suka gana da juna a birnin Busan na kasar Koriya ta Kudu, lamarin da ya jawo hankulan kasa da kasa, inda shugabannin 2 suka yi musayar ra’ayoyi dangane da huldar da ke tsakanin kasashen 2 da al’amuran da suka jawo hankulansu. Sun amince da inganta hadin gwiwar kasashen 2 a fannonin tattalin arziki da cinikayya da makamashi da kyautata mu’amalar al’adu.
A yayin ganawar, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya jaddada cewa, yana son hada kai da shugaba Donald Trump na Amurka wajen aza harsashi mai kyau na raya huldar da ke tsakanin kasashen 2, tare da samar wa juna kyakkyawan yanayin samun ci gaba. A nasa bangaren, shugaba Trump ya ce, kasar Sin, abokiyar Amurka ce mafi girma. Kasashen 2 za su hada kansu wajen samun nasarar gudanar da manyan ayyuka da dama a duniya. Nan gaba Amurka da Sin za su kara samun nasara a hadin gwiwarsu. Shugabannin 2 sun amince su rika yin mu’amala da juna. Shugaba Trump yana sa ran kai ziyara a kasar Sin a farkon shekara mai zuwa, ya kuma gayyaci shugaba Xi ya ziyarci Amurka.
Masharhanta sun yi nuni da cewa, ganawar shugabannin 2 ta sanya tagomashi kan kyautatuwar huldar da ke tsakanin Sin da Amurka, ta kuma tsara manufar raya huldar kasashen 2 a nan gaba, tare da kwantar da hankulan kasashen duniya.
Abubuwan tarihi da kuma hakikanin abubuwa sun nuna cewa, wajibi ne Sin da Amurka su zama abokan juna. A wannan muhimmin lokaci, ganawar da shugabannin kasashen 2 suka yi ta sake tsara manufar kyautata da raya huldar da ke tsakanin kasashen 2. Muddin kasashen 2 suka aiwatar da muhimman daidaito da shugabannin 2 suka cimma, da mutunta ruhin adalci, tare da martaba juna da samun moriyar juna, to, za a raya huldar da ke tsakanin kasashen 2 ba tare da wata matsala ba, da kuma kara samar da kwanciyar hankali da tabbaci a duniya. (Tasallah Yuan)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA