Kazem Sajjadpour Ya ce: Iraniyawa Suna Daukan Tarayyar Turai Ma Goyon Bayan Harin Zaluncin Isra’ila Kansu
Published: 9th, July 2025 GMT
Mai ba da shawara ga ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Tarayyar Turai ta zama abokiyar gudanar da ta’addancin ‘yan sahayoniyya kan kasar Iran
Kazem Sajjadpour, mai baiwa ministan harkokin wajen kasar Iran shawara ya bayyana dabi’ar Turai a lokacin da yahudawan sahayoniyya suke kai wa Iran hari a matsayin abin da ba za a amince da shi ba, saboda matakin da suka dauka na goyon bayan ‘yan sahayoniyya lamarin da mayar da ita mai hannu wajen kai hare-haren.
Sajjadpour ya ce: Turai ba ta da wani matsayi a manufofin ketare na Amurka kuma Donald Trump bai ma ambaci Turai ba a cikin wannan tsari.
A wani taron karawa juna sani na yanar gizo da aka gudanar a ranar talata mai taken “Hanyar Haramtacciyar kasar Isra’ila kan Iran: Abubuwan da za a samu a nan gaba,” Sajjadpour, yayin da yake magana kan halaye da matsayin Turai a yakin kwanaki 12 da yahudawan sahayoniyya da Amurka suka kaddamar kan Iran, ya ce: “Turai na goyon bayan gwqwamnatin haramtaciyar kasar Isra’ila a kodayaushe, kuma shiru ko goyon bayan da wasu kasashen Turai suka yi kan zaluncin Isra’ila za su kasance da sun mummunar tasiri a cikin zukatan Iraniyawa.”
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Kai Hare-Haren Wuce Gona Da Iri Kan Lardin Hodeidah Na Kasar Yemen
Sojojin gwamnatin yahudawan sahayoniyya sun kai hare-hare kan tashar jiragen ruwa na Hodeidah a kasar Yemen
Jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra’ila sun kai farmaki kan tashar ruwan Hodeidah da ke yammacin kasar Yemen, biyo bayan barazanar da sojojin kasar suka yi a yammacin jiya Lahadi.
Majiyar Yemen ta fada a yammacin jiya Lahadi cewa: An ji karar fashewar abubuwa masu yawa a tashar jiragen ruwa na Hodeida, sakamakon farmakin da jiragen saman yakin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai a yankin.
A cewar majiyoyin cikin gidan Yemen, sama da fashe fashe 20 ne aka samu a Hodeidah sakamakon hare-haren da jiragen saman yakin Isra’ila suka kai.