Aminiya:
2025-07-09@17:01:43 GMT

Yara miliyan 5.4 na fama da karancin abinci a jihohin arewa 9 – Red Cross

Published: 9th, July 2025 GMT

Kungiyar bayar da agaji ta kasa da kasa ta Red Cross ta ce akwai yara akalla miliyan biyar da dubu 400 da ke fama da matsalar karancin abinci a jihohi tara na arewacin Najeriya da ke fama da matsalar tsaro.

A cewar kungiyar, jihohin su ne‎ Borno, Adamawa, Yobe, Sokoto, Katsina, Zamfara, Neja, Binuwai da kuma Kano.

Mai rikon mukamin Darktan Lafiya da Kula na kungiyar Dr Aminu Abdullahi, shi ne ya bayyana hakan a yayin taron gangamin neman tallafi kan karancin abinci na kungiyar na shiyyar Arewa maso Yamma da ya gudanar a Kano ranar Talata.

Kwanan nan gwamnati za ta sake kara kudin lantarki a Najeriya – Minista Masu ƙwacen waya sun kashe ma’aikaciyar ofishin jakadancin Ghana a Abuja

‎Ya ce daga cikin adadin, akalla yara miliyan daya da dubu 900 ne kuma ke fama da matsanancin karancin abincin, yana mai bayanin cewa akwai alaka mai karfi tsakanin rashin tsaro da karancin abinci.

Dr Aminu ya ce, “‎Munahimci cewa yaduwar cutar yunwa da sauran cututtuka kamar su maleriya da amai da gudawa da kuma kalubalen tsaro a wasu sassa na Najeriya, ya zama wajibi a dauki matakan kariya da kuma wayar da kan jama’a ta hanyar hada kai da mutane domin lalubo bakinn zaren.

“Duk inda ake da matsalar tsaro, mutane kan kyale gonakinsu su bar yankunan. Sannan mutane da dama sun rabu da muhallansu sun koma ’yan gudun hijira a wasu wuraren. To duk lokacin da aka raba ka da hanyar samun abinci, akwai barazanar fuskantar matsalar yunwa.

“Sannan ba wai iya maganar abinci kawai ake ba, magana ce ta abinci main gina jiki da kuma ruwan sha mai tsafta,” in ji shi.

Shi ma shugaban kungiyar na Najeriya, Prince Oluyemisi Adetayo Adeaga, ya ce karancin abinci babbar cuta ce da ke bukatar agajin gaggawa saboda kada ta ta’azzara.

“Idan ka je asibitocin gwamnati da na masu zaman kansu, za ka ga yadda jama’a ke tururuwar zuwa saboda cututtukan da ke da alaka da yunwa. Hakan na da barazana ga dan Adam da ci gaban kasa,” in ji shugaban.

Shi ma shugaban kungiya a Kano, Barista Salisu Sallama, ya ce kodayake jihar ba ta da yawan masu fama da cutar idan aka kwatanta da takwarorinta, amma akwai barazana idan aka yi la’akari da halin da ake ciki da zai iya ta’azzara matsalar.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: karancin abinci yunwa karancin abinci

এছাড়াও পড়ুন:

Kano ta sami rahoton cin zarafin yara 351 – NHRC

Hukumar kare hakkin bil’adama ta kasa (NHRC) a jihar Kano ta ce ta samu rahoton laifuka 351 na take hakkin yara daga cikin jimillar kararraki 446 da ta samu daga watan Afrilu zuwa Yuni 2025.

 

Kodinetan NHRC na jihar Kano Alhaji Shehu Abdullahi ne ya bayyana haka a Kano.

 

Ya bayyana cewa daga cikin jimillar korafe-korafe 446 da aka samu a cikin watanni uku 351 na da alaka da take hakkin yara.

 

Ko’odinetan jihar ya yi nuni da cewa, sauran shari’o’in sun hada da tashin hankalin gida 19, 18 da suka shafi ‘yancin tattalin arziki da zamantakewa, da kuma biyar da suka shafi ‘yancin rayuwa.

 

 

“cikin zarge zargen har na Maita da sauran shari’o’in da suka shafi take hakkin dan adam”

 

 

A cewar Alhaji Shehu, yanayin zamantakewar al’umma a halin yanzu yana nuni da yadda ake tauye hakkin yara, wanda hakan ya nuna yadda ake kara yawaitar yaran da ke yin bara a tituna da kuma rayuwa cikin mawuyacin hali.

 

“Sakaci na iyali da al’umma shi ne babban abin da ke haifar da cin zarafin yara da kuma karuwar ayyukan aikata laifuka a tsakanin matasa.”

 

Ko’odinetan hukumar ta NHRC ya jaddada cewa, yayin da bakwai kawai daga cikin wadanda aka bayar da rahoton an aikata su ne ta hannun masu  fada aji kuma yana farywa a cikin gidajen aure.

 

“Iyali su ne tushen al’umma, al’umma kuma ita ce al’umma, saboda haka, duk wani cin zarafi a cikin iyali zai yi naso a kan al’umma baki daya.”

 

Ya kara da cewa “Lokacin da aka samu babban cin zarafi a cikin iyali, ba za a iya samun ci gaba mai ma’ana a cikin al’umma mafi girma ba.”

 

Alhaji Shehu ya ci gaba da cewa, daga cikin korafe-korafen da aka samu, an gudanar da cikakken bincike da kuma kammala shari’o’i 341, yayin da 105 ke ci gaba da sauraron karar.

 

Ya yi kira ga jama’a da su samar da zaman lafiya da juna tare da kai rahoton duk wani da ake zargi da take hakkin dan Adam ga hukumomin da abin ya shafa.

 

Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, NHRC tana aiki ne a matsayin wata hanya mai zaman kanta don tabbatar da mutuntawa, kariya, da kuma inganta hakin bil’adama a Najeriya.

 

Khadija Aliyu

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Rawar Ganin Da BRICS Ke Takawa Wajen Samar Wa Kasashe Masu Tasowa ‘Yanci A Tsarin Gudanar Da Harkokin Kasa Da Kasa
  • Hukumar Kiyaye Hadura Ta Kasa Za Ta Aiki Da ‘Yan Jarida A Kano
  • Za A Horas Da Jami’an Tsaron Sakkwato, Kaduna Da Benue Sabbin Dabarun Aiki
  • Hukumar Abinci Ta Duniya ( WFP) Ta Jefa Wa Mutanane Kudancin Sudan Abinci Ta Sama
  • NAJERIYA A YAU: Sarkakiyar Dake Gaban Hadakar ADC — Atiku Ko Peter Obi
  • Sin Ta Kafa Kungiyar Masana Masu Binciken Sararin Samaniya Mai Zurfi Ta Farko
  • Kano ta sami rahoton cin zarafin yara 351 – NHRC
  • Gwamnatin Kasar Iran Ta Yaba Da Kungiyar BRICS Saboda Yin Tir Da HKI A Yakin Kwanaki 12
  • NAJERIYA A YAU: Mene ne tasirin naɗin Mataimaka na Musamman a rayuwar jama’a?