Tsohon Ɗan Takarar Gwamna A CPC, Haruna Sa’eed Kajuru, Ya Bukaci Gwamnatin Tarayya Ta Binciki Kisan ‘Yan Zariya A Filato
Published: 9th, July 2025 GMT
Tsohon ɗan takarar gwamna ƙarƙashin jam’iyyar CPC ta shuɗe a Jihar Kaduna, Alhaji Haruna Sa’eid Kajuru, ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta gudanar da cikakken bincike kan kisan da aka yi wa wasu mazauna Zariya da suka je dauren aure a Jihar Filato kwanan nan.
Alhaji Kajuru ya yi wannan kira ne a lokacin da ya kai ziyara ta jaje ga iyalan waɗanda suka rasa ‘yan uwansu a Zaria, inda ya nuna alhini da ta’aziyya ga dangin waɗanda wannan al’amari ya shafa.
Tsohon Akanta Janar na Jihar Kaduna, Alhaji Haruna Kajuru, ya yi Allah-wadai da kisan, yana mai jaddada cewa babu wani mutum ko ƙungiya da ke da ikon da kundin tsarin mulki ya ba shi na kashe wani ɗan ƙasa.
Ya ce dole ne a kama masu hannu a kisan kuma a gurfanar da su a gaban shari’a domin hakan ya zama izina ga sauran mutane.
“Kundin tsarin mulki bai amince da kisan wani ɗan ƙasa ba. Dole ne mu tsaya tsayin daka wajen ganin an tabbatar da doka da oda a kasa,” in ji shi.
Alhaji Haruna Sa’eid Kajuru, wanda shi ne tsohon ɗan takarar gwamna na CPC a Jihar Kaduna, ya kuma yi kira ga gwamnatocin tarayya da na Jihar Kaduna su tallafa wa iyalan da abin ya shafa, domin rage musu raɗaɗin rashin ‘yan uwa da masu ciyar da su.
Kazalika, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su ci gaba da zauna lafiya da juna, yana mai cewa zaman lafiya da haɗin kai su ne ginshiƙan ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’umma.
Kisan da aka yi a Jihar Filato ya janyo tashin hankali da kiraye-kiraye daga sassa daban-daban na ƙasa kan buƙatar ƙara tsaro da tabbatar da adalci a cikin al’ummomin da abin ya shafa.
Rel: Adamu Yusuf
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Yan Zariya Ɗan Takarar Gwamna Gwamnatin Haruna Tarayya
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Yusuf Ya Kaddamar Rabon Na’urorin Rarraba Lantarki 500
A wani yunkuri na bunkasa samar da wutar lantarki da kuma bunkasar tattalin arziki, gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da rabon kashi na farko na taransfoma 500 ga al’ummomin karkara a fadin kananan hukumomin jihar 44.
Gwamna Abba Yusuf ne ya kaddamar da shi a hukumance a Kano a wani shirin da nufin magance kalubalen rashin samar da wutar lantarki.
Gwamna Yusuf ya ce samar da taransfoma wani shiri ne na bunkasa masana’antu da zaburar da harkokin kasuwanci musamman a yankunan karkara.
“Wannan rabon shi ne kashi na farko na aikin samar da wutar lantarki a yankunan karkara, ba wai kawai wani aikin samar da wutar lantarki ba ne, wani muhimmin mataki ne na inganta samar da wutar lantarki ga jama’armu. Samar da wutar lantarki mai inganci na da matukar muhimmanci ga ci gaban masana’antu da bunkasar tattalin arziki.”
Gwamnan ya bukaci masu ruwa da tsakin al’umma da su mallaki na’urar taransifoma gaba daya, sannan ya umurci shugabannin kananan hukumomin da su kafa kwamitoci don kula da ayyukan da kuma tabbatar da tsaro.
Kwamishinan Ma’aikatar Raya Karkara da Cigaban Al’umma Abdulkadir Abdulsalam ya yabawa kokarin Gwamnan na inganta rayuwar al’umma da bunkasa tattalin arzikin karkara.
“Wannan rabon na nuna alamar ci gaba da yunƙurin da Gwamna ya yi na tunkarar ƙalubalen da al’ummomin karkara ke fuskanta. Na’urar taransifoma za ta inganta rayuwar jama’a sosai, da inganta tattalin arziƙi, da kuma jawo hankalin masu zuba jari.”
Bikin ya samu halartar mataimakin gwamnan jihar Kano, kakakin majalisar dokokin jihar Kano, mai martaba Sarkin Karaye, da manyan jami’an gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki.
ABDULLAHI JALALUDDEEN KANO.